Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 69

Chapter 69

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,293 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ratsashi,ita ta soma janye idanunta,ranta a hade tsaf ta taka zuwa ciki tana duban faruq,saiya miqe,anwar yace "Zan nemeka kafin na wuce kada kayi nisa" "To yaya" ya fada yana ficewa,sai da taga fitarsa sannan ta zauna hannun kujerar dake a dab da bakin qofar fita,tanason tsareshi da ido donta karanci me ya kawoshi amma batasan me yasa takejin rashin qwarin gwiwa ba,ta maida idanunta kan tafin hannunta tana murzawa ba tare data ce masa uffan ba,hakan ya bashi damar kafeta da ido,ya soma kallonta tun daga yatsan qafarta zuwa saman kanta,yana jin wasu tagwayen abubuwa na fada cikin zuciyarsa,daya nason yaqar daya gami da rinjayarsa,inda daga qarshe dayan yayi galaba,saiya runtse idanunsa yabar kallonta saboda wani bacin rai dakeson shaqeshi,kullum kwanan duniya yana son sasautawa kanshi,yana son ya daina ganin baqinta da baqin abinda ta aikata,yana son abinda idanunsa suka gane masa da hotunan daya gani su bace daga idanunsa ko zai samu salama da rangwame amma hakan ya faskara,sai komai yayi kaman zai goge saiya sake dawowa sabo fil a ransa. Walwalar da yake jin kaman zata samu a ruhinsa ta dusashe,sauran faragar fuskarsa ta bace bat. Zaman kurame ne yaci gaba da wanzuwa tsakaninsu harna tsahon wasu mintuna,sai daya gama zamanshi don kanshi sannan ya miqe,cikin wani taku ya isa dab da ita ya tsaya akanta,kana ya ranqwafa gefanta har tana iya jiyo qamshin ya aje envalope din hannunshi,ba tare daya dago ba yace mata "Baki iya gaisuwa ba saikace a gidan mashaya inda kowa yake ogan kanshi,karki tsammaci xaki gidana da wannan dabi'ar ki tsira,ga saqon da muhsin ya kawo miki daxu kika maidashi nina dawo dashi,idan kin isa karkiyi amfani dashi yadda ya dace kiga yadda zata kaya mana nidake,tunda na fahimci cikin halayen da kika koyo kala daban daban harda taurin kai ko?,good....inason wannan sabon halin naki,idan kin tashi gayyatarki karki sake ki kwaso min tarkacen 'yan maye,ko tarkacen qazaman tsaffin samarinki" daga haka ya dago yana shirin wucewa zuciyarta taje iya wuya,ta kasa daurewa "Idan ba haka bafa?,me zakayi?" Ta fada a tsiwace cikin fushi da fusata,saiya sake dawowa gabanta ya tsaya,ya dubeta na wasu mintuna sannan ya saki murmushi "Ki aikata din sai kiga sakamakon" miqewa tsaye tana masa kallon tara saura kwata sannan tace dashi cikin salo na masifa dake cin zuciyarta "Baka isa ka sakani abinda banyi niyya ba,baka isa komai ba idan ma kana tunin ka isa" murmushi ya sake saki wannan karon mai sauti,yadan buga qafarsa sannan yace "Ko a haka aka tsaya ai inga irin tawa isar ko?,hukuncin da zan miki ba isata kawai zai nuna miki ba,izzar aure da izzar anwar namiji" "Namiji shine zai tsaya takara da abokan adawarshi ya kuma samu nasara,ba wanda zai wafta koya biyo ta bayan gida ba,koya taka wani tsani don kaiwa wannan bigiren,ka daina batawa kanka lokaci wajen kiran kanka da namiji,ba namiji bane kai saidai mata maza" idanunsa ya qura mata qir sanda take maganar cikin dakiya da rashin nuna tsoro,hakanan bilhaqqi da gaske,ganin takai aya saiya soma takowa inda take tsaye,ta tsaya cak don ganin iya gudun ruwanshi,saidai harya iso gab da ita bai daina takowa ba,hakan na nufin zai hade gap din dake tsakaninsu kenan,don haka ta soma ja baya ga zatonta zai tsaya amma ina,bai barta ba sai daya tabbatar ya hada bayanta da bango,qafarshi dake saye da takalmi saman tata qafar wanda yana iya jin zafi zafi na tudun takalminsa daya take mata qafa,kusancin dake tsakaninsu yayi yawa,tana iya ganin fuskarsa tarwai wadda kyau ya cikata gamida iya gyara,idanunsa sai suke juye mata irin na anwar dinta na wancan lokacin sak,janye qwayar idanunta tayi gabanta na bugawa da sauri da sauri,tsoro da fargabar me zaiyi mata na shigarta,saitaga ya daga hannu kaman yana shirin marinta,ta runtse idonta da sauri tana wassafa me zata masa ita bayan ya gama marin nata,ji tayi yaja baya da sauri cikin kaushi yace "Sai na saki kinyi nadamar lafazinki,tsautsayi kuma yasa bakiyi yadda nace miki ba" daga haka ya juya da sauri sauri ya fice daga dakin,cikin hanzari ta daga murya "Idan ka isa ka tsaya mana ka dakenin kaga yadda akeyinta" gab da zai fice ya waiwayo yace "Aiba a gidan syrup muke ba" kalmar ta tsaya tana fassarawa,take wani abu ya cushe mata maqoshi,cikin qanqanin lokaci hawaye ya ballewa idanunta,tana jin zafi a zuciyarta duk sanda yayi wani lafazi dazai iya tuna mata da abinda ta aikata a baya,sulalewa tayi ta zauna a wajen,ba shakka ba'a bari a kwashe duka,shaye shaye ashe wani tabone da tambarinsa bai barin jikin maishi?,koda kowa ya manta ba'a rasa burbushi,ta jima a wajen tana jin ciwo kala kala kafin ta miqe ta fice daga dakin,ko kallo envalope din basu isheta ba bare ta dauka. A falo anty zubaida tace ta tsaya ta duba dinkunanta na biki wanda ita batasan ankai bama,don ko kayan har yau bata kalla ba bare ta gane me takeso a ciki har tayi tunanin kaiwa dinki?,bata cikin yanayin da zata iya zama cikinsu saboda haka tabawa anty zubaidan uzurin kanta na ciwo zata duba zuwa safiya da haka ta wuce dakinta. Washegari sun fito da anty zubaida zata koma gidan gyaran jiki tanata kumbure kumburenta da mita cikin ranta na yadda aka takura mata ba gaira babu dalili faruq dake sharar dakin da uncle hisham ya sakashi sabida zaiyi baqi ya fito da envalope din yana miqawa anty zubaida "Anty wannan a dakin na gansu,kaman na anty shahida ne don jiya na gansu a hannun uncle anwar" hanu tasa ta karba sannan ta waiwaya tana duban shahidan "Me yasa kika barsu a dakin?,abinda kikayi dai dai kenan?" Saita langabe kai,ita abun goma da ashirin,komai tayi batayi dai dai ba,saita saka hannu kawai ta amsa suka wuce,suna shiga mota ta kasa daurewa ta saki kuka tana kife fuskarta saman cinyarta,anty zubaida batace komai ba saidai ta dora hannunta saman bayan shahidan,saida tayi kukan na wani lokaci sannan anty zubaida tace mata.......*Alqawarin Allah* 3️⃣4️⃣ "Abubuwa da yawa da mukeso muke qwallafa rai a garesu ba alkhairi bane ga bawa,kiyi qoqarin rage wannan kaifin qiyayyar kamar yadda annabi yayi umarni saboda kada ta juye miki zuwa soyayya mai zafi daga baya,kiyita addu'a Allah yasa abinda zai faru dake ya zama shine mafi akhairi a rayuwarki duniyarki da lahirarki" da ire iren wannan nasihar suka isa wajen gyaran jikin. Anty zubaidan ita ta karbi envalope din ta bude taga abunda ke ciki,saita amsa ta aje tana jiran hasina tazo ta raba cikin 'yan uwa,don shahidan a yanzu bata da wata qawa banda zunnurah da take sokoto,tunda abun ya faru gaba daya ta cure qawa daga tsarin rayuwarta,saidai gaisuwa kawai ta mutunci,sabida card din bashi da wani yawa sosai,da alama dinner ce da akayi selecting iya adadin mutanen da zasu shiga. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Gaba daya ta susuce cikin kwanakin ta fita hayyacinta,idan ka ganta saika dauka ba ita bace ba,gashi daga mummy har abban nata ba wanda ya sake bi ta kanta koya tanka mata dangane da hukuncin data yanke na ba zata auri anwar ba bare ta fadi abunda yake ranta ko zataji dadi,kullum kwanan duniya kamar ibada kuwa saita kira number mima sau babu adadi amma tana a kashe amsar kenan kullu yaumin,ko fita yanzu ba kasafai take ba,kishin anwar da

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});