Chapter 32
Chapter 32
haka aka kuma kiransu aka raba abinci sukaci suka kwanta Wanda take baccin wuya ya dauke dukansu kamar bugaggu Wanda basu saniba harda maganin bacci ake basu sbd anason su samu ishashen baccin da zai warware qwaqwalwarsu ta sake sbd gudanar da rayuwarsu a natse dan komai a BOYEM nutsuwa ce tsagwaranta yake buqata. Washe gari ma haka aka kuma basu ci da wanka tareda magani suka wuni suna bacci da hutawa, Duk yanda zuciya da kwakwalwan su Ayanah yake cikin wani irin qunci da damuwa me nauyi maganin da aka Dora su akai fin karfinsu yayi bacci suke yi sosai batareda sunsan ma tayaya kansu ya fara sakewa ba yana dan dawowa da tinaninsu Akan hanya daga fatan mutuwar da sukewa kansu kullum. *****kaman yanda doka da kaidar Masarautar BOYEM take sai anyi sati biyu cif Ana basu abinci fa Hutu sosai kafin Ayi wata daya Ana horar dasu komai na masarautar Bayan an gama tababbatarda sun yadda ce tarihinta da sanin kowane irin bayani Akan bautar da zasuyi dakyau Wanda idan Baka da qwaqwalwar haddace komai da riqe komai kan hidimar dake gabanka shine ake Tura Mutum bangaren wahala da azaba inda zaka gwammace rayuwa a wata qaramar masarautar daji da babu gabas bare yamma. Haka su Ayanah suka share sati biyu Ana basu Hutu duk da babu Wanda yake cikin dadin zuciya ko kadan a cikinsu amma jikinsu da fatar su ya samu lafiya sosai dan kuwa ko gurin Kwanciyansu a tsare yake da tsafta da dokoki, Sun sauya sosai gangar jikinsu ta samu nutsuwa dan haka aka fara koyar dasu mataki ma biyu Wanda kullum ne ake koyar dasu yanda ake aiki da komai a masarautar irin su wanke toilet da gyara tareda iya aikin koina da yanda zasu iya fuskantar rayuwarsu idan sun tsayu a gaban duk Wanda yake jinin BOYEM. Rayuwar bayin BOYEM hatta inda zasu iya dagowa su kalla a qayyade yake hakama yanda zaka iya bude baki ko fidda Numfashi me sauti a gaban jinin BOYEM Akan kaida da doka yake hatta dukkanin gangar jikin bawa da abinda yake gangar jikinsa Akan kaida da tsari tareda amarni yake. Wasu irin kaidoji da dokoki tareda tsari masu tsauri da karfi aka fara dorasu dan kuwa ko tafiyarka a tsari take aka dorasu, Lokutansu na bacci da fitowa fara aiki tareda wata irin tsaftar gaske duka Akan tsari suke da yanda ma zaka dago kai Ka iya kallan inda kake sbd kaida ne koyaushe Kanka ya zama a qasa, Duk jin dadi da nutsuwar da suka samu a BOYEM din tsari da dokokin tini suka daga hankalinsu tareda shiga tsoro me tsanani sbd laifuka da kurakuran da zasu iya rabaka da ranka a masarautar yawa ne dasu sbd mafi yawan hukuncin kasar cire kai ne kawai kokuma ciyar da dabbobi namanka dan haka babu Wanda yake yadda komai tsananin tsautsayi yayi laifi dan tsira da rayuwa, Mataki mataki ne na bayin masarautar sai Wanda yakeda matakin saar karshe ta rayuwa yake samun damar yin aiki a inda asalin jinin BOYEMs din suke. ***Ayanah da Zuhrah harma da sakina basuda Sauran kowane zabi Bayan mayarda hankali suna daukan karatun da ake musu tareda samun qarin nutsuwa sbd a yanzu damuwa da kuncinsu a natse ma yake cinsu, Sun sauya sosai kawai dai quncin dake kwance a zuciyarsu ne yake hanasu yin jiki ko mulmulewa suna nan basu wani qara kiban komai ba kawai dai yunwa tabar jikinsu. Kullum da safe a kaida da doka zasuyi wanka su shirya a cikin uniform dinsu tsaf tsaf su isa gurin karban abinci abi Layi su karba abinci su ci kafin masu wucewa aiki su wuce su kuma su isa inda ake karantar dasu acan suke wuni sai yamma suke dawowa. Sakinah data Saba da bauta zuwa yanzu ta sake ta karbi sabuwar rayuwarta da babu matsi hannu bibbiyu tareda samun nutsuwa da gode wa Allah daya rayar da ita ta fito daga hannun kusra batareda rasa komai nata ba dan haka a yanzu batada doguwar damuwa saita Ayanah wadda koda minti daya quncin dayake zuciyarta bai taba fita ba zuciyarta a qulle take tamau da wani irin qunci da damuwan da har abada kila bazasu fita ba dan rayuwarta ta Riga tayi rushewan da bazata taba gyaruwa ba, Tana komai Akan lokaci tareda komai da ake Dorasu akai a natse babu hayaniya babu rawan jiki komai nata yayi sanyi ya koma zallan nutsuwa bata sake bude baki ta Ambaci Abaas ko Nurat ba komai ta tattara ta ajiye sa a cikin zuciyarta yana cin lafiyanta da kwakwalwanta a hankali ahankali batareda sanin kowannensu ba, Sakinah datafi su wayo da shekaru sosai ta fahimci Ayanah ta kafe komai a tsakiyar zuciyarta Wanda illar da hakan zai mata tasan mai yawa ce sbd ta riqe baqin cikin da quncin gam a cikin rai ta kasa fitarwa amma ganin bata nuna ba tana komai na rayuwarta a natse ya saka bata ce komaiba sai itama ta sake sbd tinanin insha Allah lokaci na tafiya quncin kila zai ringa wankewa yana ficewa daga ranta. Zuhrah da farko mamakin Ayanah ta ringa yi ta yanda ta Dena maganar su Abaas kwata kwata da iyayensu ta nutsu duk da tayi sanyi sosai kaman ba ita dinba ko dagowan magana bata iya yi yanzu Wani irin miskilanci da son kadaici ya aureta, Zuwa yanzu kusan sunsan koina a bangaren nasu na bayi da yawan bayin da suka taho tare sun sake sun karbi wannan rayuwar dari bisa Dari farin cikinsu sukeyi da walwala tareda jin dadi, Suna Sauran sati daya a kwashe su zuwa cikin asalin masarautar subar daular bayin hankalin Zuhrah ya tashi sbd tsananin tsoro da fargaban shiga BOYEM palace take dan abu daya ne akace a cikin biyun matiqar Kafarka ta shiga gate din masarautar aka rufe to tabbas gawarka ce kadai idan lokaci yayi zata fito bauta ce zakai har tsawon ranka sai kuma idan Ka zamo daya daga cikin bayin da zaa riqa kwanciya dasu Ka zama abar kwanciya kenan a duk lokacinda aka ga dama har tsufanka shima kokuma idan an gama jin buqatar kusantar taka zaka koma tamkar fankon da baida Sauran amfani a duniya shikenan. Wannan tinanin ne yake saka zuciyar Zuhrah shiga mafi girman tsoro da tashin hankali harma firgita takeyi a cikin baccinta duk tabi ta firgice ta rasa nutsuwarta ga yawan mafarkin Abaas da Nurat datake suna zuwar mata cikin yanayi na tsananin tausayi. Yanayin ya saka ta fara kasa maida hankali Akan karatun da ake musu ta fara zama yanayi na kaman tana Neman fita hayyacinta, Yau ma cikin damuwa me tsananin yawa take zaune ta kasa saka Kayanta daya fito wanka ta qurawa guri daya ido hannuwanta qanqame da uniform dinta kanta bai ma San tinanin dayake ba. Ayanah ce ta fito wankan daure da abin wankanta me tsayi da kauri fatar jikinta ta samu lafiya sosai haskensu kusan duka ya kusa dawowa, Cikin sanyinta da rashin hayaniya ta dauko uniform dinta zata saka Zuhrah daya zuba mata idanuwanta da sukai jajir zuciyarta na Wani irin zafi da quncin dayake lullabe dasu ta bude baki idanuwanta na cikowa da hawaye tace, ‘Ayanah kin samu sabuwar rayuwar data mantar dake abaas na can
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106