Chapter 11
Chapter 11
Asamah a cikin mummunan yanayi take samun tabbacin mutuwan mijinta tin shekarun baya hakama a Daren itama daqyar Tasha sbd umarnin a kasheta da shugaban kusra ya bayar. Fitowa sukai daga ramin babu me gani sosai sbd kumburin ido. Sakina ce ta Kama hannuwansu daya bayan daya suka gama fitowa suna kallan filin dajin da hayaqi yake tashi sbd wutar garin da har lokacin ci takeyi sosai hakama koina yayi tsit ko kukan dabbobi babu. Hanya suka jijjuyawa suna Neman gurin bi sbd sun riga sun sauka daga kan hanyar da Abaa ya dorasu da zata kaisu inda yace kuma bazasu maida kansu hanyar komawaba bare su sake hawa hanyar daga can. Hawaye ne masu tsananin zafi suka gangaro daga idanuwan Ayanah ta sake riqe hannun Abaas dake cikin nata gefe daya kuma Nurat na riqe da ita Zuhrah na riqe da Asamah suka Kama hanya ba tareda sunsan inda zasu ba suka cigaba da nutsuwa cikin dajin. Tafiya sukeyi bame cewa komai ba kuma me kuzari dan haka har rana ta fara ketowa zafi na ratsa su ga babu me takarma a kafa dan haka wahala ta faro sako kai amma duk da hakan babu Wanda yace komai har lokacin. Wuni guda sukai suna tafiya sai gab da magrib suka fara hango ruwa daga nesa dan haka suka dan sauke ajiyan zuciya kadan Sai a lokacin Ayanah ta kalli kafafun yan uwanta taga kowa kafarsa ya fashe sosai jini sukeyi dan haka tace su zauna su huta. Guri suka nema suka zauna babu me kuzari a jiki, Nurat da Zuhrah ne suka kwantar da kansu a kafadunta suna rufe idanuwansu hawaye masu dumi suna gangarowa daga ciki, Abaas kuwa gefe ya zauna tareda sunkuyar da Kansa yana kafawa qasa jajayen idanuwansa da sukai nauyi da kumburi. Har duhun dare yayi suna Zaune gurin salla ma a haka sukai da taimama ba ruwa, Nurat ce me tsoron cikinsu dan haka duhu na qarawa hankalinsa yana sake tashi dan haka dole suka miqe a hakan suka sake bin hanya cikin hudun dare babu motsin komai koda kuwa na dabba ne daman hakan dajin yake shiru babu motsin komai gwanin tsoro da firgita. Tafiya sosai sukai har dare ya sake tsalawa sosai karfinsu gabaki daya ya qare ga yunwa da azaba Zuhrah Amanta uku a hanya. Duk wannan tafiyar da sukeyi suna maqale da juna sun kasa sake juna, Fitsari Nurat tace zatai dan haka suka tsaya ta dan matsa gefe kadan ta durqusa tayi ta gama kenan tana miqewa taji Mutum ya cafkota gabaki dayanta batasan lokacinda ta fasa wani irin mummunan ihu me karfin gaske ba daya saka Sauran kusrawan dake gurin tahowa gurin da sauri suna ihun daya saka fitsari kufcewa Sakina. Cikin mummunan tashin hankali da tsananin tsoro Su Ayanah sukayo gurin sedai Asamah da sakinah riqe su sukai da karfi suna hanasu tafiya sbd kada Ayi biyu, Sama kusrawan su shida sukai da Nurat suna dariyar farin ciki suna tsalle tana ihu da wani irin kukan mafi tashin hankalin rayuwanta. Kwacewa Ayanah ta fara yi tareda bude baki zata kwala kiran Nurat Asamah suka rufe musu baki take suka fara kokawan kwacewa sbd ganin zaa tafi da Nurat batareda an gansu ba dan haka Abaas ya bude baki ya kira sunan Nurat din karfi sbd sunfi son a tafi dasu dukansu koma inane da a dauke dayansu abar saura su rabu. Cikin rashin Imani kuwa kusrawan suka juyo tareda biyo su Ayanah din wainda da kansu suka fito suna nufar Nurat da gudu suka rungume junansu su hudun suna fashewa da kuka. #MAMUH #ROYALTY #BEST LOVE #BOYEM #BOYEM PALACE HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070 8 *_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ******** ************ Wani irin kuka mai tsananin ratsa kunnuwa Ayanah ta fasa itada Nurat a lokaci daya suna rungume juna da tsananin karfin gaske jikinsu na wata irin rawa mummunan tsoron da basu taba shiga ba, Abaas da Zuhrah ma dukansu kukan sukeyi suna rungume junansu gabaki dayansu kowannensu jikinsa kakkarwa yakeyi musamman Nurat datafi shiga matsanancin tsoron dayake Neman juyar da kanta ita data shiga hannun kusrawan, Asamah da sakina ma qarasowa sukai da gudu suna kasa barinsu suka rungumesu kowannensu kuka yakeyi sosai sbd sanin rayuwa kuma ta tsaya musu daga wannan daqiqar. Magana Nurat ke son yi amma yanda jikinta ke fizga bakinta na kasa budewa sbd bata hayyacinta gabaki daya yasa Ayanah dake wani irin kuka mai tsanani itama jikin na rawa sake qanqameta jikinta tana kasa maganar itama, Hannunta daya ta saka ta sake qanqamo su Abaas da Zuhrah tana ambatar sunan Abaansu da karfi tareda Neman dauki daga ubangiji sbd bazasu iya rayuwan nan me cikeda tsoro ba basuda kowa a duniyar. Wata irin dariyar Jin dadi me karfi da ban tsoro tareda firgitarwa kusrawan sukeyi suna zagaye su tareda wani irin tsalle kaman sunga nama. Duk dan Adam din dazai sauke idanuwansa Akan kusrawa saiya shiga tsoro me tsananin gaske sbd kamanninsu da yanayinsu da rahamar Allah ta gama fice wa a rayuwansu sbd girma da yawan rayukan da suka raba da duniya babu tausayi ko Imani ko kadan, Ganinsu ko mafarki mummunan tashin hankali da tsoro ne sbd Al’adarsu ma da kadai yanayin shigarsu da wasu irin hudan kunnuwa dana hanci dake tattare dasu ga gashinsu da basa Daurewa a sake yake ga wainda basada gashina kuwa wani irin kitso ne me tsoro ga zane a jikinsu da shima alama ce ta kusrawa ga kowace kusra. Asamah ce ta bude hannuwanta tana karesu dan basu kariya itama jikinta koina rawa yakeyi tana jin wani iri kaman haukacewa zatai sbd yanda zuciyarta da kirjinta ke tsananin nutso a cikin qunci da tabarbarewan rayuwa data samu kanta na halin data saka rayukan da basu adadi tareda maida yara sama da daruruwa marayu, Tareda saka mata sama da daruruwa rasa mazajensu zasu zamo bayi, Yaya da iyaye sama da daruruwa sun rabu babu ranar haduwa har abada sbd kowa da inda ya gudu da kuma inda zaa siyar dashi. Juyawa kanta yaci gaba da yi zuciyarta da kwakwalwanta na sake kasa dauka idanuwanta na rage gani sbd haqqin ran daruruwan mutanen dake kanta, Rintse idanuwanta tayi tana sake ganin duhu kanta na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106