Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,299 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zata ganshi ba,da amotar haya suka tafi nafisa ba zata rabi wurinsa ba saidai wajen wani,don bashi da gurin da zata roqi alfarmar zama har shahida ta gansu tare,da a motar haya ne da tuni tare zasu dawo da shahidanshi su rabu cikin farinciki sa walwala. Ta gefan shahida kuwa hankalinta a tashe,gani take kaman za'ayi mata qwacen anwar din,duk kwanan duniya idan ta kalli anwar din sai taji fargaba ta cikata,anwar nada kyau kwarjini da cikar zatin da zai zama abun kwadayin mallakar kowacce mace,kallo daya ta yiwa nafisa ta tabbatar 'yar masu dashi ce,idan hakan yayi nasarar janye hankalin anwar fa tayi yaya?,da sauri ta kori wannan tunanin daga ranta,don fatan dorewar hakan,a ranar da qyar ta sami bacci duk da wayarta na silent tana da yaqinin ta tara miscal na anwar din. Itama kusan tubure masa tayi yadda ya mata kwanaki,qarshe dai saida suka dangana da anty amina tayi sasanci kamar yadda ta saba,zuwa lokacin ba qaramin jigata yayi ba,wanda hakan ya faranta ran shahida ta wani gefe,tunda ko babu komai ta sake sanin mizanin da zata dora soyayyar da yake matan. A haka rayuwar wannan masoya take ta kuma ci gaba da gudana,kowanne cike yake da tsananin so qauna da kuma kishin dan uwanshi,kowannensu cike yake da buri da fatan farantawa dan uwanshi,har zuwa sanda shahida suka soma shirye shiryen yin candy,a boye ba tare da saninta ba don yasan zata iya hanashi anwar yasa akayi mata jaka da memo,yace bazaiyi calender ba bare wani qato ya rataye a dakinsa ya dinga kalle masa mata,ko memo dinma babu hoto a jiki,yayi mata key walder hakanan ya soya kayan da zata saka ran walima complete,dukka yayi hakanne bada saninta ba don yanason mata suprise ne. _*TAURARUWA MAI WUTSIYA*_ Tsaye take a hamshaqin falonta gaban window,wanda yaji komai da komai na kayan alatun more ruwa,falone dan qarami saidai ya wadatu da dukkan wani abun buqata domin hutawa da nutsuwar ruhi,tana sanye da riga da skert wanda iyakar skert din qaurinta "Ina jinki mema....na zaqu naji daga gareki,wallahi tun ranar dana soma ganinshi har yau ban sake samun nutsuwa cikin rayuwata ba....duk iya qoqarina na ganin na samu zuciyarsa abun yaci tura,yana da wata izza kaman d'an wani,kwarjininsa shike sake dakusar dani,inajin sonshi ya kaimin ko ina cikin jiki da ruhina" tayi maganar duka tana tsaye jikin window din ba tare data juyo ba,idanunta na farfajiyar gidan data wadata da korayen tsirrai. Tabe baki mima tayi,ita duka mamaki ya cikata,ta yadda feena ta fada qaunar talaka matsiyaci kaman anwar din,ta kuma fita hayyacinta lokaci guda,haka kawai tana tsaka da more rayuwarta,to amma ita nata yi mata aiki ta kuma biyata,indai zata biyata din ai shikenan "Ba haka kawai kika kasa samo kanshi ba ai feena" meman wadda ke zaune kan daya daga cikin kujerun falon qafarta daya kan daya tana karkada takardar hannunta ta fada,da hanzari nafisa ta baro inda take ta qataso gaban feena sannan ta yiwa kanta mazauni kan wata kujerar daban tana duban feena idanu bude "Kaman yaya?,meye dalili?" Wani shu'umin murmushi ta saka tana qiyasta kudin da zata tatsa wajen feena a yau sanadin wannan zazzafar jaridar da zata saida mata "Zaki iya tuna yarinyar da kukayi kallon kallon da ita ranar da muka zauna motarshi" yatsanta manuni ta daga sama da sauri kaman maishirin bada amsa cikin aji "Exactly....na tunata,tun ranar yarinyar na tsaye cikin raina...na rasa wacece mai shegen kyau da izza haka,da farko nayi tunanin qanwarsa ce saikima naga basuyi kama ba tako ina" "Right....budurwarsa ce" gaban feena ya fadi ta zaro idanu "Wait....da saura fa" mima ta fada tana dariya qasa qasa sannan ta gyara zamanta "Idan kin taba karanta labarin soyayyar romio da Juliet wannan sun wuce haka,qauna ce irin wadda zata bawa bahaushen mutum mamaki,son junansu suke kaman tare aka haliccesu,daya baya komai saida shawarar daya,daya baya iya tafiyat da komai saida daya,bari dai na baki a taqaice a dunqule,sun narke sun zama abu daya...." "Dole su rabu su zama abu biyu kuwa...na fahimta,wato saboda itane na kasa cimma burina kenan?" Ta tambayi mima kai tsaye,kai ta jinjina tana lumshe idanu sannan ta bude "Qwarai kuwa....amma saidai karki damu akwai mafita" ta ambata tana warware takardar hannunta,daki daki ta soma karanta mata abinda shahida tafiso da wanda bataso har sai da nafisa ta gaji daji ta daga hannu tana dakatar da ita "Jin wannan abun dame zai qare ni?,qara qonamin rai kikeson yi mima" "Kina da gajen haquri inda matsalarki take kenan....amma tunda kina ganin haka shikenan bari na wuce" ta fada tana ninke takardarta,caraf ta kama hannunta "Mtsweeww,banason ko jin sunanta ne wlh,zauna mu qarasa" bata wani jaa ba ta zauna din don tana lissafin abinda zata samu ne,taci gaba da karanto mata inda gabar qarshe take dauke da "Ta tsani cin amana,ta tsani munafurci,ta tsani ta zauna dakai zuciya daya kai kuma ashe da zuciya biyu kake tare da ita" tana kaiwa nan ta daga kai tana duban shahida sannan taci gaba da karatunta,fagen anwar ta shiga,abinda yakeso da wanda bayaso inda shima tashi gabar qarshe ta zama "Ya tsani mace mara kamun kai,ya tsani macen dake bin maza,sannan yayi masifar tsanar mace 'yar shaye shaye" ta sake yin shuru tana duban feena,dan jim tayi sannan ta gyada kai tana sakin murmushi sosai tana nuna mema "Shegiya mima,sai yanzu na gane...ko shahidan yana tsoron kaidinki qarashe bayaninki" sosai taji dadin yadda take sake samun karbuwa wajen feena koda yaushe,ta ninke takardar sannan ta sake tattara nutsuwarta "Yarinyar tana da ciwo tana da matsala cikin rayuwarta,duk da har yanzu ba'a gano wace damuwa gareta ba,amma zamuyi amfani da wannan damar mu sanyata ta zama 'yar maye,kinga mun samu matakin farko na rabasu,zai zama matakin farko ne saboda wanna kadai bai isa ya rabasu ba bayan bai kamata da wani laifi ba bayan wannan,itama bata kamashi ba,bayan ta zaba tantiriyar mashayiya zamu qara mata da sharrin bin maza...wannan kuma aikin wadanda suka san kan na'ura mai qwaqwalwa ne,zamu saka mata cewa baya sonta ita kuma yana tare da wata,duk zan kula da yadda komai zai kasance,naki kawai ki saki kudi ki zuba idanu" murmushin nasara ya subucewa feena,ji take kaman ta samu anwar ta gama,dukka kudin da yayi saura a jakarta ta zazzagewa mima,ta kuma yi mata alqawarin wasu "Ya...zaki dinner dinsu mu'az dinne" idanu ta fiddo "Me zai hana?,ai har na shirya qaryar da zanwa momy ta barni na fita,kedai jirani na shirya" cikin mintina qalilan ta fito cikin wasu matsiyatan riga da wando,hannunta riqe da burmemen hijab da take qoqarin sakawa mima na zaune na sheqa dariya,ta zuba duk kayan makeup dinta cikin haka ta maqaleta cikin hijabin sannan ta dubi mima "Mu hadu a bakin gate,don da mun shiga tare ta ganki zata saka ayar tambaya" haka kuwa akayi,ta isa wajen momy ta shirya mata qarya ta yadda ba yadda za'ayi ta ganota sannan ta fice suka hadu da mima,tun a cikin motar ta cillar da hijabinta tahau tsara kwalliyarta yayin da mima ke driving. Cikin nasara da taimakon ubangiji ta kammala rubuta jarabawarta kaf,wanda a ranar sukayi bankwana da dalibai da sauran malamai 'yan uwansu,a daren ranar anwar yayi shiga ta musamman yazo don tayata murna,ya kuma bata duk wani gift daya tanada saboda ita,sai

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});