Chapter 63
Chapter 63
sanda labarin ya shiga kunnenta,qyaleta tayi bata bi ta kanta ba,ta barta ta gama kukan zuciyarta ta huce tukunna. Tamkar zata zauce haka taji,ta kai ta kawo ta kasa zama kamar wadda ta hadiyi tabarya,wannan wacce iriyar masifaffiyar shahida ce?,wanne irin mayen anwar ne?,ace duk yadda takai ga rabasu haqanta ya gaza cimma ruwa?,iya abinda ya kamata tayi don rabasu tayi amma ace bayan shekaru shidda sun sake dawowa sun jone?,idan ma kisa ba batasan me zatayi don rabasu ba,wayarta ta rarumo ta kira number mima,saidai hartayi quginta ta katse bata daga ba,haka ta dinga kira ba qaqqautawa amma bata daga ba,cillar da wayar tayi cikin muryar kuka mai cike da bacin rai da qunan zuciya tace "Shegiya mahaukaciya,wai ina kika shiga ne?!" Ta qarasa fada cikin qaraji wanda banda sautin tv dake aiki ba abinda zai hana momyn jiyo sautinta. Haka ta dinga qaramin hauka ita kadai cikin dakin har sha biyu saura na dare sanda wayarta tahau kuka,ta daukota da hanzari tana tsammanin mima ce,maimakon mima anwar ne,aje wayar tayi kawai tana kallonta harta qaraci kukanta ta gama,sai daya kira sau uku bata daga ba tana zaune da kallon wayar ruwan hawaye na fita daga idanunta,tana ganin hakan da zatayi kawai shine zaisa anwar din ya janye qudurinsa ya haqura shahidan. Washegari qarfe goma na safe tana gaban mudubi a zaune tana kallon yadda fuskarta ta qojale saboda kukan data kwana tana yi wayar ta sake burari,wannan karonma anwar ne a maimakon mima,bata da mafita tilas ta daga wayar ta sake gaya masa kalaman da zasu tabbatar masa da cewa ta rabu dashi kp hakan zai tsoratashi ya janye nufinsa "Karka sake kirana matsawar kana kan qudurinka na hada aurena da wata macen daban,na gaya maka tun jiya nikam nafisa bazan aureka ba anwar muddin kana a matsayin mijin mace biyu,na haqura dakai har abada" daga haka ta yanke kiran,saiya furzar da numfashi daga bakinsa ya baiwa banza ajiyarta,ya aje wayarshi yaci gaba da shirinsa,shikam ya yankema ransa babu sauran wata mace da zata sake bashi wahala,bazai sake son wata ba bare ta gasa mishi zuciya yadda ya faru dashi a baya,ya saki qaramin murmushi sanda ya tuna cewa da sonta yake da tuni yanzu yana cikin tashin hankali da dimuwa a sanda tace bata sonshi,yanzun kam hankalinshi kwance yake jinsa,saidai kuma wani bari na zuciyarsa yana dan jin damuwa,musamman idan ya tuna da mahaifanta yadda zasu dauki maganar,da wannan tunanin ya gama shirinsa ko abinci yau bai saurara ba ya dauki muqullinsa ya fito,kafin ya tashi motarsa ya tsaya ya turawa anty usaina yadda sukayi da nafisan,don baison kiranta ma bare ta bijiro da wani abun da zai hanashi uzurinsa nayau. ***** ****** ****** ***** "Wannan sakarcin banza ne ai sakarcin wofi,ta isa ta haramta abinda Allah ya halatta?" Alhj abba mahaifin nafisa ya fada cikin fushi da bacin rai yana duban mummy mahaifiyarta,kai ta gyada itama,sau tari tana mamakin halayen nafisan,ta rasa inda take debo wasu baqaqen halayen,abubuwa da yawa ita dai ta sani ba halayyarta bace kota mahaifinta ba "Atoh,nayi mata magana daxun da safe ta nunamin tana kan bakanta" mummy ta baiwa alhj abba amsa,shikam anwar yana daga gefe kanshi a qasa cikin girmamawa yana saurarensu,baice komai ba sai a sannan "Kuyi mata uzuri,duba da yadda zancan ya sameta a qurarren lokacin da bata zata ba,ni kaina bani da masaniyar abun zai kasance haka sai gab da zanyi tafiya,sai naga yafi kyau idan na dawo na shaida mata mu fahimci juna,to sai kuma aka samu sabanin fahimta" "Qarancin hankali da tunani dai,ita zata zauna maka da ita?,ko ita haqqin kula da ita yake kanta?,bilki....kiramin ita maza" a nutse hajiyan ta miqe ta fice zuwa dakin nafisan. Kwance take rub da ciki tana aikin kuka,tana son anwar tana tsoron rabuwa dashi,tana tsoron yaqi janye qudurinsa,don itakam ba abinda zai sata ta sauka daga kan bakanta,matsawar ta yarda ta aureshi to yaqin da tayi shekara da shekaru tana yi,kudinta data kashe,lokacinta data fansar duka sun tashi a babin badinuhu bataci riba ba kenan "Kin hadu da aiki kuma kin gama kanki da wahala wallahi,tunda kin daukama kanki aqidar banza da wofi,ki tashi kije mahaifinki nason ganinki" cewar mummy daga haka bata qara ba ta juya tayi ficewarta. Sanda ta isa falon anwar ta soma gani,kishinsa ya sake lullubeta ganin yadda kamar ma sake kyau da fresh yayi abinsa tsakanin kwanakin da ita take fama da quncin zuciya,gefan abban nata ta zauna ya dubeta "Nafi,wanne irin shashanci da sakalci kike shirin aikatawa haka?,saboda Allah ya halatta masa auren daga daya zuwa hudu saikice ba zaki aureshi ba saboda haka?,zaki sauya hukuncin Allah kenan?,koke kikayi kanki?to kar naji karna gani,banason wannan shirmen banza,yana da damarma yace biyu zaiyi kece ata uku" Kuka ta saki sosai "Abba...wallahi bazan aureshi ba,bazan iya zama dashi da wata ba"baki bude alhj abba ya watsa mata daquwa "Kinci gidanku,kajimin fitinanniyar yarinya?,to saikin aureshin naga wanda ya isa ya hana" miqewa tayi cikin kuka "Wallahi abba zan gudu,zan barku idan aka aura min shi" mummy na shirin kai mata duka saboda takaici ta fice a guje daga falon. Shuru ne ya ratsa falon,kunya da takaici na kama alhj abba da hajiya bilkisu,sai suka rasa ta inda zasu kama zancan,sunsan halin nafisa sarai sai addu'a,karta aikata wani abu da zai zama musu illa nan gaba,anwar ya fahimci shurunsu saboda haka yace "Alhj,karka damu,Dukkaninmu ni da kai da mummy bamu da ikon da zamu sauya mata ra'ayi,sannan duk yadda mukaso abin itace zata zauna,dole saida gamsuwarta sannan komai zai tafi yadda ake buqata"ajiyar zuciya suka saki dukansu kusan a tare cikin bacin rai da takaici "Yarone ka haifeshi baka haifi halinsa ba,kayi haquri anwar" cewar alhj abba yana jin babu dadi har cikin ransa,yana jin kaman ya muzanta "Haka Allah ya qaddara" anwar din ya furta kanshi a qasa,shima yana jin babu dadi saboda yadda sukejin laifin kaman a kansu yake. Tana zaune har yanzu inda ta zauna tana rusar kuka a haka mummy ta tura qofar dakin ta sameta,da hanzari ta daga kai cikin fargaba da razani tare da taraddin furucin da zai fito daga bakin mummyn,tana son anwar tana fata ace ya karbi muradinta "Shikenan ko?,burinki ya cika?,saikije ki samo wani mijin wanda yafi anwar" daga haka ta juya abinta ta fice tabar mata dakin,cikin tashin hankali ta miqe kaman zata bi bayan mommy don samun qarin bayani,sai kuma ta dawo da baya qwaqwalwarta na gaya mata ma'anar maganar mummyn,anwar ya barta?,anwar ya zabi shahida akanta?,wahalarta ta tashi a banza kenan?,kai ta shiga girgizawa tana fadin bazaiyiwu ba,ta dauki wayarta ta soma kiran layin mima ba qaqqautawa don tana da buqatarta a yau fiye da kullum,saidai amsar dai daya ce wayar a kashe take. A qalla ta kwashi awa kusan biyu a haka,bata da wata mafita ayanzu banda ta kira anwar,ta soma laluben number dinsa ta kira. Fitowarsa kenan daga kitchen dauke da cup na coffe wanda ya shiga ya hada da kansa,cikin mamaki yake duban mai kiran,saiya samu daya daga cikin kujerun falon ya zauna yana amsa wayar "Ni zaka yiwa haka anwar?,ni nafisa zaka gujewa saboda wata banzar shahida da bata kama qafata wajen qaunarka ba?,idan baki sani ba bari yau na fada maka,ni nafisa nice silar duk wani arzqinka,nice silar duk
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96