Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 100

Chapter 100

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ba azaba ba tozarwa ba hantara ba qyama a tsakaninsu dashi ya saka suka samu matsayi a zuciyarsa musamman ayshaah dayake kallo kaman yar uwarsa sbd sosai take kaunarsa. Shi Kansa boukar sosai yake da nutsuwa da kwanciyan hankali idan yabarsu tare sbd ya yadda da yarsa zata samu samu kulawa tamkar yananan koma fiye a gurin Nurat kaman yanda ya fada musu sunansa kenan a rubuce da larabci. Bayan sabo shekarun suna dake nitsawa shaquwa me karfi ta shigesu sbd a yanzu ya koma tamkar Wani bangare ja rayuwarsu dan haka a yanzu tamkar ahalin mutum uku suke jinsu duk da haryanzu har gobe shi bawan su ne amma akwai kauna da kulawa tsakaninsu sbd tsananin biyayyarsa da rashin hayaniyarsa. Saida yayi shekara kusan goma a hannunsu tukuna sukasan asalin jinsinsa da tintini boukar ya fahimta amma bai nuna masa ba sbd son qure lamarin Wanda baisan ina ze tsaya ba dan haka ya fuskunci hukunci me tsanani a gurinsa kafin kuma daga karshe ya barsa a macensa cewa shine hukuncin sa haka zaici gaba da zama tamkar dan daudu. Baiji ciwo da Zafin hukuncin ba sosai sedai Ka quncin sa daya dawo sabo na rashin yan uwansa a rayuwarsa dayake ganin batada Sauran amfani a gurinsa, Yanayin alaqar sa da ayshaah sauyawa tayi sbd jinsinsu daya bayyana ba daya ba dan haka ta rage shige masa sosai hakama ta Dena bayyanar da inda be kamata ba a jikinta indai suna tare sbd kiyaye dokar addini. A hakan sukaci gaba batareda sun sauya masa tako wace hanya ba ko kadan, Kaf garin sun San Nurat a matsayin bawan ahalin da shine bawan da zai zama na ahalin me zuwa dan kuwa idan har boukar ya mutu Nurat yana cikin gadon da zaa raba maana shi Kansa abinda Wani ze iya gada ne a gurin rabon gadon Wanda yan uwansa keta lissafi sbd arzikinsa yayi wata irin sake habbaka ya tara dukiya ke yawan gaske data saka yarsa taje rayuwa tamkar sarauniya a fada, Da farko Bayan angane Nurat namiji ne ba mace ba mutan gari sun so korarsa sbd jifansa da ihu aka ringa yi masa daga kasuwa da aka aikesa Wanda Koda ya iso gida sun masa mummunan illar data sauya masa kamanni sosai sbd jifar ta fasa Kansa da fuskarsa amma a hakan ya iso gidan baya ko gani sosai sbd jinin daya rufe idanuwansa. Da karfin dukiya boukar yayi amfani ya hana a kori Nurat din amma kuma tin daga wannan lokacin Nurat ya zama abin qyama da hantara tareda jifa a cikin mutane a duk lokacinda zai fita gashi har lokacin shigar mata yakeyi, Tsananin tsana da qyama tareda hantarar dayake fuskanta a rayuwarsa tsawan shekara kusan uku ya saka rayuwarsa gabaki dayanta komawa asalin baqin ciki da qunci dan haka sai abin ya fara taba zuciyarsa da daman bata taba fita tsananin qunci ba. Wasu bayin boukar ya siyo guda biyar masu karfi dan gadin gidansa da ako Yaushe ake kokarin kawo harin Kai karshen rayuwar Nurat din Wanda kaf garin suke ganin mugun abu ne a cikinsu zama da zabgegen namiji a cikin Kayan mata dan haka koda be bar garin ba to zasu kashesa dan zamansa a garin tamkar zunubi ne. Cikin wannan fitinar dake tashi koyaushe yan uwan boukar dake harin rayuwarsa suka shige sbd samun biya da cimma burinsu na shekaru masu yawa akansa sbd a yanda Nurat ta zama rayuwarsa da ‘yarsa bazasu iya rabuwa dashi ba dan haka suna samun ya fara shirye shiryen barin garin da Nurat dan komawa Wani garin suyi rayuwa hankali kwance tinda yanada dukiyarsa me yawan gaske. Ana cikin wannan halin rana tsaka kwatsam cikin dare kawai aka cinnawa bangaren abincin boukar dake gidan wuta inda tarin dukiyar abincin sa take me yawan gaske buhuhuwan hatsin da dukiya ce me tsananin gaske, Fitowa boukar din yayi cikin duhu da hayaqin daya gauraye gidan har Baka ganin komai yana kokarin isa bangaren idanuwansa da kunnuwansa sukai masa mummunan ji da ganin daya tabbatar masa da halin yan uwansa dayake zargi na shekaru masu yawa dan haka da sauri ya juya cikin hayaqin jikinsa na rawa zuciyarsa na Wani irin radadi da firgici sbd lamarin Yazo masa a bazata. Fada ne ya fara kaurewa da hayaniya tareda ihu a gurin kashe wutar wadda duk da tsakiyar dare ne amma take mutane da suka cika gurin da sunan kashe wutar da kuma son qaddamar da nufinsu a cikin hayaniyar kashe gobarar na kashe Nurat su kuma yan uwan boukar kashe sa dan hakanne ma suka fada sun tada wutar yanda zaa hargitse ana ihu da hayaniyar kashe wuta su kuma sukuma su aikata aikinsu tareda sace dukiyarsa dan haka basu taho da shirin barin ko ‘yarsa ta rayu ba bare bawansa. Fada aka fara tareda sare sare Ana fidda jini me yawa sbd bayin dake tsaron gidan da sukaga alamar fitina a tattare da kashe wutar dan haka suka fara hanawa sedai ko gama rufe baki na farkon beyiba suka rufu a Kansa suka sassarashi suna cewa shi bawa ne bai isa ya basa umarni ba sedai su su basa. Jin hayaniya da Ihun kashe karshen daya dauki gari ya saka boukar daya dauko makaminsa dakatawa ya juya ahankali ya kalli kofar dakin ayshahh sai kawai yaji tinaninsa ya sauya ko yayane yanason ‘yarsa ta rayu dan haka ya nufi kofar dakin da Nurat yake kwana yana zuwa Kai tsaye shiga dakin yayi ya tadashi da karfi tareda dagosa daga kwancen batareda yace komaiba ya riqo hannunsa da karfi suka fito tsakar gida yana sake shiga tashin hankalin hayaniyar da Ihun daya qarasa gauraye gari. Abaas na fitowa yanda wutar take ci da Ihun da akeyi ya sakasa jin Kansa na Juyawa zuciyarsa na bugawa da karfin gaske komai na yanda ya faru garinsu yana dawo masa sabo. Wani irin Zafi da tiriri yaji yana tasowa daga zuciyarsa yana gauraya jininsa komai na sake dawo masa tin daga gawar magaifiyarsu da suka fara rasawa. Rawa jikinsa keyi kowane irin radadin daya dandana a baya yana dawowa yana zama kuzari da fushinsa dan haka dagowa yayi idanuwansa jajir da wasu irin hawaye a cikinsu sbd bazai taba yadda ya sake shiga hannun kusrawaba koda zai rasa ransa gurin cetan Kansa da ayshahh da boukar sbd har abada bayason su dandana baqin cikin daya dandana shi da yan uwansa musamman ayshaahh datake mace, A baya rauni da rashin karfi ya sakasa zamowa nace yana kallo baida abin yi Bayan kuka aka tarwatsa rayuwar yan uwansa aka kashe masa Nurat dan haka wannan Karan a yanzu daya zama namiji ya zabi mutuwa Akan tafiya wannnan mummunan rayuwar. Takobi da adda boukar ya basa yana kallan Zafin dayake bayyana a cikin idanuwansa yace ‘Ka tabbatarda Ka bawa Kanka da Ayshaah kariya’ Wucewa gaba boukar yayi da dan gudunsa na fuskantar komai ai kuwa yana fita take fadan ya dawo Kansa amma dayake yanada nasa karfin sosai haka ya ringa fadan dasu. Shima Abaas baisan lokacinda ya fado cikin fadan ba idanuwansa a rufe komai na abinda ya faru dasu kawai yake gani dan haka kusrawa kawai yake gani a idanuwansa ya ringa fadan bayaji baya gani. Fin karfinsu fadan ya

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});