Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bataiba ta zare rigar baccinta ta Sama ta Bari a gurin tareda shigewa toilet din daya gama tsaruwa, Sunkuyawa qasa Ayanaah tayi a natse ta dauke rigar data zare din tana barin gurin ta kai rigar inda Kayan wanki suke ta dawo ta isa inda towels suke sama da guda ashirin ta dauko guda uku harda na goge kai suna wani qamshi me sanyi ta dawo bakin kofar ta tsaya da towels din. Tsayi me tsanani tayi a gurin batareda ta motsa ba duk kuwa azabar datake ji ta tsayin hakan take a tsaye kanta a qasa har tsawon lokacin da batasan Yaushe ne ba tukuna ime din ta bude kofar toilet din Wanda Ayanaah tayi saurin miqa mata towel din farko ta amsa ta daura a jikinta kafin ta sake bata wani t rufo jikinta kafin na ukun ta Dora akai dan goge kanta. Tana wucewa gaban mirror Ayanah ta fada toilet din ta sake gyaresa tsaf ta qamar da ruwan toilet din tsaf duk kaman ba yanzu aka fito wanka cikinsa ba. Tana gamawa ta fito tana gyara dakin da gadon dakin sakina da wata baiwar daya suka shigo suna busar mata da gashinta tareda gyarasa tana zaune tana kallan kanta a madubi. Tsawon lokaci suka dauka suna hidimarta kafin suk kammala ta fito cin abincin da Sauran su suka dafa mata sama da Kala daya ta zauna suka zagayeta kowannesu da abinda yake mata. Har dare suna tsaye kan kafafunsu basu zauna ba Bayan sallah babu abinda sukeyi sai hidimarta wadda bata qarewa. Sai tsakar dare sosai suka koma daki Bayan tayi bacci, A tsananin gajiye suke dan haka komai babu Wanda suka iya yi bacci suka buge dashi mai karfin gaske, Asubar fari aka buga qararrawa tashi yake suka fito sukai ayyukan bangarensu na bayi har lokacin sallahn asuba yayi sukai sallah sukai wanka tareda shirya wa suka fice ayyukansu na iyayen gidansu. Kaman yanda sukai jiya yauma haka suka wuni suna aikin wahala da bauta babu sukuni abincin da sukeci ma a tsaye suke cinsa ba yancin zama. ****farkon wannan wahalar da suka samu kansu a cikinta na bautar da babu Hutu ko kadan dan Baka isa kayi bacci ba sai Wanda kake bauta wa yayi nisa sosai a nasa baccin, Farko farko kafin su Saba sosai suke jin jiki amma ahankali ahankali suka saba da wahalar wadda ta zama jiki har basa jin komai, Kaman computers haka suke da aiki ba mantawa ba kuskure a natse, Watanni hudu kenan yanzu a zamansu cikakkun bayin boyem da suka Riga suka saba da tsantsan na masarautar da dokokinta ba kuskure ko daya, Idan aka hada da watannin da sukai a daular bayi kusan wata bakwai kenan a BOYEM Wanda yayi daidai da shekara guda harda wata daya rabon su iyayensu, Tsawon watannin nan babu ranar da Ayanaah bata baqin ciki da quncin rashin Zuhrah, A kowane motsi da numfashinta babu abinda ya rage na rayuwar baqin ciki da quncin datai tareda rashin yan uwanta a tareda da ita, Sakinah ce kadai zata iya shedar da qunci ne zallansa a daddabe da zuciyar Ayanah amma a bayyane ta rungumi kaddarar datake cikinta. Ime dinsu da suke bautawa kwatsam Allah ya azurtata da samun cikin daya saka aka yayeta daga zuwa shimfidar sarki sai kuma idan ta haihu idan tanada rabon ya sake kwanciya da ita kenan. Yayeta da akai ya saka dukkanin bayi shiga fargaba da tsoron sabbin imebētin da zaa zabar wa sarki Wanda a yanzu baya qasar kafin dawowansa zaa kuma zabar sabbin imebētin da zai huta dasu dakyau idan ya dawo. #MAMUH #ROYALTY #AYANAH GHAZ #NUAB BOYEM HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: _*HAYATEEM*_ Mamuhgee 24 Duk damuwa da fargaba da duka kyawawan bayin dake BOYEM ke dan shiga da tsoron sabbin imebētin da zaa zaba Ayanah bata taba ma San da hakan ba sbd bama huriminsu ne na shiga ba dan kuwa tasan a cikin sama da mata bayi sama da dubu dake bauta a masarautar bama sa cikin wainda zaa iya gani bare sani tinda suna bangaren imebētis din sarki suna bauta basa can bangaren matansa biyu da bayansu bai taba qarawa ba. Dan haka bautarta kawai takeyi babu tinani kowane iri a zuciya da rayuwarta Bayan na ‘yar uwarta datake azabtuwa da rashinta a kowane daqiqa, Tinda ta rabu da Zuhrah bata taba jin sassauci na rashinta ba ko kadan a zuciyarta Wanda bama ita kadaiba kowace daqiqa tana wuce mata ne da tsananin ciwo da quncin rashin Nurat da Abaas da Zuhrah din, Suna tsananin so da kaunar iyayensu amma yanda suke tsananin son junansu da irin gwagwarmayan da suka shiga ya saka suke jin mummunan ciwon rashin junansu fiyeda Zafin rashin iyayensu, A nata zuciyarma gabaki dayansu a cikin jininta yake jinsu tamkar itace ta haifesu din da gaske sbd uwar data zama garesu musamman Nurat datake ambatarta da AMMAH kafin rasuwarta, Ciwon rashin ‘yan uwanta da sune rayuwanta bazai taba barin zuciya da ruhinta ba har abada,da wannan ciwon zata mutu idan ma ba ciwon rashinsu bane zai zama ajalinta sbd a yanda takeji babu wahala ko azabar da bazata iya dauka ba amma ciwon rashinsu abu ne da zuciya da gangar jikinta bazai taba dauka ba musamman irin rasuwar da Nurat tayi. Rayuwanta a Masarautar BOYEM bata taba sakewa ko sabawa da kowa ba Bayan sakinah wadda take tsananin kulawa da ita idan suna daki sbd tsoron bugawan zuciyarta datake riqe da abubuwa da dama ta kasa saki ta kuma kasa fada Bare nunawa, Cin zuciyarta damuwa da quncin sukeyi Wanda suke bawa zuciyarta illa ahankali batareda saninta ba dan haka sakinah batada damuwa itama a nata rayuwar yanzu Bayan ta Ayanah din, Itama sakinah ko a mafarki ma bata taba saka kanta a lissafin da wasu bayin keyi na shakka ko tsoro sbd ko zasuyi shekaru dari a BOYEM babu ranar ma da ko bawa irin su zai iya cewa yana shaawansu bare me qasar da kansa duk da bai taba zaben macen dazai kwanta da ita ba da kansa duka wannan aikin shugabar jakadan qasar BOYEM ce gabaki dayanta wadda take Zaune cikin masarautar itama da nata bayin sbd babu me matsayi dake Masarautar BOYEM fa baya cikin nasa jin dadin da daula me girma tareda tarin dukiya. Meleketen’ya wadda ake kira da Ten’ya wato jakadiya da yarensu itama matsayi ne da ake gadonsa sbd tin kakanni da shekarun da suka gabata jini daya ne suma suke riqe wannan matsayin dan haka shima matsayi ne me girma da iko dan kuwa duka bayin dake cikin asalin masarautar BOYEM a karkashin iko da umarninta suke yawo da aiki, Hakama tenya din itace me kulawa da dukkanin abinda ya shafi sirri da babbar buqatun matan sultan da ‘yayansa wainda suke jininsa, SULTAN YASAR ALMAZ BOYEM shine Sarkin Boyem da ikonsa yake zagaye da kusan fiyeda Rabin daulolin dake duniyarsu, SULTAN YASAR sarki ne da mulkinsa yakeda tsananin zafi da karfi tareda tsananin doka da ikon daya saka ko dabbar masarautar shakkar laifi takeyi sbd hukuncin dayane fa Mutum ga dabba wato cire kai kawai dan haka a cikin tarihi

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});