Chapter 41
Chapter 41
kyau da kashe jiki akan fuskan Zuhrah wadda itama dagowan tayi ahankali. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:47 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 27 *_UMMU ASLAM COLLECTION_* 08035014107 -Ina mata yan kwalisa masu son burgewa? -Shin Kayan kitchen na zamani masu sauki da rahusa na kitchen din yan gayu dama na gargajiya kike so? -shin abayas na yayi da daukan ido da burgewa kike nema? -kokuwa original misk dahara kuke buqata dan asali? -kokuwa Kayan GHT na Neman lafiya da gyara kike so? -ke harma laces da atampopi na alfarma masu sauki kikeso? To duka kinzo gidansu indai sune abinda kike buqata ba bata lokaci kinzo kin gama samu kawai tintibi UMMU ASLAM COLLECTION 08035014107 duk inda kike zata aika miki batareda bata lokaci ba. ********* Idanuwansu na haduwa sarewa Ayanah taji kafafunta na Neman yi ta dafa bango ahankali wannan Karan hawayenta gangarowa sukeyi suna sauka fuskanta har zuwa kirjinta ta rintse ido wani yanayi na cikata ta sake bude idanuwanta akan Zuhrah dake kuka sosai itama tana jin kafafun nata sun gaza, Ahankali suka tako zuwa juna babu kowa dake ganinsu dan haka suna qarasowa wata irin runguma sukaiwa juna Ayanah na zubewa qasa Zuhrah ta bita qasan suna rungume da juna qamqam kaman zasu shige jikin juna, Kuka sukeyi sosai kaman ransu zai fita mara sauti sbd kada a jiyo su, Hannuwan Ayanah suna wata irin rawa ta kamo fuskan Zuhrah ta tsira mata ido hawaye na gudu sosai akan fuskanta tsawon mintina kafin takai bakinta ta sumbaci goshinta ta sumbaci gefen fuskanta ta sumbaci tsakiyar kanta ta kamo hannuwanta suka ta sumbata koina jikinta rawa yakeyi sbd jin kaman zata Hadiye Zuhrah, Zuhrah kuwa batada Sauran kowane irin kuzari qanqame Ayanah din kawai takeyi tana kuka kaman ranta zai bar jikinta jikinta na rawa itama sosai, Magana sukeyi wa juna amma ba daman hakan sbd zaa iya jinsu dan haka babu Wanda ya iya bude baki a cikinsu sedai ido da hannuwansu ke aiki, Zuhrah duk yanda taso kasa riqe kanta tayi ta gama ficewa hayyacinta kamo fuskan Ayanah tayi da tafin hannuwanta biyu takai bakinta kan kunnenta ta bude baki da wani irin sauti daya saka gabaki daya dan Sauran karfin halin Ayanah rushewa tace ‘Yēne Ayanah(my Ayanah),hiyiwēteni(my life),Yene widi(my precious)’ Rintse idanuwa Ayanaah tayi tana sake qanqame Zuhrah kafin ta bude bakinta cikin tsananin sanyi da mutuwan jiki tace ‘Ina rokon Allah ya zama gatanki Zuhrahna ya baki kariya da juriya tareda ingancin rayuwa, Bazan taba barin a gurbata rayuwanmu da alaqar mu ba, Duk halinda zamu shiga bazamu taba zama a cikin qazantacciyar alaqar da akeson mu zauna ba,zan baki kariya da rayuwata koda bama tare, Zan zabi mutuwa akan a hada mu a qazamiyar shimfidar mu yada mummunan zuriar datake ta Allah wadai a garemu matiqar muka hada shimfida da Mutum daya…..’ Kuka sosai Zuhrah ke qarawa sbd maganganun Ayanaah din dake sake kashe rayuwarta sbd sunzo gabar da kaddarar tayi musu muni me girma bama girma ba, Duk shauqin ganin junansu Ayau Bayan shekara guda bai taho musu da alkhairi ba dan kuwa wannan shine mafi girman quluwar kaddararsu da basusan tayaya zasu fuskancetaba kuma tinda aka zabesu din to tabbas Ana nufin sai sun sauke buqatar sultan din BOYEM Wanda mutuwar dayansu ce kadai zata Hana hakan idan kuma sun fito sun bayyana alaqarsu sbd Kaucewa hakan to dukansu ne zasu rasa ransu sbd sun aika laifi me girma ita kuma a yanzu tanason ko yayane dayansu ya rayu sbd Abaas dayake raye a duk inda yake. Sun jima a hakan kafin daqyar suka iya rabuwa da jikin juna sbd motsin fitowan wasu wanka dan haka kai tsaye a sanyaye suka fada toilet daddaya suma take suka sakar wa kansu ruwa sbd kukan ruwan ya hana aji sautin kukan dasuke fasa a tare. Sun jima a toilet din kafin suka fito kusan a tare suka fito kan kowannensu a qasa batareda sun sake kallan ko inda inuwan juna take ba. Haka aka fice dasu zuwa inda zasu zauna kowannensu da Wanda zai taimaka masa zama a dakinsa dan sai wadda sultan ya kwana da ita zaa warewa bangarenta me girma da bayi idan ta samu ciki zata cigaba da zama idan bata samu ba sultan ya gama yayinta tafiya ake da ita. Kwata kwata ba guri daya aka aje su ba kowa da dakinta daban dan haka suna dawowa ba jimaw aka kawo wa kowacensu lafiyayyun Kayan itatuwa da zallan madarar nonon raqumi me dumi da zuma tareda duk wani abu dazai Kama jikin mace na qarin Ni’iman nace me karfin gaske. Sakinah aka kawowa Ayanah wadda taje taji jikinta ya sake mutuwa Ana rufe musu daki ta zube gaban sakinah tana kuka me karfi da Neman yaya zatai da rayuwarta da wannan sabuwar kaddarar. Sakinah ma kukan takeyi cikin tashin hankali da rashin sanin tinanin yi dan kuwa wannan Karan ko ita batada shawarar bayarwa sbd abu dayane a bayyane tabbatacce kuma shine Allah ne kadai zai Hana dayansu barin duniya kokuma su dukan ma. Kuka sukeyi tare tsawon lokaci kafin aka taba kofar dakin wadda ta sakasu shire hawayensu suna Miqewa tsaye kansu a qasa sakinah ta bude dakin. Tenya ce da kanta tareda masu Binta a baya kaman zasu mata sujjada, Shigowa tayi tana kallan fuskan Ayanaah din wadda fuskanta ta kumbura sosai tayi jajir alaman kuka me karfin gaske tayi, Ajiyan zuciya ta sauke a natse tana sake kallan Ayanah din cikeda mamaki da tinani Kala Kala sbd tinda aka kafa tarihin masarautar babu macen data taba kuka akan zaa kaita shimfidar sarki duk kuwa tsoro da fargaban da matan suke shiga babu wadda ta taba kuka na bayyane sedai na boye na zuci amma Ayau idanuwa da komai na jikin Ayanah bayyanarda tsananin qiyayyrt da hakan yakeyi. Numfashi ta sake saukewa tanajin haka kawai Ayanah din takeson ma idan sultan YASAR ya sauko a Daren ya fara tarawa da ita tsawon sati guda kafin ma a sake kai wata. Murmushi me kyau ta sauke ahankali tana sake qarewa zallan kyau da wani irin sanyi da nitsuwan Ayanah din ido ta bude Baki tace ‘Yaya sunanki?? Sai a lokacin Ayanah ta motsa tareda dago manyan idanuwanta ta sukai jajir ta bude bakinta da sauti me tsananin sanyi da mutuwan jiki tace ‘AYANAH GHAZ’ maimaita sunan tenya tayi cikin kulawa da jin Ayanaah din na shiga tinani da zuciyarta tareda jin tabbas da tanada ‘da namiji yanta Ayanaah din zatai ta aura masa sbd tanada abubuwan da duk takeson mace ta mallaka dan haka koma yayane Ayanah sultan YASAR sai ya maidata cikakkiyar mace. Take ta bada umarnin duk abinda aka kawo na Shan a bawa Ayanah a gabanta ta shanye, Hakan kuwa akai haka aka fara dauko su daya bayan daya Ana bawa Ayanaah din tana shanyewa hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga idanuwanta Wanda ya saka tenya sake jin Ayanah na zama dole imebēti. Su tenya na ficewa Ayanaah ta darare ta zauna bakin gado tana kallan koina na dakin babu kowane irin abu dazai Baka ikon daukan rayuwanka dan haka zame wa tayi qasa tana jin kaman
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106