Chapter 12
Chapter 12
Juyawa sosai amma har lokacin karesu takeyi da hannuwanta, Jin kaman zuciyarta na Neman bugawa ta juyo tsoronta da tsananin tausayinta akansu na qaruwa sbd sun riga sun rasa yanci da gata harma da asalinsu tareda rayuwansu batareda sun San yaya duniyar take ba a wajen gidansu,a kuma wajen garinsu,a Bayan ran iyayensu, Basusan yaya zasu gudanar da rayuwarda babu iyayensu a cikinta ba koda iyayensu na raye bare yanxu da basa duniyar, Ko a darasin ilimin rayuwa da iyayensu ke musu tareda tarihi da labarun rayuwar dake gudana a duniya wadda baa cikin ANJOM ba baa taba fada musu menene asalin zamowa bawa ba da ukubar dake cikin bauta wadda bakasan karshentaba ko Ka samu yanci wata rana kokuma Ka mutu a cikinta. Wani irin Jan rikitarwa idanuwanta suka tana saka hannunta daya a kirjinta tana dafewa Ahankali ta kalli Ayanah tareda bude bakinta ahankali ta Ambaci sunanta kafin ta maida idanuwanta Akan Abaas datafi shaquwa dashi tareda tsananin kauna a tsakaninsu me karfin gaske ta qura masa ido wasu irin hawaye masu tsananin ciwo na gangaro mata ta sunkuyar da kanta qasa tana jin rayuwarta kwata kwata bata da sauran amfani. Dagowa tayi ta kalli kusrawan da sukayo kansu kowannesu na zaro mummunar wuqar da zata yanka Mutum a qanqanin daqiqu fit ta rabaka da ranka. Lumshe idanuwa Ayanah tayi suna sake rungume junansu dukkaninsu suna samun nutsuwa da saukin a rabasu da ransu su bi iyayensu yafi musu saukin rayuwan da basusan yaya ake gudanar da itaba, Rayuwar da babu tabbacin ko zasu take ko wahala da gagari zasu yi karshe su mutu a cikin garari dan haka gwara tin a qasar garinsu batareda sun bar garin da gawar iyayensu take ba subar duniyar. Abaas dayansu ya fizgo da karfin gaske yana Dora wuqa mai tsananin kaifi da wani mummunan fadi a wuyansa zai fizge jijiyar wuyansa da wuqar Asamah ce da idanuwanta ke cikowa da hawaye masu radadin gaske ta bude baki jikinta na saki tace ‘Inada damar alfarma guda daya tak da khams ya bani a matsayin abinda zaa biyani dashi kuma dukkaninku kun San da hakan’ Cikin rashin Imani Wanda yake riqe da wuqar a wuyan Abaas yace ‘Damarki guda daya ce tak kina fadarta shikenan kin rasa kowace irin dama…… Katsesa tayi muryanta na sake raunana da cewa ‘Kar a kashe ko dayansu shine abu daya tak danake so…… Dukkanin kusra dariya me karfi suna kece da ita kafin babban cikinsu ya kalleta cikin tinatar da ita babban gangancin da zatai wa rayuwarta sbd Ana cika mata wannan buqatar ita rasa nata ran zatai yace ‘Kina sane a dama daya tak da aka baki zaki iya zabar abarki da rayuwarki kitafi duk inda zaki ki Gina sabuwar rayuwa? Kina sane da hakan? Sannan Kina sane da idan kika zabi rayuwarsu ke bazaki rayu ba??? Gangarowa hawayen cikin idanuwanta da sukai jajir sukai ta juya sake kallansu babu Wanda jikinsa baya kakkarwa cikin wani irin mummunan halin daya saka zuciyarta sake nauyi, Abaas ta zubawa idanuwanta idanuwansa na rufe yana jiran barin duniyar kafin ta dawo da idanuwanta Akan Ayanah dake kallanta cikin yanayin da suka fi buqatan mutuwan Akan rayuwar Zuhrah ce ta iya bude baki da tsananin kuka me ratsa zuciya tace ‘Asamah mun zabi bin iyayenmu dan Allah karki zabi barin mu kema sbd kece wadda a yanzu muke kallan zaki zame mana ido a wannan rayuwar da muke makafi bamusan komaiba dan haka munfi tsananin buqatan komawa ga mahaliccinmu kaman iyayenmu…… Ayanah data kasa magana sbd tsananin shidewan datake sbd tsananin tashin hankali da kukan da hawaye basa fita a cikin dare daya da wuni hawayenta sun kafe kallan Asaman takeyi tana girgiza kai dukkanin jikinta na rawar da bata hayyaci bace. Rintse idanuwa Asamah tayi ahankali tana bude su Akan su duka tace ‘Allah zai zama gatanku, Allah zai Baku kariya, Allah zai kawo ido da haske a rayuwarku kudai ku jajirce karku rabu duk tsanani ku kasance bangon juna’ Maida kallanta tayi kan kusran ta basa amsarsa da cewa ‘Na zabi rayuwansu Akan tawa a cika mun damar da aka ban ta hanyar barinsu da rayuwansu harsai lokacin da ubangijin daya halitta musu ita zai karba da kansa… Ayanah ce tayi saurin yunqurowa da rarrafe mai sauri ga Asaman tana miqa hannu zata riqeta sbd suna tsananin buqatanta a yanzu…….. Jinin daya fesu a fuskanta da hannunta data miqa ne yawa na Asamah ya sakata sanqamewa a gurin tana dauke wuta hannunata na kakkarwa me tsanani. Wuqar da kawai aka fizge fatar wuyan tareda jijiyan Asamah kaman wucewan iska Wanda ya saka jinin bartsi sosai ta kalla a hannun Wanda yayi aikin batareda bata lokacin su ba sbd zabinta ne. Wurgar da Abaas sukai a gaban yan uwansa da gawar Asamah dake gangaro da jini, Mutuwan Zaune dukkaninsu sukai tareda dauke wuta sbd babu Wanda a jikinsu jinin bai bartsanwa ba, Abaas daya kasa matsawa yana kwance a inda suka jehosa kaman mataciyar dabba rufe idanuwansa yayi hawaye na zubowa idanuwansa yana kasa motsawa. Babu Wanda yace musu komai haka suka juya suka bar gurin shugaban cikinsu ma dago murya yace ‘Kusra bata tada Alkawari idan tayi dan haka ku tafi an cika mata burinta ko bata raye amma wannan damar itace ta cika Alkawari idan mun sake haduwa daku kun zamo namu’ Har suka bace wa gurin babu Wanda ya motsa a cikinsu Ayanah sbd babu wanda ya dawo hayyacinsa, Sakinah dake Bayan Ayanah motsawa tayi ahankali tareda qarasowa gaban gawar Asamah ta saka hannunta yana rawa sosai ta shafe idanuwanta suka rufe tana fasa kuka mai tsima zuciya itama. A lokacinne Zuhrah ta fasa kukan itama me karfin gaske tana fadawa jikin Ayanah. Nurat da bata hayyacinta miqewa tayi da sauri a zare tana bin hanyar daji kafafunta na hardewa tana qwala kiran sunan Abaansu. Ganin tana Neman nisa ne ya saka Abaas miqewa da gudu yana kamota ya rungume yana kiran sunanta da karfi da fashewa da sabon kuka. A lokacin ne Ayanah da Zuhrah suka taso suma suna riqeta tana kwacewa cikin wani irin ihu na gushewan hankali Wanda ya saka yan uwanta suna fasa sabon kuka me taba zuciya dukkaninsu suna qara riqeta sbd zaucewa takeyi. Sakinah ma kukan take fasawa itama tana rungume dukansu. Ihun Nurat ke fasawa tana fizge fizge tana yakushin kanta da karfi tana kwala kiran Abaa dajin na amsawa sosai. Qin Sakinta sukai suna sake saka karfinsu su duka suna riqeta sosai kukansu na qaruwa. Sun jima a cikin wannan sabon tashin hankalin kafin Nurat din ta zube qasa suma suka zube gabaki dayansu har lokacin basu iya Sakinta ba sbd kada ta gudu. Shiru sukai sai ajiyan zuciyar kukansu dake sauka akai akai na tsawon lokaci shima kafin suka miqe hannun Zuhrah na riqe dana Nurat din suka bar gurin. Gabas suka kalla suka sake miqa suna kutsawa hanya batareda sunsan inda suka dosa ba. Yunwa da azaba ce kawai a cike da rayuwarsu a lokacin tareda mafi girman baqin ciki da qunci, Wuni suka sake shudewa suna zagayen dajin sun rasa hanyar fita bare komawa ANJOM duk da sunsan garin ya zama na kusra yanzu. Cikin dare sosai suka sake samun wani guri suka zauna tareda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106