Chapter 94
Chapter 94
an murda qofar dakin,wanda hakan yaja hankalinta zuwa kallon qofar,yana shigowa idanunshi cikin nata,mamaki ya sanyata miqewa ta zauna sosai saman gadon,tama mance da irin dinkin da yake jikinta,idanunta fal da alamun tambaya,jingina yayi daura da qofar ya goye hannayensa a qirji yana qare mata kallo,sai a sannan ta tuna da rigar jikinta,tabi kanta da kanta da kallo saita daga kai tana hade fuskarta tsaf,miqewa tayi ta nufi wardrobe dinta ta soma lalubar mayafi,yana tsaye still yana kallonta har yanzu baice komai ba,harta gama yafa mayafin ta dawo gefan gadonta ta zauna "Ki shirya gobe qarfe tara na safe xamu fita tare xan saukeki gida" fuska a tattare ta bishi fa kallo har ya fice,saita ja qaramin tsaki ta koma ta kwanta tana tunanin ina zai kaita?,kuma me zata fita tayi. Tara saura tana tsaka da shirinta wayarta ta shiga ruri,ta qarasa inda take aje ta daga tana duba mai kiran,anty usaina ta gani,a ladabce ta daga suka gaisa sannan tace "Na kasa samun layin anwar,inata kira busy,taimaka don Allah ki gaya masa idan zai fito ya fito da wadan nan takardun" "Toh anty" ta amsa mata a ladabce tana aje wayar,qarasa shiryawa tayi sannan ta fito ta haura saman nashi,tana shiga yana aje wayar gami da miqewa ya tura qofar toilet ya shige,bata masa magana ba don qyashin hakan takeji,saita barshi ta samu saman kujerar mudubi inda ya tashi ta zauna tana dakon fitowarsa. Wayar daya aje saman mudubi wanda take dab da ita ta dauki ruri,idanunta kai kan me kiran,nafisa ta gani,ta riga data haddace sunan,saita dauke kai saidai hankalinta ya kasa daukuwa daga kai,tana jin sautin ringing din har cikin kanta harta katse,aka sake kira ta sake katsewa,ba jima wani kira yasake shigowa,batasan sanda taja wani mugun tsaki ba ta finciko wayar ta kasheta gaba daya ta dangwarar da ita awajen,tana tuna sanda ta shigo waya taga ya gama,wala'alla ma shi yasa anty usaina ta gaza samunshi wayama yake kenan "Ina ruwana da wayarshi" ta gayawa kanta tana sake tsuke fuska ita kadai,daidai lokacin daya fito daga bandakin jikinsa jiqe da lema,da alama wanka yayi,fuskarta a dinke tsaf cikin kaushi tace dashi tana miqewa "Anty tace karka manta ka fito da takardun nan" daga haka tayi gaba,binta yayi da kallo,tana gab da ficewa yasha gabanta,ya murza key ya rufe qofar,saita danja da baya tana dubanshi,kuka takeson tayi amma batasonyi a gabansa,don tasha alwashin ta daina yi din yana gani yana jin dadi "Ka budemin na fita na qarasa shiryawa" ta fada cikin sanyi,wanda ba haka taso,taso tayi maganar ne cikin kaushi da zafi,saiya kada kai yana duban idanunta wansa hakan yaso mata tasiri,saita zare nata idon gami da kauda kanta wani sashen daban. tokare _Dadai zakuyi haquri harmu cimma manufar labarin,don kowanne labari yana da manufar da akeso a cimma,idan kuma kunason shortcut shikenan_🤷🏽♀️ Mai yiwuwa gobe kujini shuru,idan kuma Allah ya bada dama to. *karku manta kuyi wekend dinku da tashar SAUTIN HIKIMA dake youtube,ku saurari littafanmu ba tare da kunsha wahalar karatu ba kuna daga kwance*💃🏻 *Asha weekend lafiya*🤝🏽 *Alqawarin Allah* 45 "Zuwa yanzu ya kamata ki fara koyan wasu abubuwan,saboda karta shigo ta rainaki" ya fada yana son dawo da salon tsokanarshi. Wani kallo ta watsa masa da idanunta sanda yake komawa zuwa bakin mudubi,wani abu ya tokare mata wuya "Wace zata shigo din?,bani ya kamata ka gayawa wannan maganar ba,don ni ba kallon mijina nake maka ba" saiya waiwayo yana zare idanu "Da gaske?,lallai kinci tuwo da yawa,wait....waima kallon me kike min?" Harara ta sake watsa masa ganin yanason maida abun shirme kamar yadda ya saba,baisan yadda ranta ke tafasa ba "Oho,koma meye ba damuwarka bane,ka budemin qofa kawai na wuce,abu daya na sani shine,daga kai har ita kada wanda ya sake yashiga hurumina" baki ya kama yana kallonta,sau tari yakanso yaga tana rashin kunya,sai dan qaramin bakinta yayita burgeshi,don a tsahon xamansu na baya bai taba ganin tana tsiwa ba sai yanzu "Idan kuma akaqi fa?" "Raine zai baci" ta amsashi kai tsaye,qaramar dariya ya bushe da ita "Kinga...kawai ki fito kice kishi ne yake damunki ko?,to kiyi haquri,na miki laifi" sake hararshi tayi,tanajin kaman ta makeshi ko zataji sauqi "Ni na gaya maka duka wannan na damuwata bace,bama kallon miji nake maka ba bare nayi kishinka,ka budemin na fice kawai" "Aiko kin makaro,dakin yadda kawai da hakan yanzu zan bude miki qofar salin alin,amma tunda kika musa to sai na gama shiryawa tsaf sannan zan bude ki mu sauka tare" tanaji tana gani yayi funfurus yahau shiryawa a gabanta ko kunya baiji,haka ta zauna ta kallo bango harya gama ya budeta. Har daki yabita ta gama daukar abinda zata dauka kaman wani body guard,tana kumburi tana komai amma bai kula ba ta fito suka fita. Gidansu ya soma kaita,ta cika da mamaki sanda suka isa taga ya sake cikinsu sosai kaman yadda suka saba a baya,sai taga kamar ma sunfi zumudin zuwanshi akan nata,hira suke abinsu da umma kamar danta,baqinciki yasa ta kasa sakewa ma bare tayi hira,basu bar gidan ba sai qarfe daya da rabi na rana bayan yaje masallacin layinsu yayi sallah sannan yace ta taso,kaman ba zata tashin ba,don ita sam lokacin bai isheta ba,amma yadda umma ke jifanta da harara yasa dole ta miqe tabi bayanshi. Daga nan gidan anty zubaida sukayi,can dinma haka suka gaisa da antyn cike da sabo,sannan ya yiwa anty zubaidan sallama kan zaije anjima zai dawo ya dauki shahidan. Kusan fiye da rabin hirarsu ya ranar jirwaye me kama da wanka anty zubaidan ta dinga mata da gugar zana,ta kuma fahimceta sarai saidai tayi kaman bata gane ba,duka dai kan zamantakewarsu ne da nafisa dake shirin shigowa gidan,wanda duka ita tana ganin wannan ba matsalarta bace,dubanta anty zubaidan tayi sanda suke tsaye cikin kitchen tana tayata yanka cabbage zata hada coleslow "Ranar yaushe zaki yinin naki ne banji kince komai ba,yaufa alhamis,lahadi kuma daurin aure" baki ta tabe bayan ta dubi anty zubaidan "Ko nawa bikinma ban tsaya wani tsara wuni ba bare bikin wasu" ta fadi cikin qunquni,murmushi ya subucewa anty zubaida saita kada kai,lallai yaro yaro ne,ga zallar kishi na bayyana kan fuskarta da kalamanta amma taqi yarda da cewa kishi take "Wancan daban wannan daban,bakyace ba zakiyi ba kodon idon mutane,kuma kema zaki buqaci wadanda zasu tayaki karbar amarya" "Waini zan karbeta ma?" Ta fada tana nuna kanta da wuqar hannunta "Eh mana,haka akeyi ai" saita jijjiga kai tana ci gaba da yankanta "Lalllai kam" anty zubaida ta fuskanci zancan ciwo yake mata ba tare datasan da hakan ba,sai kawai ta shareta suka shiga wata maganar daban. Bayan sunyi sallar la'asar anty zubaidan tace tazo ta rakata kitso,ba musu ya dauki mayafinta suka fita a motarta,huda tace zata bisu antyn yace sam tayi zamanta,suna tafe a motar antyn na nuwa shahidan wasu robobi masu dauke da gumba ta kwakwa da dabino,wanda idan kanaci zaka xaci an hada kayan qwalamane kawai sai aiki a jiki,wadda takan jima jikin mace bata bar jikinta ba,ta dinga mata dabara kanta dandana mata taji,haka ta dinga ci suna hira,antyn tana tuqi a hankali har sai dataci da yawa,ta sake nuna mata wata roba wadda ke cike da tsumi tace "Sha kiji wannan fa"dan bata fuska shahidan tayi "Wainikam anty wadan nan ba irin kayan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96