Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,296 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

qaramin lokaci,banda anty hasanan duk duniya baiga wanda zai tsaya ya soko masa zancanta ba tare daya kauda shi daga gabanshi ba "Ka taba kwanciya dai dai da rana daya ka tariyo alkhairanta a gareka?,ka taba xama ka banbance aya da tsakuwa kuwa?" Kalamanta na masa wani irin suya ne a qirji bashi da jarumatar ci gaba da sauraronta saboda haka ya qarasa ficewa cikin sassarfa daga falon,ya fada motarshi ya tashe da gaggawa ya fice daga gidan. Ta jima tsaye a wajen,dukkan wata laka ta jikinta tayi sanyi qalau,wannan wanne irin abune?,ko a mafarko ba wanda ya taba tunanin wannan kyakkyawar alaqa tarayya da abota zata juye watan watarana ta zama irin haka,jikinta ba qwari ta koma ciki ta samu d'aya daga cikin kujerun falon ta zauna tana tuna wasu daga abubuwan da suka shude cikin rayuwar muhammad da rahama. "Ita ta rusa dukkan komai,ita ta kawo dukkan wata damuwa da baqinciki da nake kwana nake tashi da ita,ita ta butulcewa ni'imar Allah ta wulaqanta rayuwar da Allah yayi mata baiwarta" kalaman daya dinga fada kenan a sandaya samu qasan daya daga cikin bishiyoyin dake jere reras a harabar kamfanin ya faka motarsa,ya kashe wajen awa guda cur yana ciki yana qoqarin controlling kansa,yana ganin wayoyin jama'ar da suke da appointment dashi amma ya kasa daga ko guda daya,baisan me yasa yake iya dealing da duk wani daya tunkaroshi ba cikin qanqanin lokaci,amma akan wannan sabgar har yau ya kasa maida kansa jarumi,ya kasa daina jin ciwon dukkan abubuwan da suka jima da shudewq,ya kasa daina jin tsanarta,ya kasa tsayawa yayi mata adalcin dako yaushe antyn da zuciyarsa ke qoqarin gaya masa yayi mata. Sai daya shafe awanni biyu sannan ya iya fitowa bayan ya rufe motar,ya dinga takawa ahankali zuwa babban ginin kamfanin daya mamaye iya kallon mai kallo,sauran mutane dake dakon jiranshi suka yo masa caa,yayi qoqarin ganin ya dawo da mode dinsa duk da yadda yake jin kwanyarsa a birkice. Tsaki taja bayan ta kammala karanta saqon,kafin daga bisani ta cilla wayar gefanta,dawowarta kenan daga makaranta a matuqar gajiya ta zauna a falon,bata ma kai ga qarasawa dakinta ba saboda gajiya,gaba d'aya ta gundura da wannan d'an banzan shirye shirye da hukumar makarantarsu keyi na zuwa shugabanta,wanda ita a ganinta ko president ne zai kawo musu ziyara iyaka kenan,ta k'agu yazo ya tafi a wuce wajen,saiga saqon nuraddeen kuma wanda ta tsani gani kamar yadda ta tsani mutuwarta,batasan sai yaushe zai gaji da halin shakulaton b'angaron da take yi dashi yayi zuciya ya barta ta rayu ita d'aya ba kamar yadda ta sama ranta. Sun riga sunyi waya da anty zubaida tasan ta fita yau bata nan,don haka girkin gidan na yau na wuyanta,ga huda da suka dawo tare tasan yunwa takeji,don ma ta siya mata cake da lemo a makaranta kafin su iso gida. D'aki ta shiga ta tube ta fada wanka,bayan ta fito ta sanya huda itama ta shiga tayi don yau babu islamiyya,a gurguje ta shirya tayi sallar azahar sannan ta shiga kitchen. Indomie ta soma dora musu sannan ta dora girki a dayan wajen "Anty kin gama?" Huda data shigo yanzu ta fada tana qarasowa inda shahida ke zaune sosai qasan kitchen din tana gyara kayan miya,don ta duba nasu markadadden da suke ajewa ya qare "Sauran kadan hudallah....dadina dake bakya juriyar yunwa" "Anty yunwa bata da hankali,haka d'an almajiri fa yake cewa" murmushi shahida tayi wanda ya qara kyawun fuskarta,hakanan ya bayyana wushiryarta,kafin tace wani abu hudan ta sake cewa "Anty...dama d'an wake kika yi mana,inason d'an wake" a hankali ta juya ta dubi yarinyar saboda tuna mata wani abu da tayi,yana matuqar son d'an wake a rayuwarshi,a duk sanda taga abincin ko taji an ambaceshi saita tuna dashi.*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH)KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don samun shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi* https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *AA* 0️⃣4️⃣ Kasa cewa komai tayi,maganar hudan ta cillata tunanin wata duniya can baya,wanda duk yadda takai ga hana kanta batasan sanda ta fada ba. Sai data sallami huda sannan taci gaba da sabgar girkinta,batasan me yasa ba sam batajin yunwa,ko zancan da huda tayi ne ya cushe mata cikinta gaba daya ya sanya har walwalarta ta ragu. Tana tsaka da kwashe abincin cikin coolers huda ta shigo da sauri hannunta dauke da wayar shahida tana fadin "Anty ana kiranki,zata katse" ta fada tana miqa mata,bata amsa ba ta kalli screen din wayar dake hannun huda,nuraddeen ne,saita dauke kai taci gaba da juye abincin tana cewa "Ajiyeta kawai huda,aiki nake" juyawa yarinyar tayi ta fice da wayar zuwa falo da gudu don kada cartoon din da take kallo ya wuceta. Tana cikin kintsa wajen sallamar anty zubaida ta karade falon sannan ta taddata cikin kitchen din "Sannu da dawowa maman huda" "Yauwa sannunki shahida,kin ganni sai yanzu ko?,wallahi layi yau na samu....me aka dafa mana ne yau da yunwa na dawo" nuni shahida tayi mata da food flask din dake jere a wajen,ta qarasa tana budawa "Hmmmmm,kice yau na musamman ne abincin,bari wannan sai nayi wanka zan zauna sosai tukunna na kwashi dabge" qaramin murmushi shahida tayi mai fitar da d'an sauti tana duban anty zubaidan,har takai bakin qofa ta dawo "Au....ni kuwa kinsan nuradden na qofar gida zaune cikin mota yana jiranki?" Asanyaye ta daga kai ta dubi anty zubaidan,sai ta sadda kanta tana goge plates din data wanke zata jerasu a muhallinsu,hakan da tayi shi ya tabbatarwa anty zubaida ya kira bata daga ba kenan "Shahida.....wannan wacce irin rayuwa ce kika daukarma ranki?,mai sonka fa ya wuce ka wulqantashi,laifin wani dama yana shafar wani?" Shuru ta sake zabar tayi,saboda tana ganin sun gaza fahimtarta ne gaba daya,ta yiwa soyayya hidima,ta yiwa soyayya halacci,ta yiwa soyayya dukkan wata kara da alkunya,qarshe data tashi ita mai ta bata?,data tashi da wanne sakamako tazo mata?,sunfi kowa sani saboda haka sunfi kowa amsar dukka tambayoyinta,ko daya bata tsinci komai cikin soyayya ba face tsantsar butulci mummunan sakamako da kuma mummunar makoma,shin ta yiwa kanta a dalci kenan idan ta sake cusa kanta a wannan bigiren? "Nidai ya roqeni alfarma,saboda haka idan na isa dake ki leqa ko gaisawa ne kuyi" zancan anty zubaida ya katse tunaninta,daga haka bata sake cewa komai ba ta ida ficewa daga kitchen din,tana jinta sanda ta kira huda suka haye sama tare,tasan kuma tayi hakanne don sanin halinta,ba qaramin aikinta bane ta fita ta baro masa huda ta cikashi da surutu wanda idan ya gaji da zama yake sallamar huda shima ya wuce nashi guri. Anty zubaidan tafi qarfin komai a wajenta,don haka ta dauraye hannayenta ta wuce dakinta,ta zari hijabi ta saka ta sanya slipper dinta ta wuce qofar gidan. Kamar kowanne lokaci yana zaune cikin motar,bayanshi jingine da seat din kujerar dayake kai,da alama ya jima zaune a wajen,duk da haka ganin fitowarta bai hanashi miqewa ba yana sakar mata murmushi harta qaraso "Barka na tunda na samu kin fito" ya fada tamkar wanda baiyi zaman jiranta ba "Inda kayi aiki da shawarata tun a karon farko da duk bamu kawo wannan matsayin da muke kai yanzu ba" ta fada kanta tsaye tana dubanshi,kafin daga bisani ta janye idanunta,har ga

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});