Chapter 86
Chapter 86
matuqa,ta sake fidda kyawunta,kallo daya xaka mata kasan macace mai aji tako ina,wannan itace ranar farko da zata soma zuwa office din anwar da sunan ma'aikaciya. Shi dinma yana tsaye daura da teburin yana kurbar tea gami da jefa soyayyen chips a bakinsa,kacokam idanunsa nakan wata takarda dake saman teburin kusa da farantin chips dinsa,wanda ke dauke da zanen taswirar wani gini da gwamnati ta basu kwangilarsa da xasu soma yinsa cikin satin. Takun daya soma ji shi yaja hankalinsa,har yakai kofin bakinsa ya janye ba tare daya kurbi tea din ba,daga sama zuwa qasa ya qarewa kwalliyar tata kallo cikin taqaitattun daqiqa ya kauda kanshi yaci gaba da shan tea dinsa. Qarasowa tayi itama ta fara hada nata ba tare data dubeshi ba tace "Gd mrng" fuska a tsuke "Mrng" ya amsa mata a taqaice shima yana juya fasalin takardarsa ba tare daya dubeta ba,wani abu ke tsunkulin zuciyarsa,shigarta sai yaga ta bayyana ado da yawa,duk da ko ina a jikinta rufe yakr ruf ba wani abu nata daya bayyana,amma sai yake ganin kamar kallonta za'a yita yi idan suka je,dana sanin cewa tayi aiki a kamfaninsa ya kamashi,inama ace cewa kawai yayi ba zatayi aikin ba gaba daya,gashi ya ruga ya furta babu damar ya canza,yin hakan zai nuna qarantarsa ne kawai. Sai daya gama tas ya dire cup din yana cewa "Wannan shigar batayi ba,kije ki canza wata ki sameni a mota,idan kuma kika makara to cikin albashinki" daga haka ya juya ya soma takawa,ya dauki handkherchief dinsa da muqullin mota dake aje saman daya daga cikin kujerun falon,ta bishi da kallo galala baki sake harya fice,sai daya bacewa ganinta sannan ta dauke idanunta tana lumshe ido,takaici nason kamata amma tana daurewa. Yana daga xaune cikin motar,ta baqaqen gilasan da batasan yana kallonta ba ya xuba mata ido,karo na biyu kenan daya sake maidata ta sauya shiga amma shi har yau baiga wani abu na kyanta daya buya ba,bayyananniyar ajiyar zuciya ya sauke,tunda can yasan cewa haka take halittarta ce,duk kayan da zata saka suna mata kyau gami da dacewa da ita komai rashin kyau ko tsadarsa,agogon dake daura a hannunsa ya kalla,dole ya haqura ya qyaleta su tafi hakanan,zuwa yanxu ya cinye sauran lokacin da suke dashi. Tana zuwa gidan baya ta shiga,baice mata komai ba yaja motar suka fice daga gidan,suna dab da ginin kamfanin ya tsaida motar,ba tare daya juyo ya dubeta ba yace "Dawo gaba" jim tayi sai kuma ta fito don batason ma ta yawaita magana dashi. Tun daga harabar kamfanin ta karanci yadda suke ganin qima daraja da mutuncinsa,wannan karon baiyi parking inda kowa yake ba,sai dayaje gaban ginin sosai sannan ya tsaida motar suka fito,basu shiga ta gaban ginin ba saita bayanshi. Kallon office din babu abinda ya tuna mata dashi face nata office din,kusan tsari yanayi da kuma zubinsa kamar nata office din,take kewarsa ta kamata,ta lumshe idanunta sanda take zaune kan cushion din office din tana jira ya kaita nata ofishin. Abinda ya bata haushi da mamaki shine bai wuce yadda taga yayi zamansa kan tashi kujerar ba ya shiga ayyukan daya taras kan teburinsa ba,yayin da take zaune shuru bata wani aiki. Ganin sun cinye awanni biyu cur a haka ya sanyata gyara zama sannan ta dubeshi "Ban gane manufar ajeni cikin office dinka ba,ka mantane aiki nazo yi?" Sai sannan ya daga kai ya dubeta,saiya maida kan cumputer dinsa yana cewa "Na fiki sanin ai aiki kikazo yi,gaggawar me kike?,zakiga aikin naki ai" daga haka ba wanda ya sake tankawa wani,saidai sau uku tana daga kai sai taga kaman kallonta yake,daga kanta yasa ya kauda nashi kan,saidai har yanxu bata kamashi dumu dumu ba shi yasa bata tabbatarwa da ranta hakanne ba. Minti talatin bayan nan yace "Hadamin coffee,ki bude can ki ciromin cake guda uku" duk yayi maganar ne ba tare daya dubeta ba,karon farko daya fara bata umarni irin haka tunda sukayi aure,saita miqe din tayi yadda yace ta dawo ta zauna. Ba'a jima ba sosai ya sake cewa ta dauko mishi ruwa,ta dauko ta aje masa saman table din,saiya daga kansa ya kalleta sannan ya maida kan computer dinsa yaci gaba da aikinsa,awa biyu tsakani yace ta dauko mishi lemo a fridge,idanunta ta juya cikin nuna qosawa,ta sauke numfashi sannan taje ta bude ta dauko masa ta aje "Ba wannan kalar nakeso ba,ki duba akwai wani daban shi zaki dauko min" hadiyewa tayi ta juya din ta maida ta dauko masa ta aje,saiya dubeta ya kauda kai "Waishin haka ake bawa mutum abu,a dire masa kaman dutse,baza'a bude masa ba bare a zuba masa?" Hannayenta ta goya a qirjinta ta zuba masa ido "Wai na tambayeka?,aiki nazo yiwa kamfani ko kai nazo yiwa aiki?" A nutse ya dubeta sannan ya ture cumputer din gefe kadan ya hada yatsunsa cikin na juna "Bakisan cewa nine kamfanin ba gaba daya?" Ido ta fiddo alamun bata gane ba,girarsa ya daga mata "Eh,aikin kamfani xakiyi,kuma nine kamfanin gaba daya,babu aikin dayafi nawa aikin,wannan aikin shine aikinki a office dina,zan biyaki albashi kamar kowa albashinma daya fi na kowanne ma'aikaci,ba shikenan ba?" Idanu kawai ta zuba masa tana kallonshi yana fidda qaramin murmushi,tsantsar raina mata wayon da yayi kawai ya isheta bacin rai,saita juya kawai ba tare data tanka masa ba ta nufi qofar fita. Gabanta yasha ya tsate hanya "Ina zaki?,lokacin tashi baiyi ba madam" "Aikinne na fasa bazanyi ba gaba daya" duka kafadunsa ya daga,hakan ya masa shima,don baisan ta yaya zai dinga barin mutane na shiga masa office ba alhali tana ciki "Fine and good....saiki jira sai lokacin tashi yayi saimu wuce gida" daga haka ya juya zuwa wajen wayarsa da tunda suka fara taqaddamar ta soma ringing,daga wayar yayi yana dubawa,wannan shine kira na dari da biyu daya samu da lambar daga farkon satin xuwa yau,tunda ya daga yaji muryar nafisa bai sake daga wayar ba,don baisan me kuma zata ce masa ba,me yayi saura tsakaninsu?. Wayar ta wurgar a gefanta ta fada saman kujera tana yamutsa gashinta,sam ta kasa jurewa da rashin anwar kamar yadda mima ta shawarceta ta jira sai zuwa wani lokaci da ita miman ke shirya mata,ta rasa ta yaya zata iya jurewa,daga qarshe dole tabi zabin ranta ta soma neman khalipha baji babu gani,tana neman hanyar da zata gyara kurenta,kullum ranta soyuwa take ta gaza sukuni idan ta tuna yanzu haka fa yana can suna rayuwarsu shida shahidan?,me yasa kishi ya rufe mata ido haka ta tauyi rayuwarta?,ta yaudari kanta akan ba zata iya aurenshi ba?,bayan tasan cewa ka ta kawai ta yiwa qarya,ta ina zata soma gyara wannan babban kuskuren data tagka,tasan cewa abune ba mai sauqi ba musamman idan ta tuna da yadda ta samu soyayyarshi a baya,saidai koma meye tanajin zata jure harsai haqarta ta cimma ruwa,sai taga abinda ya turewa buzu nadi,zata aje mima a gefe wannan karon,zatayi yaqi ta samawa zuciyarta abinda takeso kota yayane ma,idan yaso ta nemi miman daga baya su dora daga inda suka tsaya. Dirowa tayi daga saman gadonta ta shiga bandaki ta dauraye fuskarta sannan ta yafa qaramin mayafi saman kanta ta fito. Dakin mahaifiyarta ta wuce,ta sameta zaune tana waya,saita samu waje tana jiranta garta kammala,kusan tunda abun ya faru ta sake dauke mata wuta,a baya ta sani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96