Chapter 91
Chapter 91
sauri "Rabu dani na mata duka,baki da kunya nafisa ko kadan?,a gabanmu kice kin fasa aurensa,sannan ki dawo a gaban namu dai kice ya aureki?,wace iriyar yarinya ce ke?" Cikin kuka sosai nafisan tace "Kuskure ne mummy yanzu kuma na gane kuskuren da nayi,wallahi idan babu anwar rayuwata ba zata taba dai daita ba,mummy ku tayani bashi baki" "Ce miki akayi baida zuciya da zaki gujeshi yanzu ki dawo masa saboda rashin ta ido?,kema kinsan bazai taba yiwuwa ba" mummy ta amsa mata tana jifanta da harara,so take kawai ta samu dama ta daki bakin nafisan ya fashe ko zata samu sassauci takaicin dake cikata "Na amince zan aureta" anwar ya furta,lafazin daya girgizasu dukka su ukun,basu taba zata ba sam ko a mafarki,sunyi tsammanin bazai taba yarda ba,cikin hikima yake karantar yanayin fuskar alhj abba da munny bilkisu,ko basu fada masa ba ya gama karantar yanayin da zukatansu suka shiga,alhj abba da mummyn suna da daraja a idanunshi,ya sani cewa tsantsar kara kawaici da alkunya ne dasu,amma da qauna kowa ya sani suna matuqar qaunar nafisa,me yasa shi bazai iya musu kara ba ya auri diyar su wanda yasan shine cikon muradinsu,ba shakka da nafisan diyar wani ce da ya barta kenan har abada,amma ko a lahirama wani yana cin albarkacin wani bare nan gidan duniya. "Bazaiyiwu ba anwar,ka tashi kawai kayi tafiyarka" cewar alhj abba,don harga Allah bayason su xama sila na yiwa anwar din dole,wani tashin hankali ya saukowa nafisan,ya ga qoshi ga kuma kwanan yunwa tana shirin yi?,me yasa abban nata zaiyi mata haka?,girgixa kai anwar yayi cikin qarfin hali "A'ah abba,ba za'ayi haka ba,nafisa qanwa take a gurina idan da kara da kawaici,abinda ya wuce ya riga daya wuce tunda ta gane kuskurenta,Allah ya yafe mana gaba daya ya kuma kiyaye gaba" murna farinciki kaman ta taka rawa a gabansu,saidai yanzu ba lokacin hakan bane,sake kwantar dakai tayi sosai ta sake neman afuwa gamida nuna tsantsar nadamarta,itakam hajiya bilkisu miqewa tayi ta fice tabar falon,tana jin ciwo cikin zuciyarta sosai duk lokacin da nafisan ke roqar soyayya,ta rasa wacce irin diya Allah ya bata?,zataso ace nafisan ta auri wanda shi yake mutuwar sonta ba ita take mutuwar sonshi ba,ta rasa meye matsalarta meye damuwarta?,ba kalar saurayin da bata dashi wanda kowa neman yardarta kan ya aureta yake amma sam ita ta qwallafa rayuwarta kan anwar,eh anwar ya isa mutumin da za'aso a zama mata a gareshi,amma duka hakan a ganin mummyn xaifi kyau idan har shine yazo da kanshi ya nemi hakan. Tunaninsa ne ya dinga kasuwa kashi kashi,abinda ya faru yanxu cikin gidan alhj abban,tabbas shi shaidane kan irin son da nafisan ke masa wanda sautari hakan yakan bashi mamaki qwarai,karbar aurenta da yayi yasani shi kadaine abunda zaiwa alhj abba ya saka masa dimbin alkhairin da yayi masa da kyautatawa a rayuwa,da yadda yake kallonshi tamkar danshi,saidai ko daya zuciyarsa babu nutsuwa ko jin dadin karbar da yayi,bayajin wani daidaito ko daya kan batun nafisan,duk da agefe guda ya sani yana da buqatar kulawar mace,amma,ta yaya wata zata sanyo kai cikin rayuwar gidan alhali ga yadda take?,ta yaya zai kawo gyara?,tuninsa ya sake tafiya kan hotunan dake aje har yanzu suna yankawa gami da qona zuciyarsa duk daqiqa ko sa'a daya da zata shude,duk lokacin da idanunsa suka kai kai,yaha shahidan tsirara tare da wani sai yaji kaman mai shirin haukacewa,duk sanda ya kallo hoton yaga shahidan rungume qirjin daya daga cikin masu saida kayan maye sai yaji dama makaho ne shi,Allah ne kadai da qarfin addu'a suka sashi ya rayu har yakai bigiren da yake kai a yanzu. Sassanyar ajiyar zuciya ya saki sanda yake kashe motar shi,ya daga hannunsa ya kira maigadin,cikin girmamawa ya qaraso "Baqi indai ba 'yan uwa bane na jiki duk wanda yazo kace musa bama nan"ya qarashe maganar cikin muryar dake nuna jiki da zuciyarsa duka babu qwari "To ranka ya dade" ya wuce ya koma bakin qofa yayin da shi kuma ya fito,ya dinga takawa a hankali zuwa cikin falon. Shuru yake kaman koda yaushe,saidai ya hangi abinci a shirye saman dining,hakanan yayi sha'awar xama a falon,idonsa kan wata tasha da suke nuno fasahar zamani da qere qere,suna wani shirin kan na'ura mai qwaqwalwa,tsohon mintuna idanunsa nakan allon talabijin din,wani bayani da baqon nasu yakeyi ya dauki hankalinsa matuqa,yadda ci gaban xamani yazo da sauye sauye,yadda za'a qirqiri abu a idanunka kaga haka yake,amma da za'a sanyashi a na'ura sai kaga abun ba haka yake ba,tsahon minti ashirin yana bayanin wanda yayi matuqar daukan hankalinsa. A hankali tunaninsa ya karkata ga abunda zuciyarsa keson tuna masa tun daxun,saiya miqe da hanzari ya soma haurawa saman cikin sassarfa,bai tsaya ko inaba sai bakin safe din nashi,cikin sauri ya tsugunna,ya soma saka lambobin sirrin ya budeshi,envalope din ya ciro kaman ko yaushe ya zazzage hotunan ciki duka suka fado "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya furta kaman yadda ya saba sanda yake binsu da kallo daya bayan daya,duk sanda zai gansu yakanji kaman duniyarshi sama ta kona qasa ne,kullum yanajin kamar ranar ya soma ganinsu,saiya zauna sosai zuciyarsa na fata da kuma burin samun mafita,xuciyarsa ta cika da fatan dama ace ba haka bane,dama ace ba ita bace,dama ace ba shahida bace a jiki shine bai ganin dai dai duk sanda zai kalla,saiya sake gyara zamanshi sosai,ta ina zai fara?,bashi da wani qarfin sani ta wannan fannin,idan kuma yi masa za'ayi duk duniya bayajin akwao wani mahaluki da zai iya bari yaga hotunan,koda mahaifiyarshi data haifeshi ce inda tana raye. Sake miqewa yayi da sauri saboda tunawa da yayi da makarantar computer da sa'ida ta mishi xancan ummi ta musu register xasu fara zuwa,idan bai manta ba ta gaya mishi akwai online classes da special classes da za'azo har gida a koya maka,system yayi nufin kunnawa,sai yaga kamar ba zata masa sauri ba,ya ciro wayarshi daga aljihunsa ya kunna data sannan ha fada google ya soma rubuta sunan makarantar,bai manta sunanta ba saboda kusan ma'abocin siyayya ne a shagonsu na yanar gizo wato www.rahamalls.com,bakin gado ya koma sannan ya rubuta sunan makarantar *RAHA COMPUTER INSTITUTE* ,cikin qaramin lokaci ya samu dukkan bayanai,kuma tsarin ya gamsar dashi,ya dauki number dake cikin bayanan ya kira. Cikin sanin daraja da mutuntaka tadan adam ya sake samun bayanan da yake buqata,cikin abinda bai gaza awa guda ba yayi register dasu da komai da komai,ajiyar zuciya ya sauke sanda komai ya kammala,ya duba agogo yaga lokacin daya kwashe,ya miqe a hankali yana fidda kayan jikinsa,ya sauya wasu marasa nauyi,wando iya gwiwa sai jallabiyya daya fitar ganin lokacin sallah ya kusa,ya shiga bandaki ya daura alwala,sanda ya fito wayarshi na ruri,gab da zai isa gareta ta katse,saiya duba mai kiran,nafisa ce,miscal na shida kenan daga sanda ta fara kiransa zuwa yanzu,sai a sannan ma zancan ya dawo masa,ya duba saqon data tura masa wanda na godiya ne da kuma ya yaje gida,aje wayar yayi ya isa inda magungunansa suke ya cira yasha,sannan ya fesa turare ya qarasa bakin gado ya dauki jallabiyyarsa ya saka,hakanan yakejin kaman wani nauyi ya ragu daga zuciyarsa. Cikin mamaki ta dubi table din sanda ta fito daga dakinta,taji kaman ya shigo amma bataga alamun hakan ba,kaman zata share sai kuma taba hakan bai dace ba,kodon jikinsa takega ya kamata ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96