Chapter 80
Chapter 80
lokacin da HAILE ta isa kofar toilet din mai girma da tsari zata shiga, Shigowan Aslam ya saka Hailen dakata wa cikeda mamaki mai dan girma idanuwanta Akan Aslman din sbd ganin lokacin da Aslam din ta taho Bude Baki tayi zatai magana Aslam ta rigata da cewa ‘Ya dawo, Shine ya dawo Bayan shekaru Mamee, Ya dawo Masarautar BOYEM, ‘Dan mistress din Sultan ya dawo Mamee, Ya dawo a daidai lokacinda muke kokarin ganin mun cimma burinmu kota yaya, Mamee tayaya zaki kawar da sultan daga duniya ASIM ya hau mulki a yanzu wannan yana masarautar? Tayaya zamuyi aure yanzu? Tayaya komai zai tafi yanda mukeso a yanzu da wannan din ya dawo? Tayaya sultan zai bar duni…….. Wani lafiyayyan mari HAILE ta sauke mata cikin kidima da rikicewa zuciyarta na wata irin rawa sbd gabaki daya Aslam wata irin mahaukaciyar zuciya ne da tinani da ita, matiqar zata shiga tsananin baqin ciki da bacin rai haka zata ringa tona asirin zuciyarta cikin tsananin baqin ciki da Zafin zuciya dayake fiddata hayyacinta dan hakanne ya saka haile bata barinta magana koina sbd zata iya aikata kuskuren da zaiyi karshen rayuwarsu gurin magana idan takai maqurar bacin rai, Marin da HAILE tayi mata ita kanta hayyacinta barin jikinta yakeyi da abinda Aslam din ta fada dan kuwa bazai taba yiyiwa ace NUAB ALMAZZ ya dawo Masarautar BOYEM din ba dan haka tafi yadda da sultan ne ya fita kila ya dawo batareda saninsu ba dan haka Kai tsaye toilet ta fada kafafunta na dan rawa hakama zuciyarta na tsalle. Alwalar sallar asuba zatai amma gabaki daya ta rikice hannuwanta rawa sukeyi bata Kama ruwa ba alwala tayi ta fito har lokacin kafafunta rawa sukeyi zuciyarta data kasa yadda da abinda Aslam ta fada amma sai bugawa takeyi sosai tana Jin batada Sauran nutsuwa idan zuwa tayi ta tabbatarda waye ya shigo akai wannan sanarwar. Kallan Aslam dake Zaune cikin matsanancin yanayi tayi zuru ta bude Baki tace ‘Kije kiyi sallah zan tabbatarda me yake faruwa idan na kammala komai da kaina zan tafi gurin sultan dan tabbatarda komai.’ Miqewa Aslam tayi batareda tace komai ba sbd jikinta dayake matiqar a sanyaye babu kowace irin kuzari a tattare da ita dan kuwa a duniya babu abinda zai iya kashe zuciyarta lokaci daya ta buga irin ace bazata samu cikar burinta na aure ba Wanda shine maqasudin ragewansu Akan ASIM ALMAZZ ya hau mulki, A yanzu rana tsaka idan NUAB ALMAZZ ya dawo BOYEM tabbas zasu samu babban katangar da zata iya shiga tsakaninsu da burinsu duk da bawai yadda zasuyiba zasu iya aikata komai Akan cikar burinsu ciki kuwa hadda kawar da rayukan wainda baa taba tinani ba. Ficewa Aslam tayi zuciya da gangar jiki ba nutsuwa hakama HAILE tada sallarta tayi itama zuciyarta babu sukuni. *****Motocin daya bayan daya suna zuwa can quryar harabar da iya jinin sarautar suke isa can a Jere suka fara Parkin daya bayan daya cikin tsarin da suka saba motar LEUL dince a tsakiya Kai tsaye suka fara fitowa daya bayan daya aka bude kofar da LEUL BOYEM yake Zaune ya ziro kafafunsa cikin izza waje kafin ya fito gabaki dayansa yana shakar iskar Masarautar datake jininsa, Lumshe fararen idanuwansa masu kyau da kwarjini me zafi yayi yana Jin Wani bangare na zuciyarsa yaja cikewa da gurbi me Zafin dayake ciki da wani sanyi me ratsa zuciyar sbd Ayau gashi inda mahaifiyarsa ke rayuwa yana shaqar iskar Numfashi daya da ita, Gabaki dayansu a tsaye suke qyam babu alaman gajiya ko buqatan Hutu a tattare dasu ko kadan saima karfinsu mai daga hankali dayake sake bayyana. Sarkin bayi ne cikin wata irin gaggawa ya iso gurin tareda tarin bayin da suka zube qasa gabaki dayansu kansu a qasa suna gaidasa batareda sanin yabar gurin ba Kai tsaye bai jira komai da kowaba ya doshi bangaren mahaifiyarsa shi daya tak sbd babu me hurumin shiga bangaren matan sarki idan ba ‘yayansu ba dan haka gabaki daya Yaransa suna tsaye a inda motocin su suke babu alaman sauki ko rahama ko daya a fuskarsu. Aleey ne ya sanar da sarki bayi LEUL BOYEM ya Riga ya wuce bangaren mahaifiyarsa nasa bangaren suke buqatan a kaisu dan tabbatarda tsaronsa. Babu bata lokaci Kai tsaye aka wuce dasu bangaren nasa me girma Wanda yake part guda mai tsari da kyau, Duk da baya nan babu shekarar da baa sauya furnitures da komai na bangarensa sbd haka doka da kaidar take, Komai na sauyin da ake masa ahankali ahankali yana tafiya ne da cigaban zamani da ake samu har zuwa yanzu da aka zuba duk wani luxury na rayuwa da zai basa Hutu da nutsuwa isasu, Komai a tsare yake da duk abinda zai saka yaji kaman yana gidansa na Moscow kawai dai yar qura ce sosai itama a take Sarkin bayi ya fara bada umarnin a fara gyara. Dakatar dashi Aleey yayi cikin nutsuwa da buqatar full control na kulawa da komai daya danganci lamarin LEUL komai qanqantarsa, Babu abinda babu a Masarautar BOYEM na Jin dadi da biyan buqata dan haka take Aleey ya bada umarnin a fara sauya komai dake bangaren a cikin kankanin lokaci dan haka ba bata lokacin Sarkin bayi ya saka a fara fidda Kayan a fara shigo da wasu da suka fisu komai. ******Sultan YASAR a daidai lokacin da sautin qarar dawowan magajin dayayi shekaru yana jiran wannan ranar ta dawowansa a wannan lokacin wayar sa ne da wishmah ayanah ghaz wadda a tare sautin ya shiga kunnuwansu ya isa ga zuciyarsa yana sanyayar da wani gurbi me girma da yayi shekaru a zuciyarsa, Ahankali sautin yake sake ratsashi ya rufe idanuwansa masu kyau da kwarjini yana jan wani Numfashi me dumi ya saukesa a hankali tareda bude idanuwansa Akan fuskar Ayanah dake bayyane kan screen dinsa shiru ta zuba masa ido a sanyaye bata iya cewa komai. A natse cikin sanyin nutsuwa ya sauke ajiyan zuciya datake dauke da shirin zartarwa da shirin fuskarta abubuwa da dama a masarautar da wainda suke cikin masarautar dan kuwa wannan ranar yake jira Wanda NUAB ALMAZZ zai kawo kansa masarautar da kansa amma kuma fitarsa da kansa ya rasa kenan saida umarnin sa dan kuwa shine yake riqe da cokalin juya rayuwarsa yanda yaso har sai ya cika masa burinsa daya dauka akansa tin daga ranar daya diro duniya, Burinsa daya saka ya banzatar da abinda yakeso fiyeda komai da rayuwarsa. Kallan Ayanah yayi a natse ya Lumshe ido akanta ya sake budesu akanta kafin ya bude Baki cikin mulkin dayake yawo jininsa shima da sautin daya shigeta yace ‘HAYATEEM dinki Zaki me BOYEM ya dawo gareki a matsayin cikakken namijin da BOYEM ke buqata’ Motsa idanuwanta tayi akansa tana Jin maganar tasa ta sauka cikin hankali da tinaninta harma da gangar jikinta dan haka ta motsa tana tashi Zaune da kyau duk da bata karfi ko kadan sbd rashin lafiyan datake cinta, Juya kanta tayi ahankali zuwa kofar ficewa bedroom din nata datake ciki daidai nan sultan ya kashe wayar yana jinginar da bayansa ga lafiyayyar kujeran dayake Zaune ta bedroom dinsa tareda dake rufe idanuwansa ahankali zuciyarsa na yin dum tareda shiga tinanika da dama. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106