Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,307 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sauri,cikin sa'a ta cimma titi kafin ya juyo ta samu abun hawa ta shige ko waiwayenshi ma batayi ba bare ta san ya iso ko bai iso ba. Tsam tayi da ranta cikin abun hawan lokacin da yake sake kusantata da ainihin unguwarsu,wadda anan komai na rayuwarta ya samo asali,a nan duk wani babu na quncinta ya bude,anan komai ya wanzu ya kuma wakana cikin shafukan rayuwarta. Tafiyar mintina talatin suka iso,ya gangara da ita cikin layinsu kamar yadda ta saba aduk lokacin da tazo unguwar tasu bata sauka a titi saita dangana da qofar gidansu,kanta ta dauke gefe guda lokacin da sukazo gifta wani katafaren gida,bata maida kanta ga kallon gabanta ba har sai da suka isa qofar gidansu,sauka tayi ta sallami mai motar tana cusa kai cikin gidan gami da yin sallama. Fakadeden tsakar gidan nasu wanda ada can zamanin quruciya takejin babu wajen daya kaishi dadin xama da dadin yin wasa,kafin wasu murd'addun al'amura su zama silar da zaman tsakar gidan ya zame mata tamkar zama kusa da ramin maciji,babu kowa a tsakar gidan saidai a share yake sarai fes cikin tsafta da kulawa,batayi mamakin ganin babu kowa din ba don tasan a irin wannan lokacin saura qannenta na islamiyya. Daga falonta ta amsa mata sallama,shahida taci gaba da takawa har zuwa qofar falon ta sabule takalmanta ta shiga tana sake maimaita sallamarta. Cikin sanyi ta amsa mata kamar kowanne lokutta,wanda hakan kusan ya zame musu jiki ita da umman tata "Yanzu kike tafe?" Umman tata ta fada cikin jin nauyin d'iyartata wanda har yau ya kasa barinta "Wallahi umma,na manta yaune ranar da nake zuwa sai wajen uku na rana na tuna" "Da kin bari sai gobe ai,tunda yamma tayi.....mubina ma ta riga da tayi wankin harsun bushe ta shanya,tunda taga rana ta soma baki zoba tace wataqila yau yaya ba zata samu zuwa ba" "Me yasa?,da ta jirani ai ina kan hanya" gaida ummantata tayi ta amsa tana tambayarta anty zubaida huda da mai gidan,ta miqa mata saqon da anty zubaidan ta bata wanda itama batasan meye a ciki ba,bayan umma ta gama godiyarta ne kuma shuru ya biyo baya,shahida ce ta dinga qoqarin sako hira jefi jefi,ko kusa a yanzu batason yadda umman take qin sakewa da ita,kaman ba ummanta ba?,komai ya canza tsakaninsu tun shekarun baya da suka shude. Qarfe biyar ta shiga kitchen ta soma dorawa ummantata abincin dare da taga tana niyyar daurawa,ita kuma tana daga tsakar gida zaune kan tabarmar da suka shimfida,duk wani motsin rahama na kan idanunta,itama rahaman ta ankara da hakan saidai ta nuna bata kula ba,irin wannan kallon umman tata ta saba binta dashi da dadewa,kallon tausayi,kallon nadama,kallon kaicon biyewa son rai da son zuciya da sukayi ita da mahaifin rahama shekarun baya da suka shude,har hakan yaso jefa diyar tasu cikin hallaka,da tuni yanzu bayan shudewar mai gidan ita daya zata ci gaba da kurbar baqinciki da bacin ran abinda suka aikatawa rayuwar rahaman. Qarfe shida qannenta nata suka shigo,ta bisu da kallo sanda suke shigowar cikin jin dadi tare da musu addu'a cikin ranta,koda yaushe tana jin dadi har cikin ranta na yadda rayuwarsu ta banbanta da tata rayuwar a sanda take da shekaru kamar nasu,kallo daya zakayi musu kasan suna samun kulawa da tarbiyyar data dace,mubina ke bin rahama(shahida),sai khadija,faruq,sajid sai qaraminsu nasir. Dukkansu fuskarsu qunshe da walwala suka iskota,ta jima cikinsu yayin da mubina ta amshi aikin girkin,tana yi suna hira da yayarta da sauran qannunta. A nan kan qatuwar tabarmar suka ci gaba da zama,suka gabatar da sallar magariba,sannan mubina ta zuba abinci cikin babban tray. Gaba dayansu kowanne ya sanya hannunshi suka soma ci,suna hira lokaci lokaci,har cikin ranta tana jin dadin kasancewa cikin 'yan uwanta,saidai wannan kallo da duba da umma ke mata tana qaunar ya gushe daga idanunta,ta manta da faruwar komai,ya zama tarihi kamar ma bai taba faruwa ba. Sallamar usman d'an maqotansu shi ya katse hirar tasu,ya gaida ummansu sannan yace "Ana sallama da anty shahida" hada idanu sukayi da umman,yayin da kowa abinda ke yawo a zuciyarsa ya tashi daban da na d'an uwanshi,qas da kanta shahida tayi tana kokawar hadiye lomar tuwon data riga ta saka abakinta,batakai ga hadiyewa ba saqon usman ya shiga kunnenta,sai taji gaba daya abincin bai mata dadi a bakinta,ya kuma gagara wucewar,hakan ya sanya ta miqe tsam ta isa bakin rariyarsu ta zubda tuwon sannan ta wuce dakin umman ba tare data bi takan aiken da akayo mata ba. Suya kawai qirjinta yake,waye wannan yakeson mata kutse ne cikin rayuwarta a sanda bata shiryawa hakan ba?,waye shi da zai tunkari rayuwarta a sanda bata da dukkan wani tsari akan kowanne d'a namiji?. Shigowar umma dakin shiya katse mata tunaninta,ta yunqura ta miqe ta zauna sosai daga kasalalliyar kwanciyar da tayi,wani mummunan tashin hankali ya ziyarceta sanda ta dubi idanun umman taga hawaye na biyo kuncinta,cikin matuqar rudewa da gigita tace "Um....umma...hawaye fa kike umma meya sameki?,don Allah kibar kukan,kiyi shuru kice wani abu" "Dole nayi kuka shahida....bazan daina kuka ba harsai sanda abinda yake damuna ya gushe,tashin hankalin da kika shiga kadai sanda aka aiko kiranki ya tabbatarmin akwai sauran rina akaba,kuma hakan ke nunamin cewa dafin da muka zuba a zuciyarki har yau bai gama wankewa ba" zamowa tayi daga saman kujerar tayi gurfane a gaban umman tata itama hawaye na sakko mata cikin tashin hankali "Ko kad'an umma,kufa iyayena ne,kune kukayi silar zuwana duniya,umma....ba tun yauba na gayamiki ki goge duk wani abu daya faru daga ranki,ki daina alaqanta duk wani yanayi da zaki gani tattare dani da cewa laifinku ne" "Indai kinason hakan ta faru shahida ki koma yadda kike....ki amshi wani cikin masu sonki kiyi aure,anwar bashi kadai bane namiji da don ya miki wani abu zai zama silar da zaki maida kanki wata aba daban ba,indai ina ci gaba da ganinki a haka baki sauraren kowa bare akai ga batun aure bazan daina zargar kaina ba har na koma ga mahaliccina,kamar yadda mahaifinki bai daina zargin kanshi ba har ya koma ga mahaliccin......" Maganar tata saita riqe,kuka sosai ya qwace mata,tana tuna abubuwa marasa dadi da suka faru a rayuwarsu,tana tuna komai tar cikin kwanyarta,qaruwar kukanta ya qara dasa tashin hankali a zuciyar shahida,wadda ta miqe ta figi mayafinta cikin rawar murya tace "Zanje,zan fita umma indai hakan shi zai sanya farinciki da walwala a cikin zuciyarki" bata qara second guda ba tayi waje,kai tsaye kuma ba tare da saurarar komai ba ta wuce zuwa qofar gidansu.*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER* 07067124863 *KO KUMA* 09032345899 *ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sabbabi,karku manta ky danna SUBSCRIBE,kuyi LIKE sannan kuyi SHARINGπŸ™πŸ½* πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½πŸ‘‡πŸ½ https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos 0️⃣3️⃣ Jingine yake jikin motarsa ya qurawa qofar gidan idanu,ji yake kaman ya shiga ya fito da ita,ganin fitowarta ya sanyashi kasa tsaiwa jikin motarsa kamar yadda yake tsaye a dazun,sai ya tsaya qyam yana dubanta,ji yake tamkar an masa rahama,shi kadai yasan yadda yake jinta cikin jiki da ruhinsa,wani irin so yakewa shahidan,kamar ya rufe ido ya bude ya ganta cikin gidansa,ta zama matarsa kuma mallakinsa. "Barka da fitowa,Allah yasa ban takura ki ba" ya fada yana sakin murmushi,duk da

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});