Chapter 27
Chapter 27
waje yaci karo da mutum uku cikin maqotansa "Yauwa malam nuraini...dama yanzu muke neman yaron da zai mana sallama dakai" qoqarin dai daita fuskarshi yayi ya basu hannu suka gaisa "Ashe haka abu ya faru?,wallahi sam bamuji dadi ba,yarinyar da kowa ke mata kallon hankali da nutsuwa" daya daga cikin maqotan nashi da ake kira da malam sallau ya fada "Wallahi kuwa malam sallau,amma nidai ina kyautata zaton sharrin qawaye ne tunda kowa ya shaidi nutsuwar yarinyar....amma cire ciki aiba qaramin abu bane,sanda haruna ke gayan qaryatashi nayi saida yatabbatar min da kunnensa yaji saurayin yana fada" a hautsine abban shahida ya dago yana musu wani bahagon kallo,kusan bai fahimci me suke fada ba gaba daya "Yata shahida ce tayi ciki harta cire?" Sai suka koma kallon kallo tsakaninsu,malam sallau ya dubi abban "Errrhmmm malam nuraini kodai mata sun maka irin halin nasu ne an boye maka bakasa me yake faruwa cikin gidanka ba?,banda haka wannan zancan ai ya karade unguwarnan daga daren jiya zuwa safiyar yau" "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ya dinga maimaitawa yana dafe da kanshi,me yayi jama'ar unguwarsu haka sa cikin qanqanin lokaci zasu jefi diyar cikinsa da wannan sharrin,kansa ya dafe da yaji ya soma juya mishi sai kawai ya juya zuwa cikin gida "Allah ya tsare gaba ya kiyaye" ya juyo malam sallau yana fada cikin daga murya,dai dai sanda shahida data fito don shiga bayi ta kama ruwa ta saki butar hannunta cikin tsananin tashin hankali ta koma dakinta,dukka jikinta rawa yake,tana tariyar kalaman da saurayin ya dinga fada bayan ya saketa a qofar gidan,kenan duk abinda ya fada sun yarda dashi?,kenan yanzu kallon da kowa zai dinga mata?,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha"shine abinda ta dinga maimaitawa kenan. Cikin kwana biyu kacal ta rame ta fige ta fita a hayyacinta,bata taba tunanin akwai tashin hankalin daya wuce na fadan iyayenta ba saiga wanda ya ninkashi ya risketa,duk ta silar kaucewa wancan bacin ran ashe zata fada wanda yafi wancan tsanani rusa farinciki dama ruguza rayuwa gaba daya. Ba ita kadaiba gidanma gaba daya ya zama shuru,baya ga abinda ya faru abbanta ya kwanta ciwo sosai tun randa su sallau sukazo masa jaje,wanda ba komai bane ya taba ranshi irin maganar da suka furta,qarshe da aka aunashi jininsa ne yayi mugun hawa,hakan ya saga hankalin ummanta itama ta shiga wani sabon tashin hankalin da firgici. Kwana uku amma shahidar jinta take akwai ya babu,gata nan dai kawai amma komai ya fice mata aka,ranar kwana na ukun da yammaci wani yaro yayi sallama tsakar gidan nasu dauke da takarda wanda yace gashi a baiwa shahidan. Mubina ce ta bita har cikin daki a sannan tana kwance saman abun sallah ta miqa mata,saita saka hannu kawai ta amsa ta aje saman kanta tana ci gaba da lazuminta,wanda kusa fiye da rabi istigfari take da salatin annabi. Sai data idar sannan ta dauko envalope din,tana daga kwance ta farketa,takarda ce qwaya daya a cikinta ta fado,sai wata azurfarta guda biyu data siya ta baiwa anwar ajiya,da sauri tasoma warware takardar tana zumudin jin daga gareshi,don tunda abun ya faru taji dif daga bangarensa,tana zaton wala'alla yazo ance mishi bata da lafiya,don bata da maraba da mai lalurar,ita kuma wani kunya da nauyin kiranshi take,gani take kaman daga muryarta zai karanci komai,zai karanci halin data fada,wasiqace cikin rubutun anwar din mai tsari _Basai nayi miki sallama ba don baki cancanceta ba,saqo nake son isar miki dama ba wani mai tsaho ko yawa ba,shahida,sam baki dace dani ba,kuma sam bakiyi dai dai da rayuwata ba,tuntuni ina zaune dake ne kawai don bani da abinyi kuma bani da wata qwaqwaqwarar sana'a,gashi ina da buqatar macen da zan di ga rage dare a wajenta,to zuwa yanzu al'amura son suma yimin kyau,bana jin zan iya ci gaba da zama dake,ki sani ni muhammad anwar ban taba sonki ko qaunarki ba,na miki alfarma ne kawai a baya,kuma ki saka a ranki cewa baki taba soyayya da wani mai kama dani ko suna na bar har qarshen rayuwarki,wasiqar na tafe da guzurin sabuwar masoyiyita wadda nake da tabbacin ta fiki komai,idan nace komai ina nufin komai da komai da kikasan diya mace na mallaka_ Cikin rawar jiki ta miqe zaune dungurgur,sannan ta jawo envalope din ta sake lalubawa ciki,saiga hotuna guda shida rigis sun fado,dukkaninsu anwar ne cikin hotunan da wata matashiyar budurwa cikin kyakkyawar shiga ta alfarma,kana musu kallon farko zaka tabbatarwa kanka lallai masoya ne da sukayi zurfin cikin qaunar juna,saboda yadda kowanne ke kallon danuwanshi cikin fara'a da shauqi,sosai ta tsurawa fuskar yarinyar ido zuciyarta na wani qara gudu tamkar zata faso qirjinta,suya zuciyar tata take mata tanason yin kuka amma bataji koda alamarsa ba bare yazo,nazarin fuskar yarinyar take take ta tuno inda ta santa,ranar bikin umaima,ranar bikin umma zaune gaban motar daya amso don ya kaita ya daukota,saita saki hoton tana girgiza kai tare da laluben wayarta duka lokaci daya,tamkar tababba take zancan a fili ita kadai "Nasan wasa kake min ya anwar ba zamu taba rabuwa....nasan wani ya kaima labarin abinda ya faru dani,ranka ya baci ka furta min wannan kalaman saboda kishina da kake" maganar tata ta katse sanda wayar ta shiga ta soma ringing. Wata murya daban ta dauka,cikin matuqar sauri da zaquwa tace "Don girman Allah ka taimakeni ka bawa anwar" dan jimmm yayi cikin tunani,don a yanzun bayajin anwar din zai iya wata dogon magana,tunda Allah yasa suka miqashi asibiti yayi kwanaki biyunsa cur ya farfado yace a dawo dashi gida yazo ya dauke wata envalope dashi kansa muhsin baisan meye a ciki ba ya adana yake zaune waje daya,kana kallon yanayin fuskarsa kasan ya dulmiya cikin wani qunci,iein quncin dake kama zukata ya riqe tamau ya dinga yankarta a hankali yana saka rudani damuwa da baqinciki mai yawa a rayuwa,irin baqincikin dake tasiri kadan kadan daga ruhi zuwa gangar jiki ya illata mutum ta farat daya ba tare da an ankara ba. Miqa masa wayar yayi,sai daya daga idanunsa da suke nuna alamun gajiyawa da damuwa ya dubi muhsin sannan ya maida kan wayar,hannu ya saka a hankali ya masa,muhsin ya sakar masa yana tashi gami da cewa "Bari naje gida na dauko wayata na barta a chargy" kai kawai ya iya gyada masa yana kara wayar a kunnensa. Abu na farko da tayi kuka ta sakar masa,wanda yake bayyana rauninta qarara,gajiyawa da rashin samun madafa,idanunsa ya runtse yana jin zuciyarsa cikin wani inji ana hautsinata sama da qasa ko zata faso qirjinsa ta fito. *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wannan number* 07067124863 *ko kuma* 09032345899https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki nemi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 1️⃣5️⃣ Tamkar ana hautsinashi shi kanshi,wani irin abu ya dinga ji mai kama da tsana qyamata da haushi cike fal a zuciyarsa,wannan runtse idanun da yayi ba abinda ke gilmawa cikin idanunsa sai hotunan daya gani kwanaki hudu baya da suka shude "Dama akwai wani wani lokaci da zaizo da zaka daina sona ka juyamin baya ya anwar?" Shuru yayi ba tare daya ce komai ba,duk sanda yayi yunqurin cewa wani abu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96