Chapter 68
Chapter 68
kitchen din tana duban agogo,tasan zuwa sanda zata gama hudu tayi saita da alwala kawai gaba daya. Miyar na soyuwa haidar ya shigo yana shaida mata tazo inji anty zubaida,saita rage wutar can qasa yadda ba zata kama ba kafin ta dawo ta fito zuwa falon,a zaune ta sameta da tulin kaya a gaba da alama sabbabi dinkuna ne tana dagawa tana kalla gami da ware wasu gefe "Kije waje kinyi baqo"gabanta yadan fadi,tadan bata fuska " waye haka da la'asar din na" "Ban sani ba nima,idan kinje zaki gani" hakan yadan kwantar mata da hankali jin ba wanda ta tsani ganin bane,nan kan kujera ta dauki mayafinta data dawo dazu dashi ta yafa sannan ta fice. Matashin saurayine mai kyau da aji tsaye jikin motarsa,sanye yake da shadda riga da wando dinkin tazarce,hankalinsa duka nakan wayarshi a haka ta kusa cimmasa,bata sanshi ba amma sai take ganin tasan fuskar a wani waje daban ko can da dadewa,sallama ta masa ganin baisan da isowarta ba,ya daga kai da hanzari yana amsawa fuskarsa ta fadada da fara'a "Barkanki da yamma kin wuni lpy" "Lafiya alhmdlh" ta amsashi a taqaice "Ya mutanen gidan kowa da kowa lafiya?" "Lafiya qalau" ta sake amsawa tana mamaki ina ya santa tare da zurfafa tunaninta ko zata iya tuna a inda ta sanshi,murmushi ya saki "Nasan baki sanni ba,ni sunana muhsin,aboki kuma aminin anwar" lokaci daya maganar ta sauka a zuciyarta,sai yanayin fuskarta ya soma sauyawa,fuskarta ta soma tsukewa,duk da haka tadan dake hadi da qoqarin sassautawa,shima dubanta yake yana karantar sauyawar yanayinta lokaci kadan,bai sake cewa komai ba ya bude murfin motar da yake jingine a jiki ya zura hannu ya ciro wata babbar envalope da qarama ya miqa mata,kallon envalope din tayi sannan ta dawo da kallonta kanshi alamun neman ba'asi "Katin gayyata ne na dinner ko zaki gayyaci qawayenki,wannan kuma kudine ko zaki buqaci wani abu" kai ta girgiza tana danja baya,a fuska tana ganin mutuncinsa amma baya ga haka so take taci masa mutunci ne shida wanda ya aikoshin,amma duk da haka ba zata kasa bashi saqo ba "Ka maida masa dukkan kayansa,ka gaya masa aurensa baya buqatar wani shiri tunda a shiryensa aka qulla shi,kudi kuwa baiyi kudin bani ba a yanzu har zuwa nan gaba,ka gaida na gode" daga haka ta juya zuwa cikin gidan tana takawa a nutse,da kallo ya bita qwaqwalwarsa cunkushe da tunani da mamaki,kullum kwanan duniya sake mamaki yake kan meye haka mai girma daya raba kwanunansu ya tarwatsasu haka zuwa pieces suka kasa kuma daidaita tsahon shekarun?,amsar daya kasa samunta kenan haryau daga wajen anwar duk da sanda rabuwar ta afku shine mutum na farko daya sha wuya da anwar din kafin rayuwarshi ta daidaita,saiya xagaya ya bude murfin motar tasa ya shiga yana tuna yadda sukayi da anwar sanda zai ya shirya kudin da katin yace zai kaimata da sunanshi,har kusan haurawa sukayi kan koda zaikai din yakai amma bada sunanshi ba. Iska ya furzar daga bakinsa lokacin da muhsin ke zaune kan daya daga cikin kujerun office din yana sake tambayarsa wanne laifi ya aikatawa shahida haka?,ya dubi envalope din daya fita dasu ya dawo dasu kamar yadda suke,hakan na nufin bata karba ba kenan "Bata karbi kayan daka kai din ba kenan?" Anwar ya tambayi muhsin kai tsaye yana dubanshi,kai ya kada "Ni duk ba wannan na tambayeka ba,inason gyara wannan barakar ne shi yafi damuna,banason alaqar taci gaba da tafiya a haka" "Me ta gaya maka sanda kaje?" Ya sake jeho masa tambaya ba tare daya damu da nashi bayanan ba "Batace komai ba" murmushin yaqe ya saki,takowa yayi kusa dashi kujerar dake fuskantarsa ya zauna "Ta fadi maganganu a kaina,takuma ce ba zata karba bata buqata right?" Idanunsa cikin na muhsin ya fada,kauda idonsa muhsin yayi saboda shi kansa wasu lokutan anwar na masa kwarjini da yawa "Kaga malam nidai bance maka haka ba,banason tone tone" miqewa yayi yana jijjiga kai "Ta fada,na santa kamar yunwar cikina" gaban envalope din ya qarasa,ya farke dayar ya cire kudaden ciki ya janyo locker din office din nasa ya zubasu ciki,sannan ya janyo daya locker ya ciro wasu ya musanyasu dasu ya maidata ya manne muhsin na kallonsa,ya kwashesu duka ya aje masa key saman teburinsa "Idan ka gama ka rufe ko ina" daga haka ya juya yana takawa sannu sannu zai fice daga office din "Wait mana malam,ina zaka je?" Murmushi ya jefa masa ya fita ba tare daya amsashi ba. Gidansa ya soma isa ya bude sashensa ya shiga,ya aje kayan hannunsa,bandaki ya shiga ya tara ruwan wanka mai dumi ya sake wanka sannan ya nemi abinci yaci ya qoshi,wardrobe dinsa ya bude ya zabi kayan da yaje gani sun dace da irin wannan lokacin ya sanya,ya tsaya gaban mudubi yana taje kansa gami da kallon kansa yadda kayan suka amsheshi,tuna abinda ya faru tsakaninta da muhsin yayi,saki yaja,wato ita mai taurin kai ko?,har yau bata kallon laifinta sai wani take dorawa alhakin faruwar komai ba tare data duba nata laifin ba,aikawa yaso yi direct inda dole ta karba saqon,amma hkanan yaji yana son yaje yaga hawayenta ya takaleta ya kuma tsone zuciyarta,saiya aje cumb din yana daura agogon fata sannan ya zauna ya daura takalmansa ya feshe jikinsa da turare ya dauki key din motarsa ya fito. A hankali yake tafiyar kaman bazaije ba,karon farko da zai fara zuwa gidan anty zubaida kenan,yadan yi nauyi a hanya hakan yasa bai isa ba sai qarfe shida mintina hamsin suka rage kenan a yi sallar magarib. Maigadin gidan anty zubaida ne ya iso ya bashi hannu don suyi musabaha,cikin tantama yadanyi jim don yana ganin bai kamata suyi hannu da hannu ba "Mu gaisa mana abokina,bakason ladar ne" da sauri ya miqa masa suka gaisa "Inason magana da wata yarinya shahida a gidan nan ne" cikin washe baki yace "Au,kaddai kaine angon?" Murmushi kawai yayi sannan ya sake cewa "Idan ka shiga matar gidan zaka sanarwa zuwa na,sannan ka turomin faruqu ko haidar" "Toh...toh" ya fada yana juyawa zuwa ciki. Sanda saqon kiran ya sameta tana daki tana shiryawa bayan ta gama mitar wankan turaren da anty zubaida ta kafa nata dokarshi,turaren na nata dadi da qamshi amma tuna dalilin yinsa ke qona mata rai da dagula mata lissafi,tsaki taja sanda huda ta gaya mata ana kiranta,ta shiga mita "Wai wanne irin kirane da baqi haka tun dazu ba za'a bar mutum ya huta ba?,haka kawai kana zaman zamanka daada ta tada zaune tsaye cak,ni wallahi na gaji da wadan nan abubuwan,daga wannan sai wancan?" A haka ta shirya ta zari hijabi ta fito "Baqon na waje ai" anty zubaida tace da ita sanda taga ta tsaya ta mata turus,haka ta juya ta fita kaman zata fashe. Faruq ta soma hangowa cikin dakin saukar baqi na gidan baki na motsi da alama hira yake zubawa,harara ta zabga masa duk da bai ganta ba,a haka ta isa ta yaye labulen,tare idanunsu suka sauka cikin na juna,yawun bakinta ya tsaya kowannensu na kallon dan uwanshi ba tare daya dauke ido ba,gani yayi kamar ba ita,fatarta ta sake sauyawa kyanta kaman an matso shi,qamshinta ya soma cika wajen,shima kwarjini taga yayi mata,shigar ta amsheshi,yayi kyau ya sake zama cikakken mutum da hankali da ilimi suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96