Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 79

Chapter 79

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,305 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

iya daurewa ba amai na taso masa,ya sanar mata kan zai wuce gida,cikin damuwa ta tsaidashi tasha gabansa tana duban yadda yanayinsa ya sauya,aman ya taso masa,yasa hannu da hanzari don ya kaudata gefe amma taqi ta matsa din,da haka ya soma wanke mata jiki dashi,daqyar ya matsar da ita gefe ya qarasa a qasa,yana ta jikinta daya bata mata amma ita sai yaha ba damuwarta bane,qarshe ma dayaqi tsaiwa ta gyara wajen tace "Idan baka bari ba wallahi kana kallo xan shanye aman gaba daya" cikin mamaki yake dubanta,qaramin murmushi ya subuce masa,ya zaci da wasa take "Toh shikenan bismillah,amma dai ni bazan barke ki wanke wajen nan da kanki ba alhali gani a tsaye" bai ankare ba ta durqusa,cikin zafin nama ya riqe gefan hijabinta gam da mamaki yake cewa "Kina hauka ne shahida?!,amaine fa qazanta" rai ta bata sosai "To matsa gefe idan ba haka ba na aikata" haka ya matsa din yana kallonta ta gyara wajen. Tunaninsa ya yanke sanda shahidan dake gabansa ta soma motsawa da alamun barin wajen dauke da farantin lemon "Kin makaro tunda ada kinsha ai" da hanzari ta dago ta dubeshi suka hada idanu,ta tuna lokacin da yake nufi din itama,amma saita yatsina fuska kamar bata gane ba "Kama zancan xamanin jahiliyyar shahida,kuma da ana maida hannun agogo baya da sai na maidashi na kuma goge wajen don baka cancan......" Bata kai ga qarasawa ba ta tsinci bakinta cikin nashi,ya riqe fuskarta da dukka tafin hannuwansa,ta tsorata sosai don bata zaci haka ba,garin yunqurin qwacewa ta saki jug da cup din duka suka zube anan qasa suka tarwatse,sai daya tsotse duk lips dinta da cikin bakin iya son ranshi sannan ya saketa,bacin rai a sannan ya bayyana qarara a fuskarta,ta bude baki xatayi magana cikin fushi ya rigata "Tunda wancan xamanin ya shude ba zaki iya gogewa ba saiki goge wannan ai na sabon zamani dake wanzuwa a yanzu,ki saku reza ki yanke bakin kiyar ki canzashi da wani" daga haka ya juya abinshi,rasa amsar bashi tayi ga kuka nason qwace mata kuma bata son tayi a gabansa,saita juya da sauri zata fice,tana bude qofar yana sake shan gabanta,fuska a turbune yace da ita "Wannan zaqin da bakinki yake ina fata ba syrup kika sha ba ko?,don nan gidan ba'a haka ciki" yakai qarshen zancan yana dage mata girarsa qwaya daya,kukan da take riqewa ya qwace mata,hawaye suka soma layi,duka girarsa biyun ya kuma dagewa "Au....shi kika sha kenan?,sauka ki tafi to kafin ya fara aiki" ya fada yana matsawa gefe gamida kafeta da ido "Allah yasakamin ban yafe ba" kawai tace tana ficewa cikin sassarfa,wata dariya ce taso qwace masa sanda ta fice din ya maida qofar ya tura,saiya tuna shahida 'yar 16 shekaru shida baya da suka wuce,bata da tsiwa amma bata iya bacin rai ba,baiji dadin kukanta ba amma yasan wannan ce kawai hanyar da zai sata tayi magana,tunda can mutum ne shi da bai iya gaba ba sam,duk da har yanzu bacin ranshi game da ita na nan danqare cikin ranshi amma bazai yarda ayi xaman maqiya dashi ba. Yana kwashe fasassun gilasan yana tuna abinda ya farun,yakai tatsunsa saman lips dinsa ya shafa,yadan cije lebansa na qasa kadan,tabbas yaji zaqi a bakinta,saidai yasan ba kayan maye bane,don tunda ya bada sadakinta ya zuba ido akanta sosai amma bai taba ganin wani abu da zai sashi ya zargeta ba,ko da shahida nakan halayenta nada da idanunsa suka gani,koda bazai dore a zaman aure da ita ba zaiyi qoqarin ganin ya maidata saitinta kodon soyayya da amanna da mahaifinta ya bashi a baya,duk da hakama baiga wani mummmunan abuba game da ita har yau daga sanda ya soma sanya idanu a duk motsinta. _gashinan yau na muku,amma har gobe sai jibi idan Allah ya kaimu_🙏🏽🙏🏽 *Alqawarin Allah* 3️⃣8️⃣ Kafin ta sauka qasa ta dan jima a tsaye saman step na kusa da qarshe tana dai daita yanayinta sannan ta sauka a hankali. Ana qwala kiran sallahn ya sauko cikin jallabiya mai gajeran hannu fara sol da ita,bisa dukkan alamu sabuwa ce,jikinsa na tashin qamshin turare mai sanyi kaman wanda yayi wanka dashi,zuciyarta taso yadan fisgeta ta kalleshi amma tayi ta maza ta dake kaman bata ganshi ba har ya fice masallacin. Ba'a jima can da idarwa ba ya dawo,ya zauna saman kujerar falon suna dan taba hira da anty amina kafin su kammala kintsawa,da suka tashi tafiya saita rasa me zata basu,qarshe data shiga dakinta wajen akwatunan lefanta ta isa ,karo na farko data budesu ta kuma kalla abinda ke ciki,guda biyu ne masu dauke kayan sawa taf daqyar aka rufesu don ba abinda aka taba a ciki,ta dinga daga kayan daya bayan daya tana kalla,kan wata shadda lace ta tsaya,ta kalleta sosai,tun daga colour har design din choice dinta ne,tasan duk duniya kuma babu wanda yasan hakan sai anwar,hakan ya saka ta sanya hannu ta cirota,ta kalleta sosai,iya kyau ta mata kyau qwarai,kuma kana ganinta kasan babbar ce,saidai ba zata iya sanyata a jikinta ba,tasan anwar ne ya zabeta,ta yanke ta baiwa anty amina ita,sauran manyan su uku ta zaba musu atamfofi,yan yaran da yan matasan kuma ta diba musu kayan kwalliya,ta zaba kayan gararta da yawa ta hada musu. Anwar yana tsaye ta miqawa kowa,ta miqo ledar anty amina yafi kusa da inda take tsaye,saboda haka ya zira hannu ya karba ya buda yana gani sannan ya rufe,daga kai yayi tasan ita zai kalla saboda haka ta dauke kai,ilai kuwa itadin ya kalla,haka kawai yaji kyautar ta masa ciwo,bawai saboda kudin abarba,a'ah,yafi qarfin kudinta hakanan anty amina a wajenta tafi qarfi wannan,yasan cewa da biyu tayi kyautar itama ta san da hakan,abinda ya bata ranshi kenan. Har bakin mota tayi musu rakiya,anwar yace a matse sukazo hala,su ragu wasu su shiga motarsa ya kaisu,ta musu sallama ta koma cikin gida,harsun gama shiga yace yana zuwa,ya buda murfin motar ya koma cikin gidan. Tana tsaka da tattare wajen taji shigowarsa,ta daga kai ta dubeshi saita basar taci gaba da abinda take kaman bataga shigowarsa ba,bayanta kadan ya tsaya,kaman bazaiyi magana ba sannan daga bisani yace "Duk yadda kikeji a zuciyarki game dani kusan nima haka yake koma fiye,amma,karki sake gangancin da kikayi yau,duk kayan dana siya nasan wa na siyawa shi,idan da buqatar bada kyautar irinsu a siyo daga waje ba daga cikin akwati ba" idanunta ta watsa masa sannan tace "Ina ruwan wani?,ina cewa kayana ne ko?" "Alright,hakane fa,amma keda kayan qasan wa kuke?" "Oho" tace tana ci gaba da aikinta,shuru yayi yana kallonta,saiya jinjina kai sannan yace "Zaki gane kurenki" ya juya ya fice saboda tunawa da yayi yabar mutane a mota,tsaki taja taci gaba da aikinta tana cewa "Na dade ban gane kuren nawa ba" A gurguje ta gama duk abinda zatayi ta dauki duk abinda take buqata ta shige dakinta,wanka ta soma yi sannan taci abinci,ta jawo wayarta ta fara amfani da ita,kama daga kiran waya,da duba saqonnin wayarta ta watsapp,bataji shigowarsa ba sai wajen qarfe goma na dare,dai dai sannan ta miqe ta kashe qwanta ta koma gado tayi addu'ar bacci tayi kwanciyarta. Shika koda ya shigo dakinsa ya wuce abinsa,baibi kota kan abincin dake kan tebur ba. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Washegari ma ta samu baqi ba laifi duk da basu kai na jiya

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});