Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 104

Chapter 104

Hayateem Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fara bude nasa idanuwan da ganinsu ya fara ragewa ya saukesu Akan NUAB din. Wani irin Numfashi me tattare da sanyin jiki NUAB ya sake tareda daga hannun Abaas din ahankali ya Dora Akan na Amminsa dake kwance har lokacin bata farfado ba ya hada hannuwansu guri daya ya matse musu su da nasa hannuwan biyu yana sunkuyar da Kansa qasa wasu hawaye masu tsananin Zafin gaske suna ciko idanuwansa ya kasa cewa komai…. Kokarin tsayawa Numfashi da bugawan zuciyar Abaas sukeyi sbd abinda ya dirar masa zuciya ya Lumshe idanuwansa ya bude ahankali da qurawa fuskar NUAB dake sunkuye ido batareda ya juyoba yaga fuskar hannun dayake hade da nasaba sbd bazai iyaba. Aleey ne dayake Bayan NUAB din ya tako a sanyaye shima nasa idanuwan na cike da hawaye masu zafi ya Kama kan Abaas din cikin kulawa da ya juyo dashi setin fuskan Ayanaah dake gefensa Akan nata gadon daban idanuwanta a rufe fuskarta fayau asalin kamanninta babu abinda ya sauya sai manyanta datai…. Wasu hawaye ne masu tsananin dumi suka gangaro daga cikin idanuwan Abaas daya kasa kyaftawa daga kafe idanuwansa dayayi Akan fuskar Ayanah hawayensa na tsanananta gangarowa da Wani irin dumi, Bude bakinsa yakeson yi ya Ambaci sunanta amma Allah bai basa damar hakan ba dan haka hannunsa ya dan iya motsawa ahankali ya Kama hannunta cikin nasa tareda sauke ajiyan zuciya me sanyi ya rufe idanuwansa ahankali wasu hawayen suka gangarowa ahankali idanuwan na rufe. Shiru gurin ya sake dauka me tsananin gaske Wanda ya saka NUAB sauke ajiyan zuciyar daya sauka tareda wasu irin hawaye masu Zafin gaske daga idanuwansa da suka kasa riqe dukkanin jarumtarsa. Aleey ma Juyawa yayi ahankali yana saka hannunsa daya ya rufe idanuwansa dake fidda hawaye sosai har hannuwansa rawa sukeyi kaman yanda na NUAB ke wata irin rawa sbd tabbatarda Ran ABAAS GHAZ ayau yabar jikinsa ya amsa kiran ubangiji. Sakinah dake bakin kofa rawa jikinta itama ya dauka me tsananin gaske ta saka hannu da karfi ta rufe bakinta tana fasa wani irin kuka Mara sauti zuciyarta na tsananin ciwon me Zafi. BAHAR da bata fahimci meya ke faruwa ba tana tsaye daga waje idanuwanta jajir ganin irin yanda sakinah ke Wani irin kuka jikinta na jijjiga ya sakata fara takowa ahankali ta sako kai cikin dakin kafafunta na rawa. Gap da isowa ga mahaifinta data kafe da ido takeyi Aleey ya sake fasa wani irin kuka me sautin daya sakata fahimtar Abaa dinta ya bar duniya yabarta. Duhu ne ya rufe zuciya da idanuwanta ahankali Wanda ya sakata kafafunta gazawa ta yanke jiki a gurin ta zube jikin NUAB Wanda ya tarota da hannu daya har lokacin Sauran hannunsa daya yana riqe da hannun Abaas da Ayanah. Doctor shigowa sukai suka fara kashe naurorin dake manne da Abaas din bayan sun rubuta time of death nasa. Daganan ficewa sukai sukabar fmly da jimamin rashin. Kuka sosai sakinah takeyi kaman rayuwanta tazo karshe sbd wannan itace kaddarar karshe data qarasa yanke farin cikin dasuke sakaran yi a gaba, Ayau Abaas ya tafi yabar duniya kaman yanda Nurat da Ayshaah suka tafi sun barsu da tabo da gurbin da bazai taba cikewaba har abada. NUAB daukan Bahar yayi yakaita Dayan dakin da doctors zasu dubata kafin aleey ma da yasha kuka sosai ya fara shirin komawansu da gawar da bazaa rufeta a nan ba dole zasu koma dashi ghaz acan zaa rufesa. Zaman qunci da damuwa tareda zullumi me tsanani sukai kafin cikin saa suka samu jirgin dawowa da gawar wadda Washe gari tinda safe suka Juya kuma har lokacin Bahar bata farfado ba haka suka dawo da ita. Haka suka kuma doguwar tafiya kafin suka sauka kai tsaye suka sake daukan manyan motocin da suka kaisu har cikin ANJOM ghaz da gawar Abaas GHAZ Wanda a lokacinda Bahar ta farfado rungume gawar tayi ta kasa cewa komai hatta kukan ya kasa zuwar mata idanuwanta ne kadai sukai Wani irin ja. A haka babu bata lokaci akai janaizarsa aka rufesa a cikin masarautar gefen kabarin mahaifinsa da mahaifiyarsa da Ayshaah da akai a cikin masarautar duka dan haka Ana gama janaizarsa suka tattaro suka juyowa tareda Bahar wadda gabaki daya baa San ma Wani halin rayuwarta take ciki ba sbd ko kyaftawa kaman batayi komai nata ya tsaya cak tana rungume a jikin sakinah wadda take jinta har cikin jinin jikinta. Suna isa qasar inda zasubi jirgi anan NUAB ya bada umarnin Maa sakinah da Bahar a wuce BOYEM dasu shikuma zai koma ga Amminsa. Zasu wuce Bayan kowa ya fice kallan Maa sakinah NUAB yayi da manyan idanuwansa da sukai tsananin Laushi ya tattaro dukkanin nutsuwansa ya bude baki yace ‘Maa ina Neman wata alfarma da nakeson kimun alkawarinta a yanzu, Inason kimun alkawarin idan Ammi ta farfado bazaki taba fadawa mata Abaas yabar duniyaba sbd bazata iya dauka ba a yanzu da muke kokarin Neman lafiyanta, Kimun Alkwarin bazata taba sani ba Bazata zan komai ba har sai ranar dana fada mata hakan da kaina, Zuwanmu ghaz da duka abinda ya faru Inason ya zama sirrin da bazai taba fita ba sbd lafiyarta da bazata iya dauka ba, Ki riqe ‘yarsa Amanace ya bar miki amma kada Amminah tasan wace ce ita sbd sanin ita waye din zai saka dole tasan anga Abaas ankuma rasashi dan haka ita din batada kowa sai ke sbd auren da aka daura ba aure ne dazaa tinaba bare qararwa, Maa Inason kiyimin wannan alkawarin’ Numfashi mai tsananin dumi sakinah ta sauke tareda dagowa ta kalli NUAB tukuna ta Gyada kanta alaman tayi wannan Alkwarin har karshen rayuwarta matiqar ba shine ya tado zancenba ta rufesa kenan har ranta ya fita. Numfashi me nutsuwa ya sauke kafin yayi sallama da ita aka wuce dasu airport ba bata lokaci jirginsu ya daga zuwa BOYEM. Suna wucewa da awa hudu suka nasu jirgin yayi daga zuwa ga Amminsa wadda bazai taba dawowa da ita ba matiqar lafiyarta bata daidaitaba. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laoualir *_HAYATEEM_* Mamuhgee 70 A jirgi kwance jikin Maa sakinah Bahar ke kwance idanuwanta da sukai ciki ciki jajir da galabaitar rayuwa da zuciya tareda sarewa da fidda rahama ga rayuwa gabaki daya, Rungumeta cikeda wata irin kulawa da kauna me tsananin gaske da Jinta har jininta Maa sakinah tayi sbd BAHAR itace Abaas da suka rasa har abada sai kuma Aljannah idan Allah yayi sunada rabon haduwa, BAHAR itace jini daya tak ta Abaas dinsu a duniya da idan basu jita har cikin jininsu ba me zasuyi? BAHAR itace jinin Abaas da duniya Ayanah batada kamarsa, Ayanah Allah baiyi tanada rabon sake Dora idanuwanta Akan ‘dan uwanta ba rabin jikinta ba sedai tanada rabon rayuwa da ‘yarsa a matsayin matar ‘danta da bazata saniba sbd ita kanta koda NUAB bai sakata alkawarin kada ta fada mata Abaas ya tafi yabar duniya ya barta ba itama kanta bazata taba iya fada mata mutuwar Abaas ba Wanda Ayanah bazata iya dauka ba dan haka wannan Alkawari ne ta daukanwa kanta itama bazata iya fada matan ba sedai shi NUAB din duk ranar dayaga ya kamatan, BAHAR Amanarta ce a yanzu da zata riqe da

Table of Contents

Chapters

106 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});