Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

abin kunnayen Ayanah tayi a hannunta tana dauke kanta daga kallansu su duka kukanta na Neman tsananta amma dole zata aikatawa dan uwanta hakan. Zuhrah ce da itama kukan takeyi ta miqe tsaye tareda Kama hannun Ayanah ta kasa maganar da zatai sbd kukan dake zuwar mata sabo mai ciwo dan haka juyawa tayi itama tana Dora hannunta a kirjinta dake ciwo da nauyi. Rarrafowa Ayanah tayi cikin mummunan gaban Abaas din tareda daga hannuwanta dake rawa sosai takai tafukan hannayenta fuskansa ta tallafo ta kallesa ya Lumshe idanuwansa yana kasa barin taga tsananin rauni da baqin ciki tareda quncin dayake cikinsu sbd kada ya qarasa karya zuciyarta da gangar jikinta. Bakinta takai kan gefen fuskansa ta sumbacesa hawaye na gangaro mata kafin ta sake dorawa kan goshinsa ta sumbacesa hawayenta na diga kan goshin nasa. Zuhrah ma cikin karfin Hali tana danne zuciyarta ta juyo ta durqusa gabansa ta Kama hannuwansa biyu ta sumbacesu duka kafin ta sumbaci tsakiyar kansa da gashinsa me tsayi kaman mace yake daure har lokacin. Tafin hannu Ayanah ta bude ta kalli yan kunnayen kafin ta daga ahankali tareda Kama kunnansa, Bude idanuwansa yayi ya sauke Akan fuskan Ayanah din wadda cikin idanuwansa take kallo tana masa kallan tsananin kaunar dake nuni da har abada idan kowa zai gujesa su suna tareda dashi har mutuwa sbd su a gurinsu rasa kowace darajarsa ba ta ‘da namiji. Baice komaiba Bayan rufe idanuwansa da yayi ahankali sbd su kadai yake buqata a rayuwarsa daman kuma idan yana tareda su shikenan zai iya jure komai. Hannunta ta Dora a kunnansa cikin radadin zuciya ta huda kunnan nasa da karfin da na karfin hali ne, Zuhrah kaman a zuciyarta haka taji hujin kunnan shi kuwa ko motsawa beyiba sai wasu hawayen da bana radadi bane suka gangaro masa. Haka Ayanah ta huda Dayan kunnan tana bar masa yan kunnayen a kunnuwansa. Tallafe fuskansa ta sake yi da hannuwanta tana kallan idanuwansa dake rufe yana riqe kukansa me tsanani dake zuwar masa. Itama kokarin riqe nata takeyi har saida Zuhrah ta saka hannunta cikin riqe nata kukan itama ta zare daurin gashinsa take gashin ya sauka har kafadarsa, Wani irin kuka me karfi da gunji suka sake a tareda dukkaninsu suna rungumesa. Har lokacin Sakinah bata juyoba itama kuka takeyi sosai a yanda take, Nurat ma kukan ta fasa tana fadawa cikinsu tareda ambatar Ayanah da AMMA itama. Rigar Zuhrah me dan adon Kayan mata suka zare aka saka masa tasa kuma Zuhrah din ta saka. Sakinah ce ta matsa kadan gaba ta Debo wani ganye shar ta kawo Ayanah ce ta murza ganyen da hannuwanta biyu ta goga a fuskan Abaas din Wanda bazai bazai taba barin gashi ya fito a fuskansa ba. Sake rungumesa Ayanah tayi suka sake samun Yar nutsuwa da dangana kafin suka miqe suna kama hannuwan juna suka bi hanya ahankali cikin galabaita Wanda babu ta yanda zaka zan akwai namiji a cikinsu.. Koda rana ta fadi babu me iya tsayuwa sosai a cikinsu sbd tafiya da azaba, Kafafunsu dukansu babu Wanda bai fashe ba, Kaman a mafarki suka fara hango ruwa me yawan gaske yake dukkaninsu suka Ji sun samu dan kuzarin daya qare musu. Ruwan suka nufa suna jin maqoshi da jininsu na sake qafewa. Ana magrib suka isa ruwan Wanda da rarrafe dukkaninsu suka qaraso sbd qarewar karfi gabaki daya, Nurat bata iya qarasowa ba sbd ranta dake gap da fita dan haka Abaas ne yayi saurin diban ruwan da hannuwansa biyu yana kawo wa inda take yana bata a baki batareda damuwa sa qazantar dake ruwan ba. Daqyar yake takawa yana kai mata ruwa yana zuba mata a baki har shima ya gaza ya fadi yana zubewa a gurin. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 10:46 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 10 *_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ******** Ayanah datai tsananin laushi itama ce ta qaraso gurinsa da rarrafe cikin sauri tana kokarin kamo sa amma hannuwanta rawa sukeyi sosai gashi bata da kuzari sai kuma ta kasa iya Dena kokarin rungumosa jikinta idanuwanta da sukai surfi sosai suna kasa ko hawaye. Sakinah ce da itama taje Numfashi daqyar ta matso ta fara Debo ruwan itama a hannunta tana tahowa tana zubewa a bakinsa suka samu yasha sosai numfashin sa ya fara daidaita ya rufe idanuwa yana lashe lips dinsa da suka bushe qayau harsun fara tsagewa. Ayanah ma Sakinar ce ta kawo ruwan ta ringa bata ta dan samu karfi da kuzari itama tana lashe bakinta daya bushe ya tsatsage. Acan bakin ruwan sakinah tasha ruwan sosai itama kafin ta zube a gurin a kwanta tana sauke Numfashi bakinta itama yana samun sassaucin azabar yankewan bushewa. Zuhrah kuwa daman tana bakin ruwan tin dazi a kife Jin takeyi kaman ta fada ruwan ta sanyaye jikinta da bakinta da suka bushe har sun yayyanke musamman kafafunsu da basuda kyalla sun fashe kace kaca sunyi wata irin Dauda da munin kalla. Ba iya kafafunsu ne da munin kallo ba sbd Dauda me yawa hadda su sbd dauda ce sosai a jikinsu tareda jinin da sukayo gwagwarmaya dashi daya bushe a jikinsu tin daga kan na Ammansu dama Abaansu da Ayanah ta taba saina Asamah dama Sauran wainda aka kakkashe tin farkon barowansu babu me Kyan gani a cikinsu sbd sun koma wata halittar sbd dauda da kyama. Dukkaninsu kwance suke a gurin babu Wanda ya motsa Numfashi suke sauke wa a hankali ba kuzari kuma ma idan sun miqe basu San tayaya zasu tsallaka ruwan ba bare dan haka magana ce ta sake zagayawa dajin zasu yi Neman hanyar da zata fiddasu inda ba ruwa su fice daga nahiyar gabaki daya su fada inda garururwa da Jamaa suke. Shiru sukai kowa idanuwansa na kasa qaqaro hawayen tashin hankalin inda zasu sake komawa dan Neman hanya. Kasa tashi kowannensu yayi a gurin anan suka kwana kwance gaban ruwan kowa a inda yake zube anan ya kwana sai asuba suka dan iya tashi suka hade guri daya suka dunqule sbd tsananin sanyin ruwan dayake ratsa su. Daqyar suka iya sallah Bayan gari yayi haske suka sake Zaunawa guri daya a hade kaman kashin awaki, Shiru sukai suna tinanin yanda zasu sake komawa su kutsa cikin dajin Wanda basu San ranar

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});