Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 34

Chapter 34

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da gasken gaske duniyar take son Allah ya dauketa daga cikinta ta tafi ta huta amma kuma idan babu ta Ayanah zata zama mara amfani a duniya sbd bazata taba moruwa ba. Koda asuba tayi suna tsaye sbd tin kafin asuba aka tadasu aka tarasu a babban guri, Anan aka sake rarraba musu uniform da abubuwan amfani a jaka aka bawa kowa nasa, Sallar asuba kawai suka koma daki sukai aka sake buga qararrawa kira suka ringa fitowa kowa dauke da jakarsa fes dasu, Jikin Ayanah dana Zuhrah a sanyaye sbd Sai yanzu ne Ayanah take sake fahimtar tsoron Zuhrah na zaa iya rabasu a gurin aiki ko gurin kwana dan haka itama jikinta ya tsananta sanyi. Motoci ne masu tsayi bus bus aka zuba su a ciki aka fice dasu zuwa cikin palace din. A mota ma hannuwansu na riqe dana juna qamqam sakina na gefensu, Ficewa akai dasu daga babbar gate din daular bayi aka miqa zuwa mahaukacin gate din shiga BOYEM palace wadda securities dinta suka mugun baci sbd tsananin tsaro, Shi Karan Kansa gate din shiga Masarauta kashe idanuwansu sukaga kaman yana yi sbd kyansa dayake tamkar na zinari, Scannin komai nasu dasu kansu akai daya bayan wuni guda Ana abu daya kafin Ana gap da kammala wa aka zo kan wasu su biyu wainda sunan mahaifinsu Yazo irin daya komai da komai. Dakatar dasu akai tareda zagaye su da wasu irin securities da suka sakasu saurin durqusawa kasa kansu a qasa jikinsu na wata irin rawa cikeda tsoron dake Neman rabasu da bugawan zuciyarsu. Chief security ne Yazo gurin da Kansa ya kallesu dakyau kafin ya kalli sunayen nasu Akan wadda tafi girma ya tsaida idanuwansa ya bude baki yace ‘Meye alaqarku da sunanku Yazo daya?? Wani yawu babbar ta Hadiye kafin cikin sanyi kanta na qasa tace ‘Alaqar jini ce…… Ko rufe baki bata gama yi ba akai sama da ita tamkar ba Mutum ba aka jefa cikin wata motar da batai Kama da mota ba sbd tsarinta dayafi Kama da motar yaqi. Wani ihu taje yi tana kokarin riqo qanwarta a lokacinda ake janta tana jin kaman ranta zai fita amma ko imanin kallanta babu take aka buga kanta da karfen motar ta zube a cikin motar jini na fitowa gefen fuskanta kadan. Qanwar tata ma Wani irin kuka me karfin gaske takeyi tana ambatar sunan yar uwarta kaman ranta zai bar jikinta take aka sumar da ita da wata shocker a gurin akace a dauketa a maidata daular bayi. Ganin hakan ya saka wainda ke bayinsu suma su uku fara rawar jiki sbd suma yan uwane uwa daya uba daya. Suma Ana duba sunayen su take aka rarrabu su ukun aka soke lasisin biyu aka bar daya Sauran zaa rabasu zuwa dauloli daban daban ga Wanda yayi rashin saa kuma ciyar da dabbobi namansu kawai akeyi sbd tin farkon shigowa qasar baa karban bayin da suke da alaqa da juna, Doka ce da kaida me tsananin karfin gaske baa barin masu alaqa a masarautar matsayin bayi duk lokacinda aka Kama masu alaqa kai tsaye hukuncinsu a kashe daya abar daya tin asalin asali wannan dollar take sbd a shekarun baya sosai da suka gabata akwai bayi uku da suke uwa daya uba daya da suka kulla shirin guduwan juyin mulkin daya haddasa fitina mai tsananin gaske a masarautar boyem wadda baa taba maimaita irinta ba dan haka tin kakannin kamanninsu aka tsauranta dokar tareda kafata mai karfin gaske kai tsaye duk bawan daya kasance yanada ahali to kai tsaye hukuncin Kisa ne ga ahalin gabaki dayansu sbd kawar da kowace irin barna, Bayi da yawa tin shekarun da suka gabata sun rasa ahalinsu akan hakan, Duk bawan dayake boyem Sai an tabbatarda baida kowa a duniya Bayan Kansa sbd Kaucewa fitar sirrin masarautar Shiyasa ko Ka samu yancin Ka baka taba barin qasar boyem sbd bakada kowa a duniyar sedai Ka Gina sabuwar rayuwa. Dan hakanne yasa duk wainda suke kawo bayi qasar sai sun tabbatarda bayinsu basuda kowa a duniya ko sunada Sai a tabbatarda basa duniya an kawar dasu sbd Ka zama na masarautar ita daya, Kusrawa tin a farkon shigowa qasar sun tabbatarda bayinsu basuda kowa a duniya dan hakanne kai tsaye a yanzu duk Wanda aka samu yana tareda wani nasa zaa kawar da daya a bar daya. Doka ce da tsananin karfinta babu Wanda zai taba wucewa kai tsaye ba tsayawa tinanin komai ake kawai da daya dan haka yanzu dinma hakanne zai faru akan wainnan sabbin bayin. Cikin masifaffiyar azaba suna tsananin fita hayyaci suke kasa rabuwa da juna inda daga karshe suka zabi a dauki ransu su duka ukun wainda suke Bayan na farkon dan hakan babu bata lokaci take aka jasu su ukun kai tsaye akai baya dasu sedai kawai yaji qarar bindigar cika musu burin abinda suka zaba amma babu Wanda yaga inda aka fito ko yi da gawarsu. Zuhrah da Ayanah dake kusan qarshe dagowa sukai a Wani irin slow suka kalli juna dukkaninsu jikinsu na qarasa sakewa gabaki daya da sabuwar mummunan kaddarar dake gabansu wadda basuda ma tinanin yi akanta. Jajir idanuwan Ayanah sukai Zuhrah kuwa gangarowa nata hawayen suka fara da idanuwanta da suka kasa daukewa daga kan Ayanah tanajin tin yanzu tamkar ruhinta na barin jikinta sbd rabuwa da Ayanah na nufin mutuwarta, Ita zata zabi a kasheta abar Ayanah sedai kuma basuda masaniyar waye zaa Bari a cikinsu kuma waye zaa bari, Ita tanason Ayanah ta rayu sbd tanada dauriya da tawakkali hakama zata rayu a cikin aminci anan din amma kuma tasan Ayanaah zata zabi a kashesu gabaki dayansu kaman yanda na gabansu suka zaba sbd bazata iya barin a rabasu ba. Wasu hawayen ne masu zafi suka gangaro mata tana sake kallan Ayanah tanason rungumarta taji dumin jikinta na bankwana amma daman hakan ta gama qare musu har abada dan haka zata zabi su rayu sbd Ayanaah kawai koda hakan na nufin raba jininsu har abada indai tana ganinta hakan ma ya isheta. Sakinah dake gabansu dan juyowa tayi ahankali ta shiga tsakiyar su itama idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin tausayinsu musamman Ayanah dake girgiza kai ahankali idanuwanta na tsananta ja hannuwanta na fara rawa ahankali ta bude baki tana kallan Zuhrah dake kallanta tana hawaye masu tsananin rauni da ciwo tace ‘Zuhrah bazan iya rayuwa babu ke ba, Zuhrah na zabi barin duniya tareda dake mu tafi mu huta….. Girgiza kai Zuhrah tayi hawayenta na tsananta jikinta a sanyaye tace ‘Abaas fa?’ ‘Allah zai zama gatansa amma a yanzu da kike tare dani bazan iya rayuwar da babu ke ba Zuhrah’ Kuka Mara sauti Zuhrah ta sake tana kokarin zare hannunta daga na Ayanaah din tace ‘Sbd ki rayu tare dani din zan zabi hakan, Inason ki rayu Ayanah ki samu rayuwan da zai baki nutsuwa dan hakanne dole zamu zabi raba jini, Kina raye Ina raye muna Masarauta daya muna shakar Numfashi guri daya insha Allah zamu samu yancinmu wata rana mu tafi tare’ Girgiza kai Ayanah tayi da karfi tana sake riqe hannun Zuhrah tace ‘Zuhrah idan muka zabi hakan mun rabu kenan har abada,muna guri daya amma bazamu taba nuna mun san juna ba bare Hadin jini, Bazamu taba sake

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});