Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,300 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sannu sannu saboda yadda takejin jikinta sam.babu qwari,gagara yin sallar tayi a tsaye saboda yadda takejin qafafunta kamar lagwani tilas ta zauna ta yita a zaune. Tana gamawa ta miqe don hankalinta yayi gida kuma,don bata taba tsayawa a waje har wannan lokacin ba bata koma gidan ba "Ki tsaya kici abinci saiki sake samun qarfin jikinki" "A'ah fiddausi gwara na wuce gidan,ba wanda yasan inda naje" "Shikenan....bari na baki wannan duk sanda kike cikin bacin rai kina sha zaki baccinki ki manta da kowa" sam a cikin ranta batajin zata sake sha,saboda bata taba bacci irin haka ba,bugu da qari ita babu wani raguwar bacin rai data ji,don kada ta gwasaleta kawai ta amsa "Maganin damuwa ne,zaki samu relief,kin ganni nan,ko bacci ne yaqi daukata saboda wani bacin rai dana sha zanyi baccina hankali kwance" kai kawa i ta gyada,fiddausi ta rakota har qofar gida ta wuce ita kuma ta koma cikin saurin don ta labartawa mima komai da yadda abubuwa suka gudaba,sannan ra fara da turo mata kudin data alqawarta mata,don syrup dinta dama ya qare tana buqatar siyan wasu ta aje. Tsakar gidan nasu babu wadatar hasje sosai kasancewar babu wutar nepa,bata nemi kowa ba don bacin rai ke sake taso mata na yadda tabar gidan nasu dazu,uwa uba kuma wani sabon baccin take ji,gqba daya jikibta jibsa take kaman an tsoma lagwani a ruwa. Kan katifarra ta fada rub da ciki tana lumshe idanu tanajin yadda gabobinta sukayi rauni,idanun nata na arufe taji wayarta na ruri,sam baki daya ta mance da ita,ta miqe cikin kasala ta daukota daga saman akwatin kayanta,anwar ne yake kira,take ta dannan ta kara a kunneta "Ina kika shiga haka shahida?,nazo gida ana nemanki sama da qasa ba'a ganki ba?,na kira wayarki ya kusa sau hamsin ba'a daga ba" sai data lumshe ido sannan tace "Babu inda naje fa,ina gidansu fiddausi,wayar kuma na manta ta ne cikin akwatin kayana,koka kira babu lallai aji sautinta" ajiyar zuciya ya sauke yana jin tashun hankalin da yaji dazu na sauka "Karki sake irin wannan fitar,hankalin umma ya tashi sosai" "In sha Allahu" ta fada amma cikin zuciyarta tana fadin koma meye sune suka ja "Ya naji muryarki haka?,lafiya kike?" Saidata gyara kwanciyarta saboda baccin dake fisgarta tace "Lafiya qalau....kawai...bacci ne yakeson saceni" "Bacci yau kuma?" Ya tambaya cikin mamaki,sabida yasan a qalla suna kaiwa sha daya suna waya,a hakama shike datsewa yace tayi bacci,sam bata iya baccin wuri ba "Wallahi" ta fada a gajarce,saiya raya a ransa jiki da jinine kawai don haka yace "Alright,asuba ta gari to,tunda yau anmin ruwa gani da jin muryarki" murmushi ta saki a kasalance tace masa na gode ta datse wayar ta cillar gefe tana maida kanta saman filo hadi da sake lumshe idanunta. Mubina ce ta dago labulen dakin ta shigo "Yaya kizo inji umma...ashe kin dawo tun dazu ake nemanki" juyar da kanta tayi daya side din cikin muryar jin bacci tace "Saida safe...kice mata nayi bacci" yau ba 'yan maganar bane akan mubinan don haka ta fita ta shaidawa umman tasu saqon shahida,sai gata ra taso da kanta "Ke shahida....ina kika je tun dazu?" "Gidansu fiddausi" ta bata amsa ba tare data juyo fuskarta inda umman tata ke tsaye ba "Tashi ki dauko abincinki a kitchen kici" "Ba qoshi" ta sake fada cikin muryar bacci,sam umman tata bata lura da sauyin dake tattare da ita ba,ga tunaninta fushi tayi kaman yadda ra saba a duk sanda wani abu ya gilma tsakaninta da mahaifinta,saboda haka ta tabe baki "Indai ba zaki sawa ranki haquru da kauda da kai ba zakita ganin bacin rai,kije ki hadu da hawan jini a banza,babanku baida haquri kuma baida adalci,ni kuwa bazan tsaya ya tauyen haqqina ba atoh" tana gama fada ta juya ta fice,sama sama take jin abinda umman ke cewa,ga mamakin kanta da kanta,maimakon ta sake jin haushi yadda ta saba sai taji sam maganganun basu d'a d'ata da qasa ba,baccinta ya fiye mata komai,idanu ta sake rintsewa ba jimawa kuwa wani nannuyan bacci ya kwasheta. Kwana biyu tsakani suka ci gaba daga inda suka tsaya,a lokacin tana daki zaune tana turawa anwar tex,tun tana daure zuciyarta harta kasa,ta toshe kunneta duk a banza,takai ta kawo cikin dakin ita kadai saita fita,haquri ta soma basu tana kuka kowa idanunshi ya rufe ba wanda ya saurareta bare yayi shuru ya ragawa dan uwanshi,dare yaui ba damar ta fice daga gidan ta huta,sai kawai maganin da fiddausi ta bata ya fado mata ta juya da sauri ta koma dakin ta rufo qofar don sautin tartsatsin fadan ya ragu,ta duba saman madubinta yana aje ta dauka ta bide ta shanye gaba daya,ta koma gefan gadon ta zauna tana kuja gamida addu'ar Allah yasa yayi mata aiki,Allah yasa baccin yazo da wuri ya dauketa kota huta dajin meke faruwa cikin gidan. Cikin mintina qalilan bacci ya soma zuwa mata,kafin kace ta sheme a wajen,ba ita ta farka ba sao washegari da safe bayan gari yayi tarwai rana ta take,da hanzari ta miqe tana tariyo abinda ya farun,sosai taji dadi har ranta da Allah baisa taji qarshen masifar ba,don haka batasan ya aka qarke ba,ta bude sakatar dakinta ta fita tsakar gidan nasu,a share yaje fes saidai gidan nasu yayi tsit alamun ba kowa ko duka yaran basa nan,tasan da hakan don lokacin tafiya makaranta yayi,saita tari ruwa ta shiga bandaki,wanka tayi don tafijin qwarin jikinta sannan ta hado da alwala ta fito ta shiga dakinta ta sauya kaya ta tada sallar asuba da bata samu tayi ba,bayan ta kammala ta wuce dakin ummanta,ta sameta a zaune a falonta tana tsintar shinkafa,ta dago suka hafa idanu,kallo daya zaka mata kasan ranta a masifar bace yake,wanda tasan hakan bai rasa nasaba da kace nacen da sukayi jiya da babanta,gaidata tayi ta amsa sama sama "Wato don wulaqanci da iskanci da asuba kina ji ana bugun qofarki ki tashi kiyi sallar asuba kikaqi ko?" Ita sam batasan anyi hakan ba,batasanma yaushe aka buga qofar tata ba,amma kawai sai tace "Kiyi haquri umma,bacci ne yaci qarfina" "Oho ke kika sani,naga alama kin fara goyawa mahaifinki baya,to wallahi kikace haka zakiyi wahala zakisha" ko kadan ranta bai baci ba sai tace "Kiyi haquri" banza tayi da ita,sai bayan mintina wajen goma sha biyar sannan tace da ita "Saikije ki dauki abun karyawarki a kitcheni,idan kin gama ki kunnan wuta na dora shinkafar nan" "Toh" ta fada tana miqewa zuwa madafa. Tana cin abincin tana tunanin abinda ya farun jiya,gaskiya baqaramin rage mata radadi maganin yayi ba,ko banza batasan qarshen abun ba,hakanan bata ji wani bacin rai ba,saita yanke kawai yau ta sake zuwa gidansu fiddausi ta gaya mata inda ake saida abun ta siya,duk sanda suka soma balahirarsu tasha ta samu bacci ta qyalesu. To tun daga lokacin shahida ta shiga ruwa tsundum,batasan illa da giraman abinda takeyi ba,batasan yadda take rushe rayuwarta ba,kawai ita ta bada amanna ne tana shan maganin matsalarta,batasan tana sake qarawa rayuwarta matsala bane,tana tunanin maganin bacci kawai takesha,batasan ta fada shaye shaye bane tsundum,wanda ba wanda ya kula da sauyawarta banda anwar,lokaci zuwa lokaci idan yazo fira wajenta da zarar sun fara zata soma gyangyadi,haka zai mata sallama ya tafi,ya nazarceta sosai baiga wani abu daya sauya dangane da ita dinba bayaga yawan

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});