Chapter 16
Chapter 16
Allahu yana tare da mu" "A'ah anty.....karki takurawa kanki karki damu,nima zanci gaba da nawa qoqarin...". A hankali ta koma da baya cikin tsananin mutuwar jiki,ba labe tayi musu ba amma ta kasa tafiya sanda yake wayar da anty husaina,cikin mutuwar jiki da karaya take juyawa zuwa cikin gidan,qirjinta ya quntata qwalla ta cika mata idanunta,dama akwai wani abu da anwar zai iya boye mata game dashi?,da wannan tunanin ta isa dakinta,gefan katifarta ta samu ta zauna tallafe da kumatunta,batasan adadin lokacin data dauka a haka ba har ya tarawa wayarta miscal bata gani ba,saida ummanta ta daga labulen dakin "Wanne shashanci ne kike haka shahida?,kinsan ba zaki samu fita ba kikabar anwar qofar gida yana jiranki?" Hannayenta ta sauke tana cewa "Yanzu zan fita umma" sakin labulen tayi ta juya ta fice tana mita "To ke kuma ya isa haka malamar mita,tunda ta baki uzuri basai kija bakinki ki shuru ba?" Ta jiyo abbanta yana fada "Kaga kar kace zakamin fada,don na mata magana laifi nayi?" "Ba laifi bane,mitar ne ni banason ji karki cikamana kunne" "Wai yau cin mutuncin naka ne ya motsa baban shahida?" Ta saki abinda take ta zuba masa idanu tana tambayarsa,saiyayi banza da ita ya zubda ruwan daya kurkure bakinsa ya dauki hularsa ya fice,ajiyar zuciya shahida dake tsaye bakin window ta saki,ta godewa Alla daya taqaita cecekucen nasu baiyi tsaho ba har yaja hankalin anwar ko yajisu. Katifarta taje ta daga,kudaden da uncle hisham ya bata ta dauko,ta zauna ta qirgasu a nutse sannan ta shiryasu,koda batasan nawa anwar ke buqata ba tasan cikon kudin bazaikai yawan kudaden dake hannunta ba,don kudaden da uncle anwar din ya bata suna da yawa,don taji ma anty amina na cewa mama su aje a karba a siyawa shahidan tukunya mai sha biyu a aje mata,lanqwashesu tayi sannan ta miqe ta gyara mayafinta ta fice. Sanda ta koma yana zaune kan dakalin,ya zubawa qasa idanu wanda hasken farin wata ya haske jikinsa yake bashi hoton inuwarsa,a hankali ya dago kai idanunsu suka hadu da juna,wani sanyi yaji har cikin rai da zuciyarsa,saiya sakar mata murmushi yana jin kaso tamanin na quncin da zuciyarsa ke ciki ya tafi,kallon farko ana biyu ya karanci lallai akwai abinda yake damunta,duk sai yaji wani iri,yaji babu dadi,duk wata walwala da karsashinsa ya shiga yin nashi guri,shi ya amshi daddumar hannunta ya shimfida ya kuma yi mata nuni data zauna,batayi musu ba ta zauna din,yana tsaye qyam a kanta yana qare mata kallo,ya samu kanshi da kasa zama "Mene ne yayi kutse cikin farincikin gimbiyata?" "Kaine...." Ta fada kanta tsaye,cikin sanyin jiki ya samu dan wani dutse dake daura da ita ya zauna samanshi "Bana fatan kasancewar wannan ranar....wane kuskure na tafka haka harya zama tarnaqi wa farincikin zuciyata?" Hawaye ta soma zubarwa,bana komai bane saina tausayinsa,zurfin cikinsa yayi yawa,kara da kawaicinsa sun baci,amma ko daya bata son ya sake boye mata wani abu daya danganceshi,tana ganin kaman hakan wani naqasu ne tattare da dangantakarsu,zai zama tamkar bai bata muhimmancin da take tsammanin ya bata ba "Ashe dukan inda nake tunanin nakai bankai can ba a zuciyarka?" "Ya salam" ya furta fuskarshi na nuna tsantsar tashin hankalin daya shiga,wanda har cikin zuciyarshi haka ne,wanda har yanajin ya zarce na rashin kudin registration da bai samu ba "Shah......" "Kar ka sake cemin komai....na kamaka da laifuka guda biyu kawo yanzu,ban taba boye maka komai daya danganceni ba....amma kai ka boyemin abubuwa har biyu,ban sani ba ko.matsayina baikai nasan wannan fannin ba...." Sanyi ya dinga ji yana ratsa qasan zuciyarshi,duk da bai fuskanci me yayi mata ba,dubanta yake cike da qaina soyayya sa shauqi mai yawa,ta damu da lamuransa fiye da tunanin mai tunani kamar yadda ya damu da nata,bai tsammaci zata soshi kamar yadda yakesonta ba,ya zaci zata soshi ne irin son da baikai ya kawo ba,kodon kyau da Allah ya bata,kodon gata data d'arashi,ko don saboda farinjini da Allah yayi mata "Yanzu karatunka ba nawa bane?" Ta fada maganar quruciyarta na fitowa fili,hakanan ta b'ata rai sosai ta kuma tsareshi da ido,murmushi ya saki wanda ya bayyana fararen haqoranshi "Nakine my shahida" "Don me baka gayamin halin da kake ciki ba?" Dan shuru yayi yana tauna amsar da zai bata,tsahon minti guda kafin yace "Shahida....kin wuce duk inda kike zato kike tsammani a wajena,tunda Allah ya busan numfashi ban taba qaunar wata d'iya mace ba saike,nine namiji,ni nake nema,kuma nine sama dake,bai cancanci ace dukkan wata wahalata tana wuyanki ba" "Koda bani da abun da zan taimaka dashi ai na sanyaka cikin addu'o'ina ko?" Idanunsa ya lumshe idanunsa yayi yana sakin murmushi "Ni na sani shahidana koda banda damuwa ba zata daina sakani a addu'arta ba" "Ta yaya zan aminta cewar mun zama daya kana boyemin ire iren wadan nan abubuwan?" "Shahidaa...karki sake tunanin bamu zama daya ba,kin zama muhammad anwar,na zama rahamatulshahida" sunan ya bata dariya har sai data murmusa,tafin hannunta ta bude sannan ta miqa masa kudin hannunta "Ungo qirgamin" amsa yayi yana zolayarta,sannan ya soma qirgawa yana cewa "Shahidana ta zama hajjaju" sai daya gama qirgawa sannan ya dago ya dubeta yana gaya mata nawa ne,kai ta gyada duk da tasan nawa ne dama "Kayi amfani dasu" sak ya tsaya yana dubanta kafin yace "Shahida...." Idanunta ta ware masa tana dubansa itama,ya gane me take nufiSai ya saki murmushi "Aro na baka,amma kayi duk amfanin da kakeson yi dasu" "Kai amma wannan yarinya kin iya bada rance....to na gode Allah ya bani ikon biya" daga haka sukaci gaba da hirarsu,saidai rabin hankalinsa dukka yana kan halayen shahidan,yana sake godewa Allah tabbas baiyi zaben tumun dare ba,hakanan ya tabbatar bai miqa zuciyarshi inda bai cancanta ba. Wannan abu da shahidan ta yiwa anwar ba qaramin qara mata qima yayi a idanun anty husaina ba,wata qauna take mata tamkar diyar cikinta tun kafin ma ta yiwa anwar hakan,ta yadda ta kuma yi amanna cewa anwar yayi dace da matar aure,ta kuma shiga sahun masu masa addu'ar Allah yasa shahidan ta zama mallakinsa. Ta gefan anwar dinma tuni ya shiga bakunan 'yan uwan shahidan musamman 'yan gidansu da anty amina wadda sukafi dasawa da shahida duk cikin 'yan uwan mamanta,kasancewar tasu tafi zuwa daya da mamanta,kuma ita daya ke gaya mata magana itama maman da ita take shawara. Cikin ikon Allah anwar yayi registration dinsa,komai yaci gaba da tafiya dai dai,rayuwarsu da shahida kuwa ta zama abar kwatance ga duk wanda ya sansu,kowa najin jinin danuwansa na yawo a nasa jikin,tun mutane na mamakin yadda sukeson juna har abun ma ya zame musu jiki,su kansu yadda suke nunawa kansu qauna basusan sunayi har haka ba saidai a gaya musu. Sannu a hankali rayuwa taci gaba da juyawa,ta wanni fannin ana samun ci gaba yayin da wani bangaren yake zamowa koma baya da babban naqasu wajen bawa. Zuwa sannan shahida sun shiga ss 3 term din farko,a sannan ne Allah ya yiwa mahaifin zunnurah rasuwa,hakan ya zama silar barinsu garin kano sukayi qaura suka koma katsina cikin danginsu,dalilin kenan daya sanya kusancin shahida da firdausi ya sake samun tagomashi mai yawa,ta maye mata gurbin zunnurah,yayin da ita da zunnurah ya zama sai a waya,lokaci lokaci idan sukayi waya tana sako mata zancan fiddausin tare da sake ja mata kunne kan tayi hankali da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96