Chapter 3
Chapter 3
tsananin tsini. Na farko ganin ya kusa fita bishiyoyin zuwa filin dajin dayake hango hanyar da yasan zai iya samun gurin tsira da sauri ya sake tsananta gudu kafafunsa na fidda wani irin Jini na fashewan kafafunsa da tarin qayar da suke cike da tafi harma da saman kafarsa. Na bayansa kasawa ya fara yi sbd zuciyarsa dake kasa dauka fara rage gudu yayi kafafunsa na jinin dayafi na gabansa hancinsa ma jini ne yake fita dan haka hannunsa ya daga ahankali ya Zare jakar fatar jikinsa Qarama ta kudin da suke tare dasu ya daga zai jefawa dan uwansa ya bude baki daqyar zai Ambaci sunansa wani irin jini me karfi ya feso ta kirjinsa,. Cak ya tsaya hannuwansa na dawo wa qasa ahankali idanuwansa na yin jajir kaman zasu fidda hawayen jini sbd tsananin azabar dasuke bayyanarwa, Ahankali ya saukar da Kansa zuwa kirjinsa ya kalli tsinin mashin daya shigo ta bayansa ya bullo ta kirjinsa. Sarewa kafafunsa sukai cikin tsananin azabar da bata da Kama a lokacin. Kafin ya qarasa kaiwa qasa wani mashin ya sake ratsa wuyansa ya bullo ta gaba take wani jinin me yawan gaske ya feso ta bakinsa da wuyan yake ya zube a gurin ba rai a jikinsa. Suna isowa gurin Sauran basu tsaya ba tsananta gudu sukai dan cimma daya sbd a tarihin kusra basa rasa duk Wanda suke bi. Mutum biyu ne suka tsaya Akansa ba wata wata suka fidda wata kakkaifar wuqar da ko ice zaa yanka da ita bazaiyi Kyan gani ba take suka fara huda kirjinsa dan cika umarnin shugabansu. Jemo daya waiwayo yaga dan uwansa rayuwarsa ta riga ta fita take yaji zuciyarsa da jikinsa na sarewa wani irin Ihun kuka ya fasa yana cigaba da gudun da yasan ba tsira zaiyiba Kuka yake yi sosai sbd dan uwansa jininsa dashi kadai yake dashi a duniya baisan yaya zai yi rayuwa babu dan uwansa Juyowa ya sakeyi koina na jikinsa na wata irin rawa gudunsa na tsananta Juyowansa da shigar mashi a goshinsa lokaci dayan hakan ta faru take ya tsaya cak yana zubewa gefe ahankali jini ya gangarowa zuwa idanuwansa take ransa shima ya fita a gurin. Cikin rashin imanin fa basuda shi suka qaraso suna durqusawa gabansa Sauran kuma hanyar da suke hange suka zubawa ido wadda ganyen Shuke shuke suka rufe amma sunada tabbacin indai akwai shuke shuke a gurin to tabbas akwai mutane kokuma gari sbd shuke shuke ne da qaramin gari sosai bazai iya ba sai garin daya tara mutane da dama hakama kuma indai har akwai gari a cikin gurin to tabbas irin hakan suke so garin dayake a boye Wanda har zasu Kai hari su gama su tafi baa sani ba. Mutum hudu ne a cikinsu suka tinkari hanyar zuwa shuke shuken da suke hankowa daga nesa sosai suna dake zubawa hanyar ido sosai daga nesa suna kasa yadda da akwai gari a cikin wannan Jejin me tsananin hadari. Tafiya suke suna sake Sauri sbd wannan abune na farin cikinsu, Cak suka ga na gabansu ya tsaya tareda kallan qasansa da sauri sakamakon abinda yaji sai kuwa ga maciji baqi qirin yana wani irin qyalli cikin rana. Wuqar hannunsa ya saka ya fizgo macijin da ita ya rabasa biyu ya jefar suna cigaba da tafiya cikin zalamar son kaiwa inda suke son, Taku goma suka qara dafin macijin ya fara aiki a jikinsa duk da ya yanka gurin daya cijesa da wuqa dafin ya biyo jini yana fita. Wani irin zufa da zafi jikinsa ya fara dauka take bugun zuciyarsa ya fara sauyawa ya tsaya cak tareda durqusawa ya sake yanka fatar jikinsa da wuqa yana turo jini waje da hannunsa. Daga bayansa wani macijin yaji ya kuma sararsa take ya juyo yana kokarin Kai masa hannu ya kashe wani ma ya sake sararsa take ya fara kokarin mine wa amma ba damar hakan sbd sankarewa da jijiyoyin jikinsa suka fara suna Dena aika jini koina. Ganin hakan Sauran yan uwan nasa basu tsayaba suka cigaba da tafiya sedai ko ina basu kaiba dukkaninsu suka zube a gurin kowannesu kumfar tsananin dafi na fita jikinsu na dafin macizai. Sauran na ganin hakan suka fahimci me yake faruwa a gurin Wanda hakan ya gama basu tabbacin da suke nema na cewan akwai gari a karshen dajin. Jiya wa sukai suka koma Bayan sunyi doguwar tafiya me tsayi kafin suka bullo bakin gabar mahaukatan ruwan. Suna isowa suka sanar da Sarkinsu gabaki daya bayanin komai. Shiru yayi idanuwansa a rufe wani irin rashin Imani da bushewan zuciya na ratsashi batareda yace komaiba. Shiru na mintina a hakan kafin ya bude jajayen idanuwansa da basuda haske ko Kadan ya sauke Akan zuciyar da suka kawo masa tana jini ya dauka batareda ta juyaba ya jefawa mahaukacin karensa me tsananin girma da munin kallo tareda tsoron kalla Wanda yaci ya ginu da cin zuciyoyin mutane ko wani idanuwansu. Gashashen maman Dabbar ruwa da aka kawo masa ya miqa hannunsa ya fara ci batareda ya wanke ko goge hannu ba. Yaransa ya sake dagowa ya kalla wainda adadin yawansu baisan iyaka ba dan tsananin yawansu ya bude baki muryansa me tsananin kauri da rashin dadin saurara yace ‘Idan gari ne a dajin nan kaman nisansa daga yanzu ya zama na kusra, Dukkanin me rai tin daga kan dan Adam har dabbar datake da rai sun zama a cikin lissafin kusra, Wannan Karan bayin na musamman ne sbd lokacin da kusra zata gina Masarautarta da qasa me sunan kusra yayi dan kuwa bayin da masarautar BOYEM take buqata daga gareni zasu fito dan kuwa acan ne kadai zan Kai bayi na mallaki cikar Burina da aka haifan dashi, Babban burin iyaye da kakanni na Akan kusra takai matakin mallakar qasar kanta da mulkin kanta Akan siyar da bayi shine kai Bayi a BOYEM, Buri ne da kakana bai cika ba,babana bai cika ba dan haka nine zan cika wannan burin kota halin yaya, Bayin BOYEM na musamman ne sbd farashin d ake zubewa a siya Wanda yake sauya rayuwan duk me siyar da bayi, A guri daya BOYEM ke siyan bayinta bata taba sauyawa ba sbd tsaro da izzarsu dan hakan ne kusra basu taba samun wannan babbar damar ba duk kuwa qwarewansu a harkar bayi a tarihi dan hakanne duk wani kusra dayake duniya yasan burinsu da macimmarsu daya ne wato shiga BOYEM Kai bayi Wanda daga ranar da BOYEM ta siya bayi daga gurinsu sun samu yancin kafa daularsu yawo ya qare musu sedai azo daularsu a siya bayi koda zasu Kai sama da bayi rai dubu dari. Hadiye Naman bakinsa yayi yana sake bawa Kansa tabbacin wannan garin shine garin nasararsa sbd zai dauki bayi daga garin harya haura qasar baa saniba sbd a boye suke labarin harin da suka kaiwa garin bazai fita ba bare ya samu tangardar tafiya duk da baa taba kamasu ba amma bibiyan da ake musu idan ya kaiwa gari hari ya kwashe mutane yana basa Tangardar mutuwa bayinsa sosai sbd basa tsaya wa duk tsananin rashin Kyan ruwa haka suke tafiya a cikinsu batareda sun tsaya kowace qasa ba dan hakanne bayin da sukayo safara suke mutuwa sosai sbd rashin sabo amma a yanzu idan baa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106