Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 19

Chapter 19

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,295 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kashewa ne,sannan ta cire wani abu a ciki tace wannan ya kaiwa anty usaina ita yafi cancanta ta sanya albarka,next month kuma idan ya sake amsa to ya fara ajiya saboda lalurorin yau da kullum,duk sai data gama kasafin ya cakude kudaden waje daya sannan yace "Qurun qus kin gama tatsuniyar taki?,toni ba haka nakeso ayi ba,da safe me mike ci idan zaki makaranta?"baki tadan cuno "Kome meye ya samu" "Good" ya fada yana cire wasu kudi ya aje "Indomie da qwai nakeson ki koma ci" idanu ta zaro tana kallonshi baki bude "Honey...me kake fada ne?" "Abunda kunnuwanki suka jiyr miki.....wannan kuma kudin kashewarki na wata gud....." "Kaga...don Allah ka tsaya ka daina wannan lissafin mana" nan sa'insa ta kaure tsakaninsu,da qyar ya yadda da nata lissafin bayan ta masa alqawarin wata na gaba ta yadda za'a sata cikin kasafin,saidai duk da haka yayi cancel kudin kashewarsa ya bata dole ta amsa saboda ya kafa mata sharadi. Koda ya kaiwa anty usaina ma itama cewa tayi ba zata soma amsa yanzu ba,ya aje wajensa zata masa magana idan lokacin daya dace yayi,haka ya dawo dasu ya miqawa shahida "Shikenan...zan saya banki na dinga tara maka,duk sanda kake da buqata saika amsa" washegari kuwa ta sayi bankin ta zuba masa harda kudin daya bata,ta nuna masa sannan ta roqeshi "Don qaunar da kakemin kada kace a'ah,za'a tara ne ka siya abun hawa ko keke ne,ko baka fadimin ba nasan tafiyar qafa kake" da qyar ya amince da shawararta,donshi a son ranta tayi hidimar gabanta kawai dasu. Wata hudu cif da fara aikinsa komai ya soma tafiya babu laifi,ta wanni fannin abubuwa da dama sun soma sauqi,cikin godiyar Allah da yadda da cewa komai lokaci ne. Cikin haka aka fitar da ankon bikin umaima,wadda take cousin ce a wajenta,ranar data kawo musu ankon wuni tayi a gidansu,har dare tana nan,sanda ta tashi tafiya anwar yazo shahidan na wajensa,mubina ce ta rakota tana nanata mata idan ta tashi dawowa ta kawo mata alawarta,qarasawa tayi wajensu shahidan tana mata sallama daga bisani tace "Ina zuba ido saikinzo siyan ankon,kuma wlh baki isa ba ba wani daya da zaki duka biyun zakiyi" "To ummata" ta fada tana hararta,don batason ta tada zancan a gaban anwar din,sun riga da sun gama maganar su tun cikin gida,da haka sukayi sallama umaima ta wuce. "Wai ina bankin nan kuwa?" "Yana cikin gida" "Idan yana kusa daukomin shi idan yana kusa" bata ce komai ba ta shige gidan ta fito dashi,bankin qasa ne ya amsa saiya sakeshi ya fadi take ya fashe kudin ciki ya bayyana,baki ta bude tana zaton itace bata bashi dai dai ba ya riqe ya fadi haka,sai taji yace "Yauwa yayi dai dai,tayani qirgawa" cikin mamaki ta duqa ta soma tayashi hada kudin,bayan sun gama hadawa ya miqa mata yace ta irga,cikin murna da mamaki tace "Da gaske ne kudi wawayene....ban zaci zasu kai haka ba wallahi" murmushi shima ya saki,walwalar da take kawai ta isheshi farinciki "Kije ki sayi ankon ko kala nawa ne,saura kiyi dinki,idan ba zasu isa ba kiyimin magana" ranta ta ba'ta sannan tace "Me kake fada ne?,kudin keken naka zaka bani kace nayi anko bayan sunkai kudin keke sabo harda canji?,kuma ma tuni umma tace zatamin daya abba guda daya" "Duk bansan wannan ba....abinda kawai na sani shahidana zata saka kaya kamar yadda kowacce mace zata saka...kada kice zakimin musu indai baso kike raina ya baci" kaita duqar "Allah ya baka haquri" dole ta fidda kudin ta sayi ankon kala biyu mayafi da abun daurawa,cikin sati uku suka shiga hidimar biki amma hakan bai hanata ganin anwar ba,shima hakan ya masa dama tunaninsa rashin ganinta. Ranar da za'ayi dinner tun safe suna gidan kwalliya,qarfe biyar da rabi na yammaci ya kirata yazo ganinta tana ina,itama yana ranta don jiya basu samu ganin juna ba basa unguwar kwata kwata suna can aikin snacks,ta kwatanta masa gidan kwalliyar,ya gane gidan saboda cikin anguwarsu ne. Sanda ya iso tuni an gama mata tata,zata wuce kuma gidan bikin ta saka kayanta kafin a soma dibansu zuwa wajen da za'a gudanar da shagalin. Dan kwalinta a hannu ta fito soron gidan don kada ya bata mata kwalliyarta,dubansa tayi yadda yayi mata kyau cikin wani sabon yadi blue black,wanda aka yiwa dinki irin na matasan zamani,bata mancewa da ita yayi shawara kafin ya sayi yadin ta kuma zabar masa dinkin qarshen wata sanda aka biya salary ya cira a ciki yayi,anwar nada wata baiwa ta daban,idan yayi dressing kai kace shi din wani ne,daga kai yayi daga danna wayarsa da yake yana dubanta,subhanallah ya fada a sarari,wani azababben kyau yaga ta qara masa,kai kace ba shahidarsa bace,sai yayi sak yana ci gaba da dubanta,abun ba qaramin dariya ya baiwa shahida ba har sai data d'an dara "Yaya anwar wucewa zanyi fa ana jirana.....tun daxun kake kallona sannan kuma kai baka ce komai ba" ta fada a shagwabe tana langabe wuya,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dubeta "Ba inda zan barki ki fita a haka shahida....gaskiya zuciyata ba zata iya jurewa wasu su kalleki a haka ba a filin Allah wajen bikin dake cakude da maza da mata" "To a yaya kakeso na fita?" Ta fada tana cuno baki wanda hakan ya sake tafiya da imaninsa,dan qaramin bakinta mai dauke da pink din labba yasha maroon din jambaki "Mafita kawai ki wanke fuskarki" idanu ta zaro tana dubanshi "Haba yaa anwar....haba don Allah" ta fada kaman zatayi kuka tana dan buga qafarta,fuskarsa ya hade sosai,harga Allah yana da wani irin kishi akan shahidan,yana jin kaman zai mutu idan wani ya zuba mata idanu bare akai ga batun furta yana sonta "Ashe kuwa zaki shekara a soron nan,don na rantse ba zaki matsa ko inaba indai fuskarki da wannan kwalliyar" tasan cewa da gaske yake saita rasa ya zata masa,hakan yasa ta juya ciki ta yiwa amarya umaima magana,ita tazo ta roqa mata alfarma wanda daga qarshe yace saidai ta cire eye lashes din da aka qara mata don nata ma ya isheta,sannan kuma a goge wasu abubuwan da aka sa mata a fuska,saida akayi hakan sannan ya qyaleta,duk da haka a gaba ya sakata tana gaba yana bayanta,sai faman sakin ajiyar zuciya yake,duk da an rage kwalliyar gani yake kowa ma kallonta yake,adaidaita ya tare mata bai barta ba sai daya rakata har qofar gidan bikin,yana mata sallama zai juya itama ta tubure kan dole yaje wajen bikin,yasan da biyu tayi hakan don bai fiya zuwa wajen fate fate ba,to amma abinda bata sani ba gata tayi masa,don har yanzu hankalinsa bai aminta ba da zuwanta wajen ita kadai,gani yake tafi kowacce mace kyau,hakanan idanun kowanne namiji yana akanta "Zanje na dawo,idan kun gama shiryawa kimin magana" tana masa dariyar cin galaba ta shige ciki. Qarfe shida aka soma daukan 'yammatan,a sannan tuni ta yiwa anwar waya,shida da rabi ya kirata yace ta fito yazo,su biyu ne ita da 'yar anty umma yayar ummanta,ga mamakinta yana jingine jikin wata qaramar mota mai kyau qirar kia,ya sauya shigar jikinsa,wannan dinma yadine wanda tare ya siyesu da wancan,saidai wannan ruwan madara ne lallausa,shima bamai tsada bane amma sai taga kaf mazan wajen ba wanda ya kamoshi a kyau duk dacewa jayan jikinsu yafi nashi tsada nesa ba kusa

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});