Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 66

Chapter 66

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,305 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

soma sauka ta gilashin motarsa,yaso ya dake yaso ya dauke kai ya saka motarsa cikin gidan anty usaina amma saiyaji kaman umarni,a zafafe yace "Oh god" yana zare belt din jikinsa,cikin zafin nama da kuma jin haushin kansa da kansa ya bude murfin motar ya fice. Yana kuzari da halittar ba daya bace,hakan ya sanya cikin qididdgaggun taku ya cimmata "Daga ina kike haka?" A nutse ta waiwayo tana dubansa sanda take gab da qarasa bakin titi,saita juya da niyyar ci gaba da takawa ba tare data amsa shi ba "Wai sanda zaki fita ma kin tambayeni ne?,saboda tsabar rinton zunubi?" Kalaman sun mata ciwo,wato tun yanzu yake nufin xai mulkata kenan?,hakan yasa ta tsaida tafiyar tata ta juyo ta dubeshi "Kai waye da don zan fita saina tambayeka?" "Kinfi kowa sanin ni waye ai ba buqatar na maimaita miki,banason dogon zance wuce muje na taimaka miki na saukeki,amma kafin sannan idan kina da niqab ki saka a fuskarki kar mutanen unguwa su ganmu tare su zaci nima dan harka ne" ya kai qarshen zancan yana dage girarsa duka biyun,wanda hakan ya masa kyau ainun duk da fuskarshi a murtuke take,sosai kalaman suka fusatata wanda hakan ya sanyata ta juyo gaba daya ta watsa masa idanunta da suka sake budewa saboda bacin rai,hakan ya tilasta masa dan qanqance nashi idanun gami da damqe hannayensa dake zube a aljihu "To hell with your taimako...Allah suturu buqui,har abada bana son taimakonka,sannan kuma aikin banza kake harara a duhu,da kake gudun kar a ganmu tare me ya kaika neman dauramin igiyarka,idan da gaske kake qyamata aiya kamata ka gujeni da gaske ta yadda ko qasa daya ba zaka hada dani ba bare inuwa daya,indai ka cika kai anwar ne ka aikata hakan" qaramin murmushi ya saki daya sake fitar da kyansa,ya dage dukka kafadunsa "Ba zaki taba samun yadda kikeso ba,niba qaramin yaro bane bare kalamanki su tunzurani nayi miki yadda kikeso,abu daya kawai na sani shine,na riga dana biya sadakinki,saboda haka ina da power a kanki ko kinqi ko kinso...saboda haka ki wuce muje" dogon tsaki taja wanda ya ratsa kunnuwansa,sannan ta watsa masa harara ta juya taci gaba da tafiya,bai fasa binta ba shima har suka isa titi. Adaidaitan farko data tsaida ya sallameshi da dubu daya yace yane abinsa,na biyu ma haka,na uku kuwa da yame dattijone yace masa baba kaje matata ce yaji takeson yi,na bata haquri taki haqura,nan yasa bawan Allahn ya tsaya yana mata nasiha,inda daga qarshe ya sallameshi da dubu uku ya amsa yana godiya,ta hudu kuwa ya samu sauayi maiji da tashen girma yaso masa gardama.kan saiya dauketa tunda itama tana son shiga "Kana sha'awar xaman gidan kaso kenan?" Harya karkata baki zai masa diban albarka saiya nutsu ya qarewa shigarsa kallo,tun daga takalminsa,kayan jikinsa zuwa agogonsa,aibabu shiri yaja abun hawansa ya fece,bacin rai ya taru ya rufeta ruf sanda ta kalli titin ta ganshi fayau ba wani sauran abun hawa na haya kuma nan kusa,ta waiwayo zata gasa masa magana ko xataji sanyi,kadan ya rage fuskarsu ta gwaru,sam batasan yana bayanta ba a tsaye,da alama kuma duk tsahon lokacin kallonta yake,baya yaja yana bata fuska "Ke baki da kunya ne?,akan titi kike neman ki rungumeni?,toki maida qwalamarki,ni ba naki bane" kawai saita fashe da kuka ba tare data shirya ba,saboda ya gama cutarta,bata ga wani kalma da zata fada masa ba wadda zata rama abinda ya gaya mata,minti biyu kacal ruwan sama ya soma sauka,ya kalli sama sannan ya kalleta "A karo na qarshe nake gaya miki ki wuce mu tafi" baya taja saman wasu tayoyi da masu faci suka tashi suka barsu a wajen ta zauna,ta gwammace ruwan yayi mata koma meye data bishi kota shiga motarshi,ganin ta zauna dafa'an ya sanyashi juyawa ya koma cikin layin don dauko motartashi zuwa nan bakin titin dukda yadda ruwa yake dukansa. Yana isowa wajen yaga tashinta cikin adaidaita sahu,qaramin murmushi ya sube masa,wato dama tana da taurin kai kenan?,saiya sake baiwa motar wuta harsai daya je daya side din na adaidaitan,ya tabbatar ta ganshi sannan ya barsu suka wuceshi,a baya yaci gaba da binsu har xuwa sanda yaga shigarta gida sannan ya karya kan motar ya koma gidan anty usaina. Sanda ta shiga gida baqinciki da takaici ya sake cikata ganin yadda gidan har baqi yadan samu,hakanan ga kayan amsar lefe a kammale gobe kawai suke jira,hasina ma ba'a barta a baya ba,ganun zata saka mata ciwon kai da tsokanarta yasa tayi zarcewarta daki ko tsayawa a wajen batayi ba bare ta zauna,gaban mudubinta ta tsaya tana kallon yadda ta jiqe gaba dayanta,haushinsa ya sake cikata,taji kaman ta sake fashewa da wani kukan,duk shi yaja mata,da ta shiga adaidatan a lokacin daya dace da duk hakan bata faru da ita ba,haka ta ringa cire kayanta daya bayan daya ta daura babban towel ta shige bandakinta ta hada ruwa mai zafi tayi wanka. https://youtu.be/alR4jOvvQUc *Alqawarin Allah* 3️⃣3️⃣ Washegari da wuri tabar gidan fiye da yadda ta saba fita,ko a kamfaninma masu gadi kawai ta taras,ta bude office dinta ta shiga ta zaun donko mai maita shara ma bata iso ba. Sanda aka tashi ta tsaya tunanin inda zata,don tasan wala'alla dai dai lokacinne ma gidan yake a cike,yankewa kawai tayi ta tafi gidan oga rayyan,ba bata lokaci ta gayawa mai adaidaitanta ya wuce can da ita. Sosai taji dadin zuwa gidan,a rayuwa gidan yana burgeta qwarai,yanayin mu'amalar jama'an gidan,nan wajen raihana ta zauna suka sha hira sosai,sai bayan sallar magariba sannan tayi haramar tafiya,nan ta cikata da turaruka tana cewa "Gashi amarya,naji oga yace kin kusa shiga daga ciki,ki fara amfani da wadan nan kafin lokacin xan kawo miki na amare" "Hmmm" kawai tace tana dan fitar da murmushin da baikai zuci ba daga fuskarta. Tun daga harabar gidan zaka san cewa ansha baqi a gidan,bata yarda tabi ta qofar falo ba saita bi ta qofar baya tayi shigewarta dakinta,kayan hannunta ta aje ta rage kayan jikinta ta shiga wanka,bayan ta fito ta murza manta mai qamshi ta saka riga mara nauyi,ta ciro wayarta daga jaka kenan taga miscal din zunnurah,sai fuskarta ta washe da fara'a,ba bata lokaci tabi kiran,bugu biyu ta daga,abu na farko data fara shine guda ta sakar mata,bacin rai ya bijirowa shahidan,wato kiranta tayi donta tsokaneta kenan?,sai kawai ta yanke kiran,ta nufi gadonta ta hau ta kwanta rub da ciki tana lumshe idanunta,dai dai nan hasina ta turo qofar "Au yaushe kika shigo?" Banza tayi da ita kamar bata ji ba,hakanan taqi bude idanunta,don tasan qarshenta itama tention xata qara mata kawai "Shahida" hasina ta sake fada tana matsowa dab da gadon,ta dora hannunta saman filon tadan daka,sai a sannan ta ware idanunta tana dubanta "Bacci nakeji,don Allah ki barni na huta" murmushi hasina ta saki "Amma na miki jaje da zaki kwana bakiga kayanki ba wallahi,kallo ya barki" qur ta mata da idanu kafin taja qaramin tsaki ta maida kanta daya barin tana rufe idanunta,dariya ta sheqe sosai da ita sannan ta juya ta fice tana waqar amarya. Da sauri ta diro daga saman gadon ta isa bakin qofar ta saka key ta kulle sannan ta sake dawowa ta kwanta,tana gyara kwanciyar tata tana mita ita daya gami da jan tsaki lokaci lokaci,rigingine ta kwanta tana kallon roofing din dakin,idanunta a

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});