Chapter 101
Chapter 101
fara yi sbd kusan duk bayin biyar an kashesu hakama suma anfara musu rauni dan haka boukar da jini sosai yake fita jikinsa kallan Abaas yayi cikin tsananin galabaitar daya fara yace ‘Ka tafi Ka dauki ayshahh da jaka na nan gefen gadonta na ajiye ku bar nan kuje garin neruji ku tsallaka ruwa zuwa kiyoje ku jirani anan,Ka tafi da sauri…. Kasan Juyawa Abaas din yayi yana kallan boukar din tamkar yanda Abaa dinsu yayi musu hakan ce yake sake faruwa Ayau din dan haka zaiyi musu boukar damqi hannunsa da karfi yace ‘Idan ban taho ba zuwa gobe to bana duniya Ka dauki Ayshaah Ka tafi da ita inda zata samu rayuwa me kyau ita amana ce gareka duniya da lahira, Hakama idan ranar goben ta fadi ban bayyana gareku ba na ‘yantaka Nurat, Ka zama gatan ‘yata ka zama gatanta da dukiyarta’ Cikin tsananin baqin ciki da radadin zuciya a Karan farko Abaas ya bude bakinsa Bayan shekaru ya furta ‘ABAAS GHAZ’ Kallansa boukar yayi da Wani irin yanayin karyewan zuciya batareda yaddarsa akansa ta girgiza ba ya bude baki idanuwansa na yin jajir yace ‘Abaas ghaz ina fatar Ka zamo gatan ‘yata da bata kariya da rayuwarka har karshen rayuwarta ko taka’ Tura Abaas din yayi da karfi zuwa cikin gida shikuma yana sake bude kofar fita daga bangarensu zuwa bangaren da hatsin zuwa da kuma zuwa kofar ficewa da tini suka shigo. Da sauri Abaas ya juya yana jin zuciyarsa na yanka da Wani irin yanayin da yake sakasa jin kaman bazai iya tafiya yabar boukar ba amma kuma matiqar zasu bawa ayshahh kariya su tseratar da rayuwarta dole ya tafi. #MAMUH HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070 Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali [09/12, 11:19 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_* Mamuhgee 67 Kai tsaye dakinta ya isa da gudun gaske ya banka kofar bai tsaya komaiba ya dauki jakar da boukar yace ya miqa hannu ya damqi hannunta datake tsaye ta miqe cikin tsananin tsoro da fargaba. Janta yayi da karfi suka fito tsakar gidan Wanda yake hayaqi da ci da wuta take ta riqe hannunsa da karfi cikin tsananin tsoro da tashin hankali tace ‘Meya ke faruwa, Ina Abbu?? Baice mata komaiba ya jata da saurin suka bi ta kofar baya da babu Wanda ya sani sai iya su zasu fice ta qwace hannunta zata koma da gudu tana kwala kiran sunan mahaifinta. Riqota Abaas din yayi da karfin gaske yana kokarin sake tafiya da ita ta fara fizgewa tana Ihun daya sakasa rufe mata baki da karfi yana kallanta cikin duhun hanyar ya sanar da ita abinda yake faruwa da kuma abinda mahaifinta ya ce akan zuwansu su jirasa. Kasa iya barin mahaifinta tayi ta fara Wani irin kuka da rawar jiki tana kokarin kwacewa sbd tasan mahaifinta bazai tsiraba kashesa zasuyi batada kowa bazata iya rayuwa ba mahaifinta ba,bazata iya shiga duniyar da tasan bazata taba sake dawowa ba anan ko kabarin mahaifinta ta ziyarta ba dan haka gwara ta mutu a guri daya da mahaifinta. Rufe mata baki gabaki daya Abaas yayi zuciyarsa na jin abinda take ji sbd shima ya shiga irin wannan mummunan yanayin harma nasa ya zarce nata nesa ba kusa ba dan haka daukanta yayi cak yabar gurin da ita yana sake rufe mata baki da duka karfinsa. Gudu yakeyi da ita a cikin tsananin duhu da shukokin da sun kusa finsu tsayi dan haka cikinsu kawai yake jefa Kafafunsa da ko takarmi babu yanaji qayoyi manya da qananu suna sukarsa da abubuwa masu laifin da harma sun fasa kafafunsa jini suke fiddawa amma bai tsayaba gudun yakeyi sosai sbd yana jiyo hayaniyar biyosu da akai Wanda hakan ya tabbatar musu su duka biyun da boukar ya fadi. Kuka Ayshaah takeyi sosai dukkinanin jikinta na sakewa a jikinsa tanajin duniyarta ta gama kifewa da lalacewa kenan har abada dan haka bazata taba dawowa daidaiba. Shi Kansa jin yakeyi jikinsa na Neman mutuwa da wannan mummunan baqin cikin na rasa Wanda yakeda mahimmanci a rayuwarsa datake a rube Bayan rasa iyaye da yan uwansa amma ganin a yanzu shine gatan ayshahh da kuma zai samu yancin zuwa Neman yan uwansa da sune kadai rayuwarsa ya saka yake sake tattaro karfinsa yana cigaba da Wani irin gudun da kafafunsa ke fidda jini sosai amma bai tsayaba dan basu tsira ba. Gudu sukeyi har kusan asuba hakama karfinsa ya kare daqyar yake iya daga kafa sbd galabaita da jininsa daya fara qasa da kuma wata irin azababbiyar ciwon kirji amma hakanan yake dagewa yana daga kafa. Koda suka isa wani garin dayake daga shi sai inda boukar din tace suje anan suka samu suka tsare wa wainda suka biyosu amma duk da hakan bai tsayaba dauketa kawai yayi ya Kama hannunta tamkar wadda bata gani haka ya ringa Janta ba karfi a jikinta ko kadan. Tafiya me tsayi suka kuma yi kafin suka isa garin dayake bakin ruwan da zasu tsallaka Anan dinma basu tsaya ba cikin wata gona suka boye yayi sallah a galabaice kafin suka fada jirgi suka bar nahiyar kwata kwata. Tafiyar wuni guda sukai kafin suka isa inda zasu din suka fito jirgin tareda barin bodar bakin ruwan wadda sai anan ne Abaas ya gane garin da aka siyosa ne dan haka ya sake riqe hannunta gam suna kutsa mutane suna shiga cikin garin sosai Wanda yake a cike tamkar kasuwa koina hidima akeyi. Wani qaramin gidan baqi da yan gudun hijira ya isa dasu suka zauna Bayan ya tsaya a hanya ya siya mata gasashiyar fulawa da zuma. Suna Zaunawa ta cusa kanta cikin kafafunta tareda qanqame jikinta tana fasa wani irin kuka mai tsima zuciya koina na jikinta na jijjiga da tsananin quncin da batasan haka radadi da zafinsa yake ba. Shiru Abaas yayi a gefenta idanuwansa jajir yana Kurawa ruwan dake mamaye da bakin bodar ido zuciyarsa na yanka shima sbd anan ne aka rabasa da tasa rayuwar, Anan ne ya rabu da wainda suke rayuwarsa, Anan ne komai na rayuwarsa ya qarasa Juyawa harzuwa matakin dayake yau akai na rayuwa da bulayi cikin duniya shi kadai babu kowa acikinta. Radadin azaba me tsanani kafafunsa keyi Wanda ya ke sakar masa da zazzabi me Zafi amma bai damuba shiru yayi ido jajir Akan ruwan. Kuka tayi Wanda saida ya qarasa cinye karfinta kafin tayi shiru tana Kurawa hanyar ido itama batareda ta iya cin abinda ya bata dinba. A gurin suka kwana Zaune cikin mummunan halin daya tsananta yanayinsa dama nata datake wata rawar sanyi dan haka ya cire rigar jikinsa ya rufa mata Akan nata Kayan da babu ko kallabi a kanta gashinta a bude yake a sake sbd yanayin da suka fito. Koda gari ya waye daqyar sukai sallah a gurin suka tashi Zaune suna sake gadin hanyar da duk masu isowa, Duk yanda yayi da ita taci Wani abin qi tayi gashi tayi Laushi sosai ta fita hayyacinta kawai mahaifinta take son ganin ya taho din. Haka suka wuni har rana ta Kuma faduwa babu boukar ba labarinsa, Zuwa lokacin dagashi har ita daqyar suke Numfashi dan haka Akan dole sukaci abinci sbd suna Neman karfin cigaba da jiransa har ranar daya taho.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106