Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,317 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana da cikakkiyar damar da zatayi lacturing amma bisa wani dalili nata ta zabi koyarwa a qaramin mataki na 'yan nursery da primary,tun daga bakin section din yara ke gaidata cikin nuna qauna da soyayya,yayin da ita kuma take amsa musu cikin fara'a da jansu a jiki,sai da zata shiga staffroom sannan suka rabu da yaran,suka wuce azuzuwansu ita kuma ta shiga ofishin malamai. Office ne madaidaici mai girma da tsari,duk da girman office din su uku ne kacal a ciki,makaranta ce da kallon farko.idan kayi mata zakayi tsammanin private ce irin mai tsadar nan,saidai sam ba haka abun yake ba,makaranta ce da wani shahararren d'an kasuwa ya ginata saidai akwai sa'ido da kulawar gwamanti akanta,duk da cewa shike dauke da duk wani nauyi na makarantar,kama daga school unifoarm,littafan karatu,abincin da yaran zasuci na break da dai sauran dukkan wasu lalurori,aqidarshi ce haka,yakan gina makarantar a duk inda yaga hakan ya dace,ya kuma hada hannu da gwamnatin garin donta tayashi lura da makarantar,bawai lura na su bada wani abu ba,a'ah,tsarin gudanarwa tsaro da sauran abubuwan da ya kamata,kusan kowacce qasa dake africa ya gina makarantu d'aya,saidai a inda makarantun suka fi yawa a nigeria ne yankin arewa,duk dalibin dake karatu cikinta yana farinciki haka iyayensa farinciki da kasancewar dansu a cikinta,saboda ta tsaru da tsari mai kyau,hakanan tana da dukkan wani qualities da akeson makaranta dashi. Hidaya kawai ta samu cikin office din tana hada littafan dalibai da tayi marking,da alama tana da ajine qarfe takwas,murmushi suka yiwa junansu "Kinso makara yau malama shahida" "Yau da gobe hidaya...." Ta fada tana zaman kan kujerar teburinta. "Sai Allah..." Hidayan ta qarasa mata kana ta gyara yafen mayafinta "Mun tashi lpy...."cewar hidaya "alhmdlh....mun godewa Allah" "Ma sha Allah....zan wuce aji don Allah idan kausar ta iso kice mata ga kayan nan ta duba" "Babu damuwa" cewar shahida,tana kallon hidaya ta bude office din ta fice sannan ta maida qofar ta rufe musu,saita maida kanta a hankali ta kwantar saman teburin dake gabanta,idanunta a lumshe,batason tuna komai,batason tunanin komai,tanason ta saita kanta kafin lokacin shigarta aji yayi,don nan da minti goma sha biyar periode dinta zai shiga. *********************** "Dukkanin takardun na cikin wannan file din,sauran takardun da za'ayi amfani dasu a d'akin taron ma gab suke da kammala,na shiga dakin buga takardun na musu magana sunce nan da mintina goma da izinin Allah....engine ne yaso basu matsala" mutumin d'an kimanin shekara arba'in dake zaune saman d'aya daga cikin qawatattun kujerun dake shirye a qayataccen office din ya fada,yana bayanin ne ga dogo kuma tsayayyen matashin dake tsaye tsakiyar office din yana kai kawo a hankali,hannunshi riqe da dan madaidaicin glass cup,yayin da d'aya hannun nasa yake riqe da wata zungureriyar takarda yana dubawa,sanye yake da suit masu azabar kyau da d'aukar idanu,wankan tarwada ne shi,dogo wanda ke tafe da tsaho da kuma 'yar qiba kadan,wadda kai tsaye ba zaka kirata da qiba ta zahiri ba saidai ace murjewar jiki,doguwar fuska gareshi wadda take cikakka,lumsassun idanu mai kama da wanda kejin bacci,saidai da girmansu idan ya budesu sosai aduk sanda yaso hakan,bashi da cikar gashin gira can,saidai gashin idanunshi a cike suke,siraran labba masu taushi,da qawataccen qasumba da aka gyarata aka rage mata yawa da fadi,ta zagaya ta hade da habarsa da kuma qasan hancinsa,kanshi saisaye ne wanda ya qawata fuskarshi saboda gyaran fuska da aka yi masa,kana kallonshi kasan tsafta hutu da iya dressing sun kama gida a wajensa,kana kallonshi kasan ba ma'abocin fara'a bane,sosai ya bada hankalinsa kacokam kan takardar hannunsa da gani kasan abune mai muhimmanci yake dubawa,yayin da ta wani b'angaren daban ya bada hankalinsa ga wanda ke masa bayanin "Ina imran?" "Yana sashen aje tsaffi da sabbin qarafa" kai ya gyada yana ci gaba da takawa sannu a hankali,har yanzu hankalinsa na kan takardar hannunsa "Amma ba tuni na bada umarnin a cire wancan a sanya sabon da mukayo order ba?" "Sorry sir.....engineer din ake dako,yaudai yayi alqawarin zuwa ya hada" ya fada cikin nuna tsantsar ladabi,bai sake cewa komai ba har na tsahon wasu mintina,sannan ya isa gaban teburinshi ya aje kofin hannunsa,ya taka zuwa gaban matashin dake zaune ya bude files din dake gabansa ya sanya takardar ciki ya rufe,sai a sannan ya dubeshi "Karku wuce qarfe biyu ba'a gama kammala komai ba,bana son delay...."kafin ya gama fada qofar office din nashi dake aiki da lantarki ta bude da kanta,wanda hakan ke nuna muhimmin mutum ne zai shigo ciki,don ba kasafai take budewar da kanta ba sai bayan sakatariyarshi ta sanar masa ya bada umarni sannan ta bude din. Dukkansu maida idonsu sukayi kan qofar,tun kafin ta qarasa shigowa ya fahimci wacece,hakan ya sanya ya maida idanunsa kan yaqub,don bashi da tabbacin yanayin da zata shigo dashi,don haka ya sallameshi "shikenan....zaka iya tafiya" a bakin qofar sukayi clashing da ita tana shigowa,cike da girmamawa ya rusuna yana miqa mata gaisuwa,kaman yadda aka saba haka ta amsa a daqile,cike da izza,shan qamshi taqama da isa,yaqub ya wuce ita kuma taci gaba da takowa cikin office din. Fuskarta qunshe da murmushi,hakanan idanunta na kan fuskarshi,taku take d'ai d'ai harta kusa cimmasa,yayin da shi kuma yake kallonta yana nazarin shigarta,babu laifi shigar tata tayau,doguwar riga ce mai wrapper,saidai kuma gajeran hannu ce,tayi rolling mayafi qarami a kanta,high hill ta saka a qafafunta,hannunta ba komai daga waya sai key din motarta "It seems kamar bakayi farinciki da ganina ba M.A" ta fada a shagwabe tana kallonshi "Uhummm....who told you?" "Ba kowa....kawai yau nayi missing ganin cute face dinka,ka fita tun da sassafe ban samu ganinka ba,me yasa baka yi break fast ba yau a gida?" Takawa yayi zuwa d'aya daga cikin kujerun wajen yayiwa kanshi mazauni,itama yayi mata nuni da yatsa yana nufin ta zauna,sai data zauna sannan yace "Me yasa zaki fito a irin wannan lokacin?" Farrr tayi da ido,tana jin wani dad'i na ratsata,a duk sanda ya nuna kulawa a gareta takanji babu ya ita a fadin duniya,sai data saki murmushi sannan tace "Kai kadai na fito don na gani,kasan bazan iya wuni ban ganka ba" shuru yayi yana dubanta,can qasan ranshi yana jinjina wanne irin so nafisa ke masa?,kalamanta sunyi shigen kama da na wata,wadda ya soma qoqari da kokawar badda ta daga ranshi a yanzun da takeson taso mishi,don ko kusa bashi da sha'awar hakan,itama kallonshi take,tasan cewa wannan plan din nata ya d'anu,tanason dukkan wasu kalamai nata da yanayin kulawa yayi kama dana waccar da tasan ta taba wanzuwa cikin rayuwarshi,duk da tana baqinciki da cewa kwaikwayonta shine zai sama mata wani gurbi data dauki tsahon lokaci tana neman samu a zuciyarsa,duk da irin baqin fenti da qin jini da yayyabe tarihinta a zuciyarsa,amma duk da haka kishinta take fiye da komai a rayuwarta "Naso na iso tun dazun sai aka samu akasi" ta katse kallon kallon da sukema juna,dan muskutawa yayi kadan,cikin muryarshi dake nuna halayyarshi yace "Akasi?,name fa?" Sai data d'an jaa fasali sannan ta sake cewa "Wallahi wasu 'yammata ne suka so yiwa motata b'arna..." "Me ya gamoki dasu?" Ya tambayeta kai tsaye yana ci gaba da dubanta,kafad'a ta daga sannan tace "No,karka damu,na musu uzuri saboda a make suke,kana ganinsu kasan sunsan sirrin shan syrup,har zan hadasu da police sai kuma na wuce don bai kamata na b'ata lokacina akansu ba" sexy

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});