Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

itace tamkar kariya da kuzarinsa sai kuma mahaifinsa. Magani da kowane irin kokari anyi na kawar masa da hakan amma Sam babu nasara dan haka suka hakura suka barshi Akan lokaci kila zai iya sauyasa wata ran zuwa jarumin namijin da suke fata. Ghaz Ali ya bawa yayansa gata da dukkanin tar biyan da suke buqata tareda shaquwa me tsanani da sakewa a tsakaninsu, Dashi da yayansa babu boyo sai sakewa da kauna me karfin gaske, A duka fadin ANJOM GHAZ babu inda zasu gifta baa basu girma me tsanani ba, Girmamasu ake yi tamkar mahaifinsu ghaz Ali wasu guraren ma idan anje tamkar zaa bauta musu ake yi kasancewan zamani ne da musulmai da masu addini daban daban suke zaune kalau cikin aminci da kwanciyan hankali tamkar Yan uwa. Rayuwa a ANJOM GHAZ rayuwa ce da kowane dan Adam ya samu zaiwa Allah godia da samunta, Rayuwa ce da mutane daga duniya daban daban suke fatan samu sedai tayi musu nisan da baza su samu ba, Rayuwa ce ta kwanciyan hankali da nutsuwan da manyan Masarautu da dama basu samu ba sbd babu fitina babu tashin hankali, Gari ne da wasu garuruwan da dama suke kiransa da gidan kwanciyan hankali, Gari ne da basa karban bakon da basu San komai akansa ba bare Yan gudun hijira ko yan ci rani hakama gari ne da baya Aminta da kowane irin gari ko Masarauta ko wace iri sbd ikonsu suma dasuke Jin sunada shi. ************* Gyara tsayuwa Ghaz Ali yayi yana sake zubawa fadin dajin dabai iyaka idanuwansa yayi zuciyarsa na sosuwa da tsananin radadin masifar datafi kowace fara fadowa garinsa da zai iya bada rayuwansa dan basa kariya sbd garin anjom ghaz shine gata da rayuwar ‘yayansa da duk Ranar da suka tsallaka wajen garin suka barsa zuwa wata duniyar daga ranar kaddararsu zata sauyane zuwa wadda baisan ya rayuwa zatai dasu ba, ‘Yayansa sune rayuwarsa dayake tsaye cak akansu, Yayansa sune ginshikin rayuwan daya tsayu ya ginawa anjom ghaz, Yayansa sune bazai taba iya barin wannan masifar ta fadawa ba sai idan babu ransa a duniya, Mutuwansa fitar ransa a kirjinsa itace kadai zata Bari yayansa su fuskanci wannan masifar dayake Jin tamkar kirjinsa zai qone sbd Zafin baqin cikin dayake cikinsa, A taurin zuciya da Zafinta da Allah ya basa yasa ya zabi akawo masa gawar ‘yayansa kaf a jere a gabansa cewan sun mutu yafi masa Akan Ayi farautarsu zuwa a siyar a bayin wata qasar suyi qasqantacciyar rayuwar Bautar bayin da har kwanciya sarakuna ko yayan sarakuna zasu riqa yi dasu. Wannan zazzafan kakkarfan raayin na GHAZ Ali yasa duk Wanda yake ANJOM hakan ya kafu a ransa sun zabi mutuwa Akan a kamasu a tafi dasu bauta qasar da kaddararsu zata sauya har mutuwa. Matansu ma kusan hakan suka zaba mutuwa Akan barin a tafi dasu a maidasu dabbobin kwanciya da biyan buqata. Numfashi me zafi Ghaz ya sauke yana rintse idanuwansa kafin ya juyo ya kalli tarin mutanen da suka zo farkon garin dan gane wa ido da kuma tsoro daya fara shigar kowa na abinda yake tinkarosu sbd kaf a tarihi an sani duk garin da KUSRA( masu karfin safarar bayi da ikon siyar dasu qasashe qasashe na sarauta me karfin gaske) suka sakawa lamba to tabbas komai karfinsu to sai sun tashi garin sun tabbatarda duk wani me Sauran rai da numfashi a garin sun mallakesa sun tafi dashi sbd siyar da bayi ga manyan Masarautu. Mutanen ANJOM tinda suka fara samun Alaman Kusra garinsu suke hari take kwanciyan hankali ya fara qauracewa a anjom duk da shugaban gari bai nuna hakan ba amma sunsan wannan masifaffiyar kaddara ce da baza su iya kaucewaba idan ba ikon Allah ba hakama a garin baa tafiya gudun hijira idan ba shugabansu ne ya bada damar yin hakan ba. Abinda yake dan kwantar musu da hankali shine sanin baa iya shiga garin Kai tsaye sbd karfin nasu tsari da kafin da sukai duk da sunsan kusra nada karfin gaske suma amma kuma sanin su ne baa iya karya kafin saida jinin ahalin GHAZ dan haka tsananin karfin tsaron ahalin GHAZ ya tsananta baa Barinsu fita koina saida tsaron askarawa masu karfin gaske shi kuma Abaas kwata kwata ya Dena fita koina sbd ko wuqar jikinsa baa iya amfani da ita dan bama Kansa kariya. ****Gawar mutane sama da ashirin ne na mutanen ANJOM din da kusra suka kashe a Daren jiyan a wajen dajin Darin jere a qasa gaban ghaz Wanda yake sake kallan girman dajin yana tunanin yanda kusra suka samu damar isowa har gap da shigowa dajin garin Wanda sai an tsallako ruwa me karfi da yawan gaske duk da su kusra daman a ruwa suke rabin rayuwansu dan sunfi zuwa qasashe a jirginsu na ruwa me kamar gari dasuke tsallakawa da bayi Wanda yake dauke da dakunansu na bacci da komai na buqatan gudanar da rayuwansu dan bayinsu na kansu masu musu bauta da girke girke duk a ciki suke da nasa dakunan daban daban suna rayuwa hakama a inda suke zuba bayin da zasu siyar wa yana iya daukan sama da bayi daruruwa dan haka su babu Wanda ya taba sanin inda suke saidai idan Ka gansu kawai dan haka babu mai ikon daya taba kamasu sbd rashin sanin duniyoyin dasuke. Basu taba sanin akwai gari a tsallaken ruwan dasuke bi su wuce ba saida tsautsayi yasa suka bi wasu bayi da zasu Kama ba suka gudu har cikin dogayen itatuwan da suka rufe dajin hanyar garin daga Bakin ruwa dan haka Mutum ashirin da suka bi bayin suna ganin sun ratsa itatuwan binsu sukai suka ratsa ciki Wanda suna shiga tin anan mamakinsu ya fara dan haka suka bazu a dajin suka bisu. #MAMUH #SLAVERY #BEST MALE CHARACTER #LION OF BOYEM #BEST LOVE STORY #ROYALTY #BRAVERY #HISTORICAL #LOVE/HATE STORY HAYATEEM 700 0022419171 AccessBank maryam sani gummi 09033181070 [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 09033181070 2 Shugaban kusra subawa hanyar da sukabi idanuwa yayi sosai yana kalla yana Jin wani iri a jikinsa sbd duk inda aka samu hanya akabi to tabbas idan an kuwa ankai karshe komai nisa bazaa rasa inda zaaje ba a gurin. Gudun cetan rai bayin sukeyi sosai suna Waiwaye sbd mashin da ake harbo musu masu tsananin kaifi da dafin da take zai karya duka garkuwan jikinsu matiqar ya tabasu ko kadan ne. Basusan ina suke jefa kafafunsu ba bare inda suka dosa gudu kawai sukeyi na tashin hankali da tsananin tsoron da zuciya bazata iya dauka ba. Nisa suke Qarama suna kusantar hanyar ANJOM wadda take cike da hadari batareda sun sani ba. Cikin tsananin rashin Imani da babu ko Kadan a ran wainda suke biye dasu Wanda yake kaman shugaban Sauran ya bude baki yana tsaya wa daga gudun dayake ya Fiddo harshensa dayake da duhu sosai ya lashi fatar bakinsa dayake baqi qirin ya daga Kai sama yayi wani irin Ihu me karfi kafin ya sake dariya kaman me ciwon aljanu ya bude murya sosai yace ‘Dayan zuciyarsa nakeso a hannuna kafin ta Dena bugawa daga fitowa kirjinsa, Dayan kuma idanuwansa nakeso zanyi wa dass sarka dasu a wuya’ Sauran na Jin hakan suka qara gudu suna sake Harba musu arrows masu

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});