Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 48

Chapter 48

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,315 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yace "Auto da sauqi abun,kaga kenan allurar cikin ruwa ce,mai rabo ka dauka" ran nuradden saiya kai qololuwar baci,hakan ya sanya shahida ta dubi saddam "Banason tashin hankali saddam,meye haka?" Baison nuradden ya gane cewa bai taba furta mata kalmar soba bare ya sake samun qwarin gwiwa,hakan ya sanya ya dubeta "Ba manufata na bata miki rai ba,sai anjima" ya juya ya fice. Sosai yake jin babu dadi cikin ranshi,saiya dubi shahidan "Shahida...tsorona da fargabata ta sake daduwa,inajin har cikin raina bani da tabbas idan har baki amsa min cewa ni kikeso ba kuma ni xaki aura ba" gaba daya sai lissafinta ya nemi dagulewa,batason ta dauki alqawarin da zai zame mata ciwo ko nauyin da wuya ta zaiyi wahala ya iya dauka,saboda haka cikin sanyin murya da kwantar dakai tace "Tsoron meye haka nuradden,ka kwantar da hankalinka don Allah". Duban nafisan yayi fuskarshi a hade" me kikayi haka kenan?,me yasa tun farko baki duba lafiyar atm din naki ba saida kika gama siyayyar?,bayan kinsan accnt din aya samu matsala sai xuwa gobe zai soma aiki?"langabe mishi kai tayi "Please anwar...don Allah kayi magana da mai kamfanin gaba daya,na tabbatar ka sanshi tunda naji kace bakason yasan ka shigo kamfanin,tunda ka bada rabin kudin yanzu zai amince ka aiko da saura idan ka koma office,Allah wannan sarqar nasha wahala na dade ina nemanta,kuma kanaji suma sukace dsign dinta kadai yayi saura,ba lallai idan na ajeta naje na dawo na sameta" idanunsa ya lumshe kaman bazaice komai ba,haka kawai yakejin kasala tunda ya tashi yau,hakanan zuciyarsa da jikinsa sam babu dadi,baice komai din ba ya fita daga wajen da kanshi ya taka zuwa sashen biyan kudi,suka tarbeshi don tunda ya shigo kamfanin suka gane waye,hakan ya sanya suketa nan nan dashi,daya daga cikin ma'iakatan ya yiwa magana yana son ganin rayyan "Ranka ya dade,oga bai shigo ba,amma babu damuwa zaka iya ganin rahama" dan shuru ya sake yana fidda wayarsa daga aljihunsa ya duba lokaci,sannan ya lalubo wata number ya kira,bata shiga ba,duka lambobin rayyan din basa tafiya,saiya sake kiran wata number din,ba jimawa aka daga,ya ambaci adadin kudin da yake buqata ya gaya masa inda zai kawo masa "In sha Allah yallabai ina hanya" daga haka ya maida wayar aljihunsa "Ai...ranka ya dade basai ka zauna jira ba,rahaman kawai zaka yiwa bayani shikenan zata shigar ne cikin kundin bayanan shiga da fitar kudi na kamfanin" lokaci ya kuma dubawa,shi kansa baison zaman,saboda jiransa da ake,banda ya riga da yayiwa nafisan alqawari kuma baison rashin cika alqawari da baiga abinda zai zaunar dashi har haka ba "Ba damuwa,bani number din office din" "To ranka ya dade" ya fada yana gaya mishi cikin sauri kai tsaye ba tare da an sanar da mai office din ba saboda sanin wayeshi baida buqatar sai sun hadashi da mai masa iso,a nutse ya juya ya soma takawa "Ina zaka?" Nafisa dake addu'ar Allah yasa su gama lafiya su fita lpy karya hutsance mata ta tambaya "Ki jirani" kawai ya fada yanayin gaba. Kallon number office din yayi sosai sannan yaja da baya ya kalli qofar,ya dora hannunshi saman handle din ya tura a hankali wanda hakan ya sanya basuji alamun bude qofar ba. *zafafa biyar na kudine,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karki sharing,idan kina da buqata ki tuntubi wannan number* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *Alqawarin Allah* 2️⃣4️⃣ "Hankalina bazai taba kwanciya ba idan ba ganinki nayi a gidana a matsayin matata ba...shahida" ya kira sunanta yana miqewa zuwa gabanta,gab da ita ya zauna akwai kusanci sosai tsakaninsu,tanason sake ja baya ta kasa,ya saka hannunshi cikin aljihunsa ya ciro zoben rannan daya siya ya bata tabar masa abinsa cikin mota,ya bude gidan xoben ya ciroshi "Ki yarda mu qulla wanna yarjejeniyar tsakanina dake yanzu yanzu shahida,ita kadaice zata dan kwantar min da hankalina" bata ankara ba ya kama yatsanta yana ci gaba da roqonta,wani abu anwar yaji ya dakar masa tsakiyar kai,yayu yunqurin juyawa ya fice daga office din salin alin kaman yadda ya shigo,saidai ya gagara haka,ji yayi kaman an kafeshi idanuwanshi a kansu,ya gaza daga qafarshi bare ya juya ya fita din,da hanzari shahida tace "Sakemin yatsa nuradden...basai ka saka..." Bata qarasa kaiwa ba ya soma zura mata zoben,bansan ya akayi ba,baisan ta yaya ba ya tsinci kanshi da furta "Stop it!" Cikin tsawa da hargagu,idanuwanshi na sauya kala,wanda yayi sanadiyyar rashin shigar zoben yatsanta,dukkansu waiwayawa sukayi don ganin waye,ga tsammanin nuradden saddam ne ya dawo,amma sai yaga bashi bane,matashin saurayi ne da shekarunsa suka tasamma talatin da biyar,mai kyau kwarjini da cikar zati tsaye yana dubansu,idanunshi qyar kan nuradden din,yayin da idanun shahida ke kanshi,mamaki yaso daskarar da qwaqwalwarta,me yake nan?,me ya kawoshi?,yazo ci mata mutunci ne?,koko yazo tozartata cikin mutane ne kaman yadda yayi mata wancan karon,anya ma shine kuwa?. Idanunsa har yanzu nakan nuradden suna kallon kallon har zuwa sanda ya soma takowa zuwa cikin office din hannayensa soke a aljihunsa,cikin wata izza da taqama,qarfin gwiwa da qarfin halin da sam baisan yana nunashi ba muraran. Kafin ya qaraso shima nuradden din ya miqe tsaye yana dubanshi gami da jiran isowarsa,a qalla kusan minti daya sukayi suna duban juna,taqin dake tsakaninsu kadanne,cikin wata murya dake cike da ginshira isa da bada umarni yace "Kar ka sake gangancin aikata haka,idan ba haka ba?...." "Idan ba haka ba me?" Nuradden ya maida masa cikin zafi "You will regret it!" Ya qarasa cikin tsawa,murmushin baqinciki da kishi nuradden yayi,wai me yasa yayi saken da har yanzu bai mallaki shahida ba?,me yasa yayi bacci har akeson kawo masa farmaki? "Ina tunanin kana cikin masu sonta ko?" Ya fada yana waiwaya ya dubu shahida dake tsaye tana dubansu kaman wadda ta zama bebiya "To ka makaro,don kuwa shahida tawa ce,mallakina ce,hakanan baka da wani hurumi na shiga sabgata da ita,idan ma kace zakayi gigin shiga kunyace da nadama a qarshe zata riskeka,yadda ka ganmu haka zaka barmu,kayi kadan ka shiga tsakaninmu,baka da qarfi iko ko izzar rabamu,tarayyata da shahida ba muhallin shigarka bane,bama kaiba,har wani ma dake iqirari ko gigin cewa yana sonta" idanunsa ya lumshe kalaman nuradden na sauka cikin kunne da kwanyarsa,yau shi ake furtawa kalaman nuna iyaka akanta?,wani abu mai nauyi ya sauko saman zuciyarsa,ya bude idanunsa dai dai lokaci da shahida ke cewa "Please noor,wannan baikai abunda zaka bata ranka akai ba,nida kai mutu ka raba ne,qaramin dalili ko qaramin abu irin wannan yayi kadan ya raba tarayyarmu nida kai" tayi maganar kanta tsaye,direct daga zuciyarta ta hada kalaman,idanunta akanshi,sai ya qarasa bude idanun nashi gaba daya ya watsasu a kanta,ta kauda nata idon da sauri tana baiwa kanta qwarin gwiwa dason yin ramuwar gayya ko sau daya ne kafin wannan damar ta kubce mata,tana son ko sau daya ne yaji ciwon rai ya kwanta yana tuna kalamanta "Me kakeyi ne anwar?" Yaji tambayar tsakar kansa,kaman an sake doka masa wani abu,yadan runtse idonsa kansa na sarawa daya tuna ainihin abinda ya kawoshi office din "Assalamu alaikum,ranka ya dade...yallabai din ya shigo,ya nemi ma yin magana dakai" wata murya ta ratsasu duka su ukun,ya waiwaya yana dubanshi,ma'aikacin daya baro dazu ne a daya sashen,sai ya jinjina masa kai ya juya ma'akacin shima cikin girmamawa ya fita. Kallonshi ya maida kan nuradden ba tare daya dubi shahidan ba,ya murtsa yatsunsa sosai kaman

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});