Chapter 6
Chapter 6
ba zata zauna a karkashinsa koda ba aure zai killaceta ya Hana kowa koda ganinta sbd kada kowane ido yayi mata illa, Duk da ba aure tsakaninsu yanada Alkawari da fatar duka yayan dazai haifa a rayuwarsa su hada jini Ayanarsa, idan kuma mace Allah zai basa to adduarsa koyaushe a cikin ibadarsa shine ta kasance tamkar Ayanarsa koda hakan shine burinsa na karshe yana fatar Allah ya cika masa shi koda a ranar mutuwarsa ce. Asamah da dukkanin jikinta yayi tsananin sanyi da kaunar ahalin GHAZ din da baka gane wane yafi wani kaunar dan uwansa Jin takeyi Inama nata ahalin sunanan da yayanta zasu yi girman su zuhrah da Abaas sbd itama ‘yaya mata biyu ne da ita sai namiji daya kaman Abaas, Hawayene masu tsananin zafi da radadi suka ciko idanuwanta ‘dacin rashinsu na taso mata Wanda daman a tsawon shekarun nan bata taba manta radadin ba koda na qanqanin lokaci ba, Hadiye hawayenta tayi sbd kada su bayyana a gabansu. Juya wa tayi Bayan ta gama jere komai ta kalli kakkaifar qaramar wuqar dake kan Kayan da zata bar gurin dasu ta yanka Kayan marmarin taga yanda take daukan ido, Zuciyarta ce tahau Kai kawo cikin tsananin qunci da baqin cikin daya taso mata na rashin yayanta da tsananin buqatar son dawowan mijinta gareta Wanda zuwa yanzu tasan azaba ta dade da sauyasa zuwa wata mummunan halittar amma tanason abinda a hakan. Shedan da zuciyarta dake rufewa idan abin ya taso mata Wanda yake tamkar tabin kwakwalwa batareda sanin kowaba suka saka zuciyarta rufewa tafara taku daya na biyun ta saki gabaki daya Kayan hannunta a jikin Abaas Wanda wuqar ta yanki gefen qafarsa take jini ya fara fito wa Wanda ya saka dukkaninsu miqewa cikin tsananin tashin hankali da damuwa Asamah ma cikin tashin hankalin da tsoro me tsanani ta zube gabansa tareda rigan kowa saka hannunta a kafarsa tana wani irin rawar jiki da kukan dayake fito wa daga qasan ranta tana basa hakuri cikin kulawa sbd a qasan ranta tasan kofar wata rayuwar ce zata bude wa duk Wanda yake garin ANJOM wadda bata San wace iri bace dan kuwa a gefen rigar jikinta ta goga jinin me yawa daga qafar Abaas batareda lurar kowa ba. Cikin sauri sakon fitar jini a jikin GHAZ Abaas ya isarwa Abaa dinsu wanda ba bata lokaci ya iso gurin Wanda ya saka duk Sauran bayin dake zagaye da gurin na kowannensu dake rumfar ja baya sosai cikin girmamawa. Wuqar da jininsa ya taba ya fara bada umarnin a karba hakama take aka kawo ruwa masu yawa a babbar tasa me kyau aka saka Asamah wanke duka hannuwanta da jinin Abaas ya taba kafin take GHAZ Ali din da Kansa yasa aka kawo magani ya karba yana kallan Abaas din Wanda hankalinsa yake son tashi sbd fitar jininsu tamkar hadari ne ga dukkanin ANJOM gabaki daya sbd da jininsu ne kadai ake iya karya komai dake ANJOM dan haka Sam baa taba yadda da kowa ba game da duk wani digon jinin GHAZ. Amma ganin Asamah ce ta raunanasa bada ganganba kuma tamkar ahali take sai hakan na hana zuciyarsa shiga tashin hankali da tsoro sosai. Kukan da Asamah ke yi ya saka Ayanah rarrashinta tareda Zuhrah Nurat da Amma kuwa suna jikin Abaas din cikeda damuwa suna kallan yanda GHAZ ya saka masa garin maganin da take jininsa ya tsaya ya Dena zuba. Ajiyan zuciya GHAZ ya sauke yana dagowa ya kalli Abaas din cikeda kulawa da qara tabbatar masa da tsananin mahimmancin jinin dayake yawo a jikinsu. Cikin nutsuwar mulkin dayake yawo jikinsa da kulawa tareda tabbatarda kiyayewa GHAZ ya bude baki yace ‘GHAZ Abaas ya koma dakinsa a tabbatarda an kiyaye danyen yankan kafarsa ta warke da kyau batareda ya sake fitowa ba’ Gyada Kai kowa yayi suna amsa wa da cewa ‘Angama’ Juya wa yayi ya bar gurin kowa yayi tsit cikeda damuwa da alhini har saida ya fice kwata kwata kafin Abaas din ya dago ya kalli Asamah kaman zai yi magana sai bai ce komaiba ya maida idanuwansa Akan Ammansa dake miqewa tabar gurin tana bin Bayan GHAZ Ayanah kuma hannu ta miqa masa ya Kama ya miqe suka nufi hanyar dakinsa tana cewa ‘Yankan qaramar wuqar cin tufa bazata girgiza jarumin anjom ba GHAZ din anjom me zuwa’ Yar dariya yayi yana kallan kafar tasa tareda cewa ‘Shekarun nawa basu Kai ba ai tukuna amma insha Allah idan nakai shekaru ashirin a duniya zan fara fita a matsayin jarumin na anjom wata ran harma na zama Garkuwa ga dukkaninku’ Har cikin ranta taji dadin abinda ya fada tana fatan hakan koda kuwa a mafarki ne. Rakasa tayi dakinsa Wanda acan suka zauna ta tayasa fira sai ga su Zuhrah da Nurat sun taho suma sbd sunsan saiya kwana biyu kafin ya fito koina sbd tsaro da dokar GHAZ din tin asali duk Wanda yake jinin GHAZ yaji rauni har jininsa ya fita to saiya kwana biyu a killace batareda fito wa koina ba sai Raunin ya qame, Hakan ne ya saka yan uwansa zuwa dan tayasa fira da debe kewa, Kayan ciye ciye da dafaffiyar madarar raqumi me dumi aka kawo aka ajiya musu sunata firarsu da hutawarsu cikin kwanciyan hankali da nishadin farin cikin kansacewa da juna, Anan suka wuni dan hatta ibadarsu anan sukayita, Da yamma ma mahaifinsu shigowa yayi cikinsu cikeda Shakuwa da kaunar juna suka cigaba da farin cikinsu anan cikinsu yayi sallah tareda iyalansa har cikin dare tukuna dukkaninsu suka watse kowa ya nufi makwancinsa. Ayanah na isa dakinta zare Kayan jikinta tayi ahankali tana rufe jikinta duka ruf da wata kakkaurar doguwar rigar wanka me Kama da alkyabba amma ita ta yadin saka me kyau. Baiwarta Sakina ce take biye da ita dauke da wutar haskawa. Gurin wankansu ta Nufa Wanda yake cike da ruwa masu tsafta da kullum ake sauyawa ta zare rigar tana zaunawa gaban ruwan tafara wanka a natse. Sakina ajiye mata hasken tayi ta koma kofa ta tsaya daga waje tana jiran fitowarta. Gama wankan tayi ta fito tana qamshin madarar flower me dadi. Dakinta ta shiga ta zauna Sakina tana tayata goge jikknta harta gama ta shirya ta nufi lafiyayyan gadonta na sarauta ta haye. Washe gari ma haka suka wuni gurin Abaas tareda iyayensu Wanda kwata kwata GHAZ ayau din bai fita koina ba yana cikin yayansa tausayin Abaas haka kawai yake shige masa zuciya sbd ganin kaman zuciyarsa tayi sanyin da bazai iya mulki ba idan ma yayi wahala zaisha sosai, Akan ‘yayansa mata ya maida idanuwansa yana kallan yanda suke dariya suna Wasagu da juna sautin dariyarsu na shiga kunnuwansa zuciyarsa na na cikewa da tsananin kaunarsu yanajin kaman ya maidasu cikin Mahaifiyarsu sbd basu tsaro da kariya daga dukkanin wata cutar duniya da wahala. Akan Ayanah ya tsayar da idanuwansa dariyarta na a bayyanarda asalin zallan Kyan da Allah yayi mata Wanda yasa Sam baa barinta fita daga GHAZ din itama, Ayanah nada zuciya me sanyi da hakuri tareda juriya tareda jajircewa Akan ‘yan uwanta Wanda yasa yakejin kannenta sun dace dan kuwa tamkar uwarsu haka take kulawa dasu, Akan Zuhrah ya maida idanuwansa yana kallan gashinta dayake sake zube a bayanta Wanda babu namijin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106