Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,299 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGπŸ™πŸ½* πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *AA* 0️⃣6️⃣ Saida gari ya danyi duhu kadan sannan ya dawo cikin gidan,ya duba garinsa yayi laushi,ya zuba suger dai dai gwargwado ya zauna gefan 'yar katifarsa ya soma sha,inda ya kunna redio da wayarsa qarama keypad samfutin tecno yana sauraren labarai. Kafin ya kammala an kirayi isha'i,sake miqewa yayi ya fice zuwa masallaci,don sam baya wasa da sallar cikin jam'i,koda aka idar nan majalisar dake kusa da gidanshi yadan xauna aka taba hira,bai jima can da yawa yayi sallama dasu,kasancewar yana da masaniyar gobe yana da lacture ta qarfe tara,kuma dama bai fiya zama cikinsu ba ba dabi'arsa bace wannan,hakan yasanya wasu kejin haushinsa tare da yi masa kallon mai girman kai,yakan zauna lokaci zuwa lokaci saboda kauda wannan zargin daga ransu,bugu da qari ya sani dole kuwa ya fita tun bakwai,don kuwa da qafarshi yake takawa har zuwa makarantar,zuwanshi mota a abun hawa abune mai matuqar sa'a,imma wani aikin qarfin ya samu yayi ya samu kudi,ko idan anty usaina ta d'anyi samuwa ta kirashi ta bashi wani abun,ko Allah ya hadashi da d'aya daga cikin 'yan makarantarsu ya rage masa hanya. Allah ya taimakeshi yau cikinsu ba wanda ya shigo masa gida,saboda haka ya kulle ko ina yayi nafilfilunsa kamar yadda ya saba,ya roqawa iyayensa da 'yan uwanshi gafara sannan ya kwanta bayan ya sake kunna rediyon yana sauraren shirye shiryen da sukeyi. Sannu a hankali tunaninta ya kutso cikin kaiwa da kawowar da qwaqwalwarsa keyi tun dazu,ya dan saki murmushi yana wassafo kamanninta,yanayinta tsarinta da tafiyarta,da ganinta zatayi hankali,da ganinta akwai nutsuwa tattare da ita,da ganinta ba maison hayaniya bace "Duk taya akayi kasan hakan?" Ya tambayi kansa da kansa,saiya sakarwa kansa murmushi yana girgixa kai gami da runtse idanunsa,shima baisan ya akayi ya tsinci kansa da fadawa wannan bigiren ba,saiya juya zuwa daya barin yana son maoda hankalinsa kan programe din da ake gudanarwa a gidan redio a sannan. Tun bayan sallar magariba ummantata keta sintirin aiken qannen nata kan ta fito taci abinci,saidai sam ta qiya,tayi kwanciyarta abinta,ranta ne kawai ke mata suya,a duk sanda irin wannan balahirar ta faru a gidansu idan da safe ne wuni take cikin qunci da damuwa,hakanan idan da yammaci ne koda dare kwana take cikin qunci shima da damuwa,wani lokacin takance inama kurma Allah ya halicceta?,inama makauniya ce ita ta huta da ganin wannan baqon lamari,wanda ya zama tambarin gidansu,ya kuma zama abinda jama'ar unguwa ke goranta musu dashi,don babu wanda baisan irin rayuwar da ake tsakanin uammansu da babansu ba,tayi kuka har sau babu adadi,tabi hanyoyin gyara bila adadin amma babu alamun ma sauyi bare akai ga gyaran gaba daya,tayi tunani iri daban daban masu kyau da marasa kyau amma bata samu hanya mai bullewa ba,tayi yaji tabar gidan batasan adadin sau nawa ba amma sun bita sun dawo da ita kan alqawarin komai ya wuce zasu gyara amma babu alamun sauyawar lamuran,ta tambayesu me yasa suke hakan amma su kansu basu san amsa ba,abu d'aya ta sani shine,dukkaninsu tsakanin ummanta da babanta babu wani mai haquri acikinsu,ummanta bata da haquri ko kad'an kamar yadda mahaifinta yake,bata raga masa ko daya,idan ya mata taga bai mata dai dai ba take zata rama,shi kuma yaga ta rainashi kenan haka zai biye mata suyita yi. Basu san ciwon da hakan ke mata a qirjinta ba,basu san illar dahakan ke haifarwa ga tarbiyya yara da tunaninsu da ginuwar hankalinsu,iyayenka a wannan bigiren na fada da juna kulli yaumin har sauran jama'a su shaida hakan kai me yayi saura a rayuwarka?. Saida umman taga da gaske take bazataci abincin ba kamar yadda ta saba a duk sanda ta samesu suna cecekuceb da suka saba,saita dire faruqu ta nufi dakin nata,ta yaye labulen tana tsaye daga dokin qofa tace "Tunda sai abinda kikaga dama zakiyi bismillah,dadin abun cikinki ne ba nawa ba,yunwa kuwa dai dai take dake matsalarki ce wannan,ki tashi ki gayamin ya akayi sauran botikaina sabbi suka fashe haka?" Da qyar ta juya daga kwancen da take ta d'aga kai ta dubeta "Wasune garin wawaso suka fasa su" "Botikan duka?" Kai ta gyada mata "K'nnnn,ai shikenan,Allah ya kyauta" ta fada tana sakin labulen,maida kanta tayi ta kwantar,inama ace haka takewa mahaifinsu a duk sanda wani abu ya hadosu?,ta tabbatar da shine tsautsayi irin haka ya faru da yau Allah ne kadai yasan qarshen fadansu. Mubina ce ta shigo da kwananon abincin ta dire mata ta juya ta fice,bata dai kallesu ba tana ci gaba da kwanciyar "Idan baki tashi kin kama abinci kinci ba na shigo sai nayi mugun saba miki" ta jiyo muryar umman daga tsakar gida tana gaya mata,hakanan badon son ranta ba ta sauko ta tanqwashe qafa ta dinga cusa abincin har sai dataji kaman zatayi amai sannan ta maida murfin ta rufe ta sake kwanciya. Runtse idanunta tayi tana fatar bacci ya dauketa,sai taga wata fuska data sanyata saurin sake bude idanunta,dawo mata yayi tar a kwanyarta,bacin ran da take ciki yasa bata sake tunowa dashi ba sai yanzu,saita gyara kwanciyarta tana kallon bango,ta dinga tuno fuskarsa da yadda tafiyarsu ta kasance daga bakin masallaci har zuwa gida,hakanan taji nauyi da bacin ran zuciyarta ya ragu sosai,ta shagala da tunanin daya d'auketa zuwa bacci mai nauyi. Qarfe biyu na rana gaba ya tsinci kansa hankalinsa ya tafi bakin masallaci gurin da ba wajen zuwansa bane idan ba shagin balarabe zashi ba ko wani babban uzurin ya kamashi na zuwa wajen,sai ya sake tsintar kansa da sake yin wanka bayan ya gama hutawa duk da kusan dabi'arsa ce a duk sanda ya dawo daga makaranta,amma wannan karon saiya laluba kayanshi har ya zaro zai saka ya maida ya sauya wasu,abinda bai taba yi ba,bai taba damuwa da suturar da zai saka,kawai dai yasan dukka kayan sawarshi a tsaftace suke kullum,hakanan basa rabo da guga,duk da cewa ba wasu masu shegen kyau da tsada bane,Allah dai yayi masa wata baiwa ta duk kayan daya saka jikinsa na dauka,hakan yasa matasan anguwar da dama ya tsone musu ido,wanda yawancinsu dukka sunfishi gata rufin asiri da komai da komai,tsaftarsa tasa baka gane kaashinsa. "Ki kulamin da botikai na,karki sake bari su fasamim botiki,kai jamilu idan ka aje mata ka dawo ka kaimin shara" cewar ummanta wadda take rufe botikin abincin data gama zubawa almajirin ya qaraso wajen ya dora a kanshi suka fice tanawa umman sallama. Har sunje soron gidan hakanan taja ta tsaya,saita juya da hanzari ta koma ciki "A'ah,lafiyarki kuwa?" Umman tata da taga wucewarta ciki ta fada "Lafiya umma ina zuwa" kai tsaye ta dauko dan kwandon kayan kwalliyarta dake saman akwatin kayanta,ta ciro ruwan madubi mai fadi dake soke a ciki ta kalli fuskarta "Hoda na miki kyau wallahi shahida,don Allah ki dinga d'an shafawa mana" ta tuna maganar da qawarta ta gaya mata daxu a makarantar boko,saita samu kanta da ciro hodar ta bude ta shafa,data sake kallon fuskarta sai taga ta canza din kuwa,sosai hodar tayi mata kyau ta sake fidda kyau da qyallin fuskarta,murmushi ta saki ta aje mudubin ta juya ta fice da sauri. Yana zaune daga shagon balarabe yana kallon duk wani motsinta dake bayyanar da hankali da nutsuwarta da kuma ainihin ita wace,duk surutu da hirar da balaraben yake masa baya gane abinda yake

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});