Chapter 96
Chapter 96
ta bude ba tare data tambayi waye ba,anwar dinne yana tsaye qofar dakin sanye da rigar da wando na shadda blue ruwan sararin samaniya,fuskarsa sam babu walwala,hannunsa goye a qirji ya zubawa qofar ido,wanda tana bude qofar idanunshi suka sauka a kanta,rabon daya sanyata a idanunsa tun ranar dinner din nafisa data matsanta mishi sai yazo,sanda ya shirya zai fita tana falon qasa tana kallo,abinda kusan ba dabi'arta bace,zai mata magana bata tsaya saurarenshi ba ta tattare wayoyinta da kayanta ta haura saman ko waiwayoshi batayi ba,sai yaji sam baiji dadi ba,tunda ba dabi'arta bane zaman falo mai yiwuwa yau tayi sha'awa ne gashi ya bata mata yanayi,koda yaje a gurguje ya dawo,amma saiya tadda ta garqame kanta,tun ranar rabonshi da ganinta sai yau. Bata ankara ba har ya iso gabanta,saiki tayi ta riqe dukka hannayenta cikin lallausan tafin hannunshi,runtse ido tayi tana son zamewa amma ya riqe gam,saita soma qoqarin ganin ta qwace din,gaba daya ya janyota sai gata cikin jikinsa,saura kadan numfashinta ya dauke,ta dinga qoqarin zuqoshi hadi da shaqar qamshin daddadan turarenshi "Babu dadi ko?,kiyi haquri" ya gaya mata muryasa qasa qasa,tsigar jikinta ta zuba sosai,saita soma kokawar cire jikinta tana tureshi da dukka hannayenta "Ina ruwana?,meya dameni?,ka sakeni don Allah bana son irin haka" "Ko baki taba sona ba shahida dole kiji haushi,dole kiji kishi,nasan halin mata fa" yayi maganar yana sakinta daga jikin nashi,saiyadan jaa baya kadan "Kije qasa kina da baqi" daga haka ya juya ya nufi dakinsa,yayin data gyara daurin dankwalinta sannan ta sauka zuwa qasan. Mubina ce khadija da huda sai sa'ida da qanwarta ,fuskarta a sake ta karbesu,nan suka sake sosai abinsu cikin gidan,sa'ida ta gaya mata anty usaina na gaidata,can gidan anty usainan dole ta hada wuni saboda 'yan katsina da sukazo duk da basu da yawa,amma wannan karon harda inna kakar anwar,wanda ta manta rabonta da kano,shi yasa wannan karon anwar din ya matsa sai tazo,tunda ta fuskanci shahidan bata da ra'ayi hada wani taro sai ita ta hada a gidanta,saidai sa'idan ta gaya mata anjima zasuzo karban amarya. Kaman babu abinda yake damunta haka suka dinga sabgoginsu da yaran,anwar din yana daga sama,wani lokaci ya leqo yayita kallonsu bata sani ba,wani lokaci kuma yana daga daki yakejin motsinsu,shi ya aika akaje aka dauko yaran yasa aka kawo mata,yasan koba komai zasu hanata zaman dakin daya tsira,ta kuwa ji dadin zuwan nasu,duk wata damuwa da take jinta liqe da ranta sai takejin ta ragu. Ko data gama abinci iya ita da yaran suka zauna sukaci,bayan sun gama tasa suka kwashe suka kai mata kitchen zata wanke,tana tsaye a kitchen din ta soma dauraye kwanukan ya shigo,ta waiwaya ta dubeshi ta dubeshi sai kuma ta dauke kai tana ci gaba da wanke wankenta "Ni ban taba ganin ango irin wannan ba,ba abokai ba komai,ka dawo gida ka samu waje ka zauna?" Take tadin ita da zuciyarta,wanda harya iso bayanta dab da ita bata sani ba,kallonta yake hakanan qirarta da shape dinta yake daukan hankalinsa fiye da qima,saiya dinga tuna baya can da bai taba ganin komai nata ba,saboda a sannan ma'abociyar sanya hijabi ce,a lokacin da yake cike da buri da fatan Allah ya bashi kudin da zai aureta ya mallaketa a matsayin matarsa,yanzu gata a matsayin matarsa,amma wani abu ya ma rayuwarsu karan tsaye,saiya kauda wannan tunanin yace "Ni ba za'a bani abincin ba?" Gocewa tayi gefe jin maganarsa dab da ita,da alama tsaye yake kenan a bayanta "Ban dafa dakai ba" ta amsa masa tana ci gaba da wanke farantan ba tare data juyo ta dubeshi ba,shuru yayi yana dubanta,bata taba hanashi abinci ba sai yau,sai baice komai ba ya matsa gefe kusa da inda tukwane suke,ya dauki daya ya dauraye ya ya tari ruwa a fanfon dake kusa da ita,ya hada kayan qamshi ya dora ruwan shayi,ya jingina da jikin kwabar kitchen din yana kallon ruwan yana jiran ya tafasa,duk abinda yake tana kallonshi ta gefen ido,ta rugashi gamawa don haka ta fita tabar masa kitchen din,suna falon yazo ya wucesu da ruwan shayin,harya soma hawa saman saiya waiwayo yana dubanta,hankalin yaran duka nakan arewa24 yace "Banfa ji haushi ba,wanda ma aka dinga bani a baya Allah ya amfana ko?" Ya qarashe maganar yana daga mata gira,kauda kai tayi yadda ta saba kaman bata ganshi ba,yayin dashi kuma yaci gaba da hawa saman. Da yammaci suka sake gyare gidan tsaf suka cikashi da qamshi tako ina,har turarukan da bata taba amfani dasu ba sai ranar,kama daga na labule carfet da wanda kebin iska,sun gama kenan sai gashi ya sauko cikin shadda brown sabuwar qarr,kyau uya kyau yayishi,sai taga kamar wannan shigar ta musammance,duk da dama shidin koda yaushe cikin saka sabbin sutura yake,hakanan taji wani abu ya tokareta sanda suka hada ido ya dage mata gira guda,saita aje pillow din hannunta ba tare data bari ya iso inda suke ba ta shige kitchen,tana jinshi da yaran suna uncle kayi kyau,ya gama dan hirarsu dasu ya fice daga gidan bayan ya dauki daya daga cikin motocinsa.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96