Chapter 24
Chapter 24
jin baccin,hakan ya sanya yayi tunanin ko shawara ce da ita?,baiyi qasa a gwiwa ba ya amso mata magungunan gargajiya harda na sanyi,ta amsa dai kawai ta jibge taci gaba da sha'aninta. Zuwa sannan sam abinda ke faruwa tsakanin mamanta da bbanta ya daina damunta,wani lokaci takan iya shigowa gidan ma ta taddasu sunayi tayi wucewarta daki ta kwanta abinta tahau baccinta,dukkan wadan nan sauye sauyen basu ganshi ba,ga ummanta kawai tayi mata shaidar ta koyi nunqufurci tana goyon bayan babanta,yayin da abban nata yake ganin hankali tayi ta daina damuwa da al'amarin dake faruwa. Ta bangaren fiddausi kuwa da akayi amfani da ita don cusa shahida cikin wannan harkar nasara ce a wajenta,don duk yadda aka tsara abun ya tafi dai dai,hakan yayi sanadiyyar samun kudade mai yawa daga wajen nafisa,plan dinsu na gaba shine cusa samari masu kudi 'yan duniya rayuwar shahidan,saidai duk yadda sukaso ga ganin hakan ya yiwu abun bai kasance ba,saboda sam shahidan tun asali a jininta yake,bata da kule kule,haka suka qaraci shirya plan din nasu suka gaji,hakan ya sanya suka sauya dabara,suka sake sabon shiri sabon taku da sabon tsari,wanda suke fatan shine mataki na qarshe da zai tarwatsa mu'amalar dake tsakanin anwar da shahida komai qarfinta. *_SHARRI KAYAN KWALBA_* Kusan a yanzu babu wata qawa kuma aminiya da shahida ke da ita data wuce fiddausi,kusan koda wanne lokaci suna tare,hudubar farko data soma yiwa shahida shine anwar ba son shahidan yake ba,yasha fada cewa mai zaiyi da yarinyar da iyayenta suka kasance tamkar karnuka saboda fada,sosai xancan ya daki shahida,saidai iya saninta anwar baisan badaqalar dake faruwa a gidansu ba,don tuni ta yanke yin zance dashi a gidansu bama gidansu kawai ba unguwar baki d'aya,yanzu kacokam gidan anty amina take tafiya su hadu a can,saidai kuma akace yau da gobe tafi qarfin wasa,sai maganar ta dinga tsayewa shahidan aranta,duk da cewa ko daya bata yarda ba bata gasgata ba,hakanan ba abinda ya ragu game da son anwar daga zuciyarta,duk sanda taso yin wani dogon nazari kan maganar fiddausi na kadar da hankalinta ta bata wani abun mayen sai zancan yasha ruwa. Ta gefan anwar gaba daya hankalinsa ya ta'allaqa ne kan nemawa shahida gurbin karatu cikin daya daga cikin makarantun gaba da secondry dake jahar kano tunda aka yi musu qarin albashi,bai gaya mata ba saboda yana sonne yayi mata ba zata,yaci wahala ya kashe kudi kafin komai ya kammala. Ana ya gobe zai shaida mata yana gurinta,ranar sun jima tare suna hira,sunyi hirar da suka jima basuyi irinta ba,kowanne yan jaddadawa d'an uwanshi yadda yake jinsa cikin jikinsa da zuciyarsa,sun tsokani juna sunyi raha wasa da dariya sosai,har anwar ta saka ranakun cikin daya daga cikin kundin ranakun farincikinsa da bazai taba mantawa dasu ba,ta bashi hotunan data dauka musamman sabodashi wanda ba qaramin kyau tayi cikin hotunan ba,kyanta ya fita muraran,ya qurawa hotunan idanu yaga kada kai "Wannan hotunan bazan iya maidasu enlargment ba" dubansa tayi tana narke ido tana dubanshi "Saboda banyi kyau ba ko?" Dariya ya saki yana cewa "Dama akwai wani lokaci da zaki qiyin kyau a idanuna koda wankan kashi kikayi?" Dariya sosai ya bata har shima ya tayata darawa "Dama ana wankan kashi ya anwar?" Girarsa ya dage "Eh waikoda ace anayi din...kyan da kikayi ne shahida yayi yawa,ina kishin mai aikin budawarma ya ganki" baki ta bude tana dubanshi "Ya anwar" "Shahida....kaman har yau kina kokwanton yadda nake sonki da kishinki ko?" Kai ta girgiza tana dariya "Xaki fahimta,sai ranar da aka kawoki dakina a matsayin matata" kunya ta sata sadda kai tana qiyasta ranar a ranta,gata ita dashi a matsayin miji da mata. Daya tashi tafiya saita miqo masa dari biyar bayan wata baqar leda,wadda daya bude links ne da agogo guda biyu masu matuqar kyau irin wanda tasan yana masifar so,kallonta yayi itama shi take kallo "Kada kacemin komai,na fuskanci yau miskini kake baka dako sisi(ta furta cikin sigar zolaya)"murmushi ya saki,gaskiya ta fada,don duka albashinsa ma na wajen wata uku ya qare ne wajen sama mata admission,dan abinda yaje riqewa bamai yawa bane,kudi ya dinga badawa don ta samu gurbin karatun,don yasan cikar burinta kenan shida ita,hakan bai dameshi ba ko kadan,yana jin zaiwa shahidan fiye da hakanma indai ita dince " har saika fada?"ta katse masa tunaninsa "Ina iya karantar zuciyarka ba tare daka furta abinda ke cikinta ba" ta fada cikin sanyi da taushi,sun riga da sun zama daya,sai ya saka hannu ya amsa yana murmushi "Na gode matata" kalmar data yi mata dadi sosai,cikin farinciki walwala da qaunar juna suka rabu,yana tafe yana tariyar dukka kalamanta,saiyakejin kyautar data masa tayau din daban take,hakan ya sanya ya kasa fasa kudin ya hau mota,ya taka har zuwa gida da qafa yana juya ledar data bashi gift din a ciki,gift din data bashine da sunan tayashi murnar xagayowar ranar haihuwarsa,wanda sam shi ya mance ma da yaune ranar haihuwarsa. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe biyar na yammaci da 'yan mintuna ta sauke wayar daga kunneta tana sakin ajiyar zuciya,itakam har cikin zuciyarta sam batajin zuwa ko ina,haka kawai taji batason fita.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani DON GIRMAN ALLAH karki sharing,ga mai buqata saiya tuntubi wadan nan lambobin* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 1️⃣3️⃣ Fiddausi ce ta kirata tanason ta rakata wajen da take siyo musu kayan zaqi kamar yadda ta sawa syrup din da take baiwa shahidan suna,duk sanda shahidan ta buqata tana amsa ne kawai daga wajen fiddausin,wanda nafisa ce ta baiwa mima kudin da za'a siya a jibgewa shahidan,ita kuma mima ta baiwa fiddausi kudin ta saya ta aje din take bata,don ita bata harkar shaye shaye,barta da biye biyenta kawai,shahidan taso ta tirje don yau din anwar ya gaya mata zaizo akwai wata muhimmiyar magana da zasuyi,amma sai fiddausin taji haushi ta katse wayar sanda tace ba zata samu zuwa ba,ita dinma a karan kanta sai taga bai kamata taqi rakata ba,tunda abun nan tare suke amfana dashi,bugu da qari duk sanda takeso kyauta take bata shi ba tare dako sisinta ba. Tilas ta shiga bandaki ta sake gyara jikinta kasancewar tana al'ada ne,kuma idan tanayi din tana bleeding ba laifi,hakan ya sanya duk sanda zata fita take saka always biyu ko kuma pant biyu,yau always din tata ta qare saura daya saboda haka ta saka pant biyu duk da tana tunanin Allah yasa ya riqeta. Tsaf ta shirya ta shuga wajen umma "Umma....zan raka fiddausi gaisuwa,baban wata 'yar ajinsu ya rasu" "Ina ita fiddausin?" "Ta gidansu zan biya ai umma yafi kan hanya" "Saikun dawo" ta fada tana miqa mata dari biyu kudin mota,ta amsa ta miqe ta fice daga gidan. A qofar gida suka hadu da fiddausi "Amma karmu jima don Allah fiddausi saboda anwar kar yazo bai sameni ba,kinsan baison yawan fita" baki ta tabe cikin ranta tace "Yau za'ayi mai gaba daya ma ai" amma a fili sai tace "Sannu matar kulle,yaushe aka daura auren naku ban sani ba?" Harararta shahida tayi "Kinga banason wulaqanci,kome zakiyi ki tsaya iyani,koda ba'a daura aurenmu ba ya isane dani" "Allah ya baki haquri...shi yasa har na kira daddy A yazo ya kaimu saboda mufi sauri sai kuma nace ya barshi,don nasan halinki yanzu zakice ba zaki shiga motarsa ba" dan hade rai shahida tayi "Kinfi kowa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96