Chapter 59
Chapter 59
saiyaji a jikinsa da zuciyarsa yadda ya janyo mata bacin rai tsakar rana ba tare data shiryawa hakan ba. ***** ****** ****** ***** Tunda ta tashi washegarin take kwance abinta kamar ruwa taqi yin komai,saidai daga nan ta koma can,hasina tayi tayi ta tashi tayi wani abun ko taji qwarin jikinta amma ta qeqashe qasa,ko kallo bata ishi daada ba sangar gabanta kawai take,tana daga kwancen tana kallon daada,yadda ta cika fridge dinta da fura da nono mai kyau,lemuka da kuma ruwa,tasa hasina tayi total na kayan fulawa aka siyo komai hasina tayi dan dai dai aka adana komai,baki ta tabe ta dauke kai bacin rai na cinta sanda daada ta fito da sabuwar daddumarta da kawu ummaru ya bata sanda ya dawo daga umara ya fesheta da turare ta baiwa hasina taje ta shimfida a dakin soro. Saida komai ya kammala hasina ta isketa kwance cikin kujera tana saqa da warwara ta zauna gefanta "Ya kamata ki tashi ko ruwa ko watsa kyaji dadin jikinki?" Idanunta da suka sake girma saboda kwana biyu data yi bata saka musu kwalli ba ta watsawa hasina cikin salon tambaya "Me kikeson cewa?,kice kawai na tashi na yi masa kwalliya saboda zaizo,mutuncina ya qara zuba a idanunsa ko?" Murmushi hasina ta saki tana kada kai "Niba haka nake nufi ba,kawai nasan yadda kikeson wanka wuni guda kuma ace tun safe ga azahar ta shiga baki watsa ruwa ba bare kici wani abun ai babu dadi,a qalla kodon tsaftar jikinki ko?" Saita maida kanta ta kwantar gami da rufe ido sannan ta amsa mata "Share kawai" dubanta hasinan tayi na wasu mintunan sannan ta miqe tana cewa "Allah ya kyauta,ya kamata dai ki sawa ranki salama,tunda kinsan cewa aikin gama ya gama,kada madai azo gaba kina jin kunya yazo kiga ya miki ki kamu da sonshi,kinsan wallahi daada ba raga miki zatayi ba"da sauri ta sake bude idon ta dubi hasina "So,bakisan nayi bikin binneshi ba?" Dariya ta qwacewa hasina ta kama baki tana kallonta "Shi kuma wannan da kika kawo fa?,mutunci kuke kenan?" "Nuradden?..inason in rama halaccin da yayi minne shekaru kusan hudu" "Tabdi,kice gwara da Allah yasa daada ta zaba miki miji,ashema ba soyayya kuke ba kenan" kofin dake gefanta shahida ta wafto ta jefi hasina dashi Allah yasa ta kauce bai sameta ba,har ga Allah taso ta sametan don bata da bakinma ce mata ta fita saboda wani abu dake takore da wuyanta "Na rantse da Allah na tashi hasina saidai daada ta fiddaki daga gidan nan" cikin dariya ta fice tana cewa "A'ah,a'ah,bani nakar zomon ba,ratayarma kuma ba'a bani ba". Qarfe uku na rana da 'yan mintina daada ta shigo ta sameta "Tashi kiyi wanka ko yanzu nasa akaimin ke bandaki na sabeki" ta furta tana nuna da gaske take,saida ta gama taurin kanta ganin da gaske daadan take sannan ta shiga bandaki tayi wankan. Sanda ta fito mai kawai ta shafa sai turarenta oily data gogawa fatarta,tasaka wasu riga da skert na atamfa ta zura dogon hijabinta daya sauka har saman qafafunta ta soma da nafila kafin ta gabatar da farillar sallar la'asar. sanda ta kammala saman abun sallar ta zauna tana jan hasbunallahu wani'imal wakil,saboda faduwar da gabanta yaketa yi wanda batasan dalili ba. 👑 https://youtu.be/H7M7h6l6wNM *xafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don girman Allah karki sharing,ga mai buqatar siya zai tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 3️⃣0️⃣ "Kana nufin kaine mutumin daya kawo sadakina da mudin airena ba tare da sani ko yardata ba?" Ta furta wani bala'i na cinta,maimakon ya bata amsa da baki saiya daga mata dukka girarsa biyun yana dubanta kai tsaye ya kafeta da idanunshi,wani tashin hankali taji ya rufto mata irin wanda bata taba jin irinsa ba tunda maganar aurenta ta bullo,tashin hankali da ba'a saka masa rana,ko zata yarda da kowa ba zata yarda da anwar ba,ko zata amince da auren kowa ba zata taba amincewa da auren anwar ba koda su biyu kadai suka rage a duniyar,murmushin takaici ta saki wanda qasan zuciyarta ji take kaman zata fashe "Kaima kasan ka dauko abinda bazai taba yiwuwa ba har abada,tamkar wanda ya mutu ya dawo ne,kai bakaji kunya ba anwar?,kana tunanin akwai abinda yayi saura?,kana tsammani akwai wani sauran abinda ya rage tsakanina dakai?,to bari kaji na gaya maka,ba zaka taba samun yardata ba,ba zaka sake samun soyayyata ba,har abada aure tsakanina dakai,har abada...." Qawataccen murmushi ya saki,da alamun kwanciyar hankali kwance kan fuskarshi,sai daya sauke qafarsa ya sauya jinginar da daya sannan ya rungume hannunsa daya dayan kuma yana shafar sajensa idanunshi a kanta,fara'ar fuskarshi ta bace bata "Hajiya shahida....dukka tunaninki bai baki dai dai ba,baije inda ya kamata yaje ba" sauke qafarsa yayi ya soma takowa inda take tsaye,sai daya rage tazarar dake tsakaninsu sosai sannan ya tsaya ya soke hannayensa cikin aljihun rigarsa "Kina tunani ko tsammanin soyayya ce tasa na nemi aurenki?,ko kina tunanin neman yardarki nake kafin na aureki?"sai ya sake takowa gab da ita kamar zai hadeta da jikinsa,ya nunata da yatsa "Zan aureki don na nunawa wancan wawan cewa nidin na girmi qaramin dalili babban dalili ne ni,sannan nayi isar da zan yanke guntuwar soyayyar da yake taqama da ita,soyayyar da bai iyata ba,bai gama saninta bama bare ya iya,baisan kanta ba baisan mece ita ba!" Ya qarasa fada yana dan daga muryarsa gami da nuna qofa da yatsa kai kace nuradden ne ke tsaye a wajen,saiya sauke hannun nashi yana maidashi aljihunsa kana yaja baya kadan har yanzu bai dauke idonsa daga kanta ba "Yana tunanin ya sanki?,yana tunanin yafi kowa saninki koya riga kowa saninki?,ya gayamin magana yayi tunanin yaci bulus?,inaso yaji ciwo ya kuma ci gaba da jin ciwo a ransa duk sa'a daya da zata wuce da tunanin wani mai suna anwar ya haramta masa auren wadda yake iqirarin yanaso,wadda yake iqirarin ba wanda ya isa ya shiga tsakaninsu" yana kaiwa nan ya juya mata baya,yana jin kamar ana yankar zuciyarsa "Baki cancanci na qyaleki kici gashin kanki ba,baki cancanci na barki kiyi zabin da kikaga dama ba,bayan kin cutar da zuciyar da bata cancanci sakamakon da kika bata ba,kin bata rayuwar da alokacin ya kamata ki tattaleta kodon iyaye da qannenki,kin bada jikinki ga wani har yayi ajiya a wajen daba muhallin......" Saiya kasa qarasawa saboda wani dunqulallen abu daya tokare masa maqoshi,ya dinga jin wani turari tun daga zuciyarsa zuwa fuskarsa,bakinsa yaji ya dauki zafi ya fitar da iska zazzafa,yana jin wani irin ciwo da qunci duk lokacin daya tuna da lokacin da kuma abinda ya faru,hotunan dake wajensa da ganin da yayi kaya ido da ido sun kasa gogewa daga qwaqwalwa da zuciyarsa,yana jin wani irin ciwo mara misaltuwa,tabbas da yana da iko daya dawo da lokacin ya goge duk wani abu daya faru ko xai samawa zuciyarsa salama. Tuni hawaye ya soma wanke mata fuska tana tuna lokacin da abinda ya faru alokacin daya bayan daya,sai a sannan ta dinga tuna kaman ta ganshi,kaman a gabanshi aka sauketa,hakan na nufin ya ganta cikin maye?,ya ganta a lokacin da jini kebin qafafunta?,yaga sanda aka cillo mata pant dinta da kwalabenta?,amma me yasa ya zama mai qaramin tsinkaye?,mai yasa ya zama mai gajeran nazari?,me yasa ya yanke mata wannan danyen hukunci farat
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96