Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,294 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kamar wadda aka biyo,don burinta shine ficewa daga makarantar ta tserewa sautinsa,wannan sautin da ta jima da neman tsari dashi da mamallakinsa. Titi kawai ta miqa bata ko waiwaye,bata buqatar abun hawa don ji take kaman qafafunta zasuyi mata aiki fiye da abun hawan,sauri kawai take zubawa wani irin radadi na keta zuciyarta kamar ana yankarta da reza,anwar dai anwar dai?,tabbas da tasan akwai wata rana da zasu sake haduwa kaman haka da tuni ta yiwa kanta kandagarki da ita,wannan wace irin baqar rana ce a wajenta "Anty shahida...anty shahida" taji ana qwalla mata kira wanda sam bata tsaya ba har sai da akasha gabanta,shugaban sashe ne riqe da jakarta ya miqa mata "Don girman Allah kiyi haquri anty shahida,ya dauki hukuncin da dukkanmu bamu isa mu sauya shi ba" 👑 *zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina buqatar siya ki tuntubi wadan nan numbers din* 07067124863 *ko kuma* 09032345899 *kuyi subscribing youtube channel dina don samun damar ganin shirye shiryenmu,subscribe kyauta ne!* 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos *Alqawarin Allah* 1️⃣9️⃣ "sabon abune wannan a wajenmu,abinda bamu taba gani yayi ba tunda muke dashi,kowa ya shaidai wannan kirkin nasa....anty shahida kodai wani abu kika masa?,mutumin qwarai irin haka canzawarsa...."da sauri ta yanke masa hanzari "Na gode malam,haka Allah ya qaddara" gaba tayi da sauri don ita kadai tasan me take ji,ita daya tasan ya take ji,baifi taku biyar ba adaidaita sahu tasha gabanta tana tambayarta ina zata je?,sai data shiga sannan ta gaya mishi inda zai kaita,duk yadda taso daure zuciyarta ta bari saita isa gida saita kasa,ta tattakura ta rushe da kuka wanda har sai da dan sahun ya waiwayo "Hajiya...lafiya?,kiyi haquri komai yayi zafi maganinsa Allah" ita dai bata iya tanka masa ba illa kukanta data ci gaba dayi. Komao nata ta wurgar tsakar dakinta sannnan ta zauna dirshan tana risgar kuka,tanajin kaman ranta zai fita ne,duk wata nutsuwarta a yanzu babu ita,anwar dai shi idanunta suka gani?,anwar shine ya mata wannan tozarcin?,wanne abu tayi mai munin da har zaikai anwar ya kasa mantawa irin haka ya sake binta da mummunan shaida da wulaqanci?. Kusan haka ta dauki dogon lokaci,wanda ita din batasan wadanne awanni ta shafe haka ba,sai tsintar muryoyin anty zubaida tayi da huda,taso qwarai ta tashi amma ta kasa saboda wani mugun ciwo da kanta yake mata,da qyar take iya motsawa bayaga idanunta da suka zama tamkar fulawar da aka zubawa yeast,muryar saddiq taji yana cewa "Mummy...tana dakinta" a hankali anty zubaida ta turo qofar tana cewa "Alhmdlh,shahida kin daga mana hankali,ina kika shiga haka ke kuwa don Allah" ta qarashe maganar tana qarasowa kanta,zaro ido anty zubaida tayi ganin irin rawar darin da take yi "Subhanallahi,ashe bakyajin dadi" ta qaraso gefan gadon shahida ta zauna tana qoqarin yaye rufar da tayi,da qyar da taimakon anty zubaidan ta tashi ta zauna sosai,qarya tayi mata kan tana shiga makaranta zazzabi ya saukar mata shi yasa ta dawo bata kai ga zuwa dakin hutun ba ganin yadda duk suka damu daga anty zubaidan har su saddiq,farouq anty zubaida ta saka ya hada mata ruwan wanka,saddiq ya zubo mata abinci,ita taimaka mata ta shiga bandaki tayi wanka gami da daura alwalar sallar azahar da magariba da duka bata samu yinsu ba,bata bar dakin ba sai data ga taci abinci ta kuma sha magani sannan. Tana daga kwancen amma hawaye take sharcewa masu dumi,duk yadda taso ga kaucewa anwar da shafe duk wani abu daya shafeshi amma haka yaci tura?,wai sai yaushe?,sai yaushe zaibar rayuwarta zuciyarta da kuma ruhinta ya huta?wunin ranar gaba daya wani irin wahalallen yini tayi,ba shakka anwar ya zamewa rayuwarta babban qalubale,har zuwa dare tana cikin yanayi guda wanda da qyar da sudin goshi ta samu wani wahalallen bacci ya dauketa. ********* ********** A hankali ya daga cup din qarshe na coffe din da yayi saura ya kwankwade wanda shi kansa baisan kofi nawa yasha ba tsahon awannin daya kwashe zaune a wajen,idanunsa jajur suke kai kace an badawa idanunsa yaji ne a ciki,saidai yaqi yarda ko kusa ko alama a kira masa likita ya dubashi,bugu da qari dumin jikinsa ya qaru sosai har kana iya juyo hucinsa idan ya fidda iska daga bakinsa. Lumshe idanunsa yayi ya dora hannunsa saman sumarshi mai tauri saidai a gyare take matuqa yana yamutsata,buri yake inama ya iya kuka idan yana cikin tashin hankali ko tsanani,inama hawaye zasu fita daga idanunshi ko zai samu sauqin radadin da yake ji?,cikin sauri ya sake bude idanun shi wanda suka sake kadawa fiye da dazu,ko yaya ya runtsesu kwalaben da suka zubo daga jakarta yake gani,hakan yana nuna har yau bata bar dabu'arta ba?,waishin waye ne?,waye ya koya mata wannan dabi'ar?,babu shakka da zaisan waye shida ita duka saiya hadasu ya hukuntasu,dukan teburin gabansa yayi da hannunsa ko zaiji sauqin radadin da zuciyarsa ke masa amma a banza. Knocking katafariyar qofar falon aka somayi wanda yana ji yayi funfurus,saidai ya cika ya batse saboda koma waye yana son sake birkita masa lissafi ne,bayan kuma ya riga da yaja kunnen duka ma'aikatan gidan na kada wanda ya sake yako doshi sashensa. Knociking din jinsa yake har qwaqwalwarsa,hakan ya sanya ya miqe a fusace ya isa qofar ya budeta ya kuma bude baki don zazzagewa koma waye masifa,muhsin ne bayanshi likita ne tsaye cikin fararen kayan aiki,dole ya hadiye abinda yaso amayarwa ya saki qofar ya juya zuwa cikin falon ya zabi wata kujerar sabanin wadda ya tashi daga kai ya zube yana maida numfashi,kallo daya muhsin yayi masa baice dashi komai ba ya kalli likitan sannan ya maida idonsa ga anwar din "Zaka iya aikinka" yace dashi,saiyaka jinjina kai ya soma takawa inda anwar ke zaune ya aje akwatinshi kana ya bude,ya ciro abun gwada B.P ya daura a hannun anwar ya soma gwadawa,cikin sakannin da basu wuce goma ba ya warware abun daga dantsensa ya samu kujerar dake daura dashi ya zauna sosai idanunsa a kanshi "Yallabai....kasan yadda jininka ya sake hawa kuwa?" Ya tambayeshi kanshi tsaye "Na sani" shima ya bashi amsa bayan ya sake bude dukka idanunshi akan likitan,cikin mamaki likitan ya maida dubanshi ga muhsin,saiya masa alama daya rubuta magani kawai ya qyaleshi,hakan kuwa akayi ya rubuta maganin ya baiwa muhsin takardar sannan ya tattara kayanshi ya yuwa muhsin din sallama ya wuce. Sai daya tabbatar da fitar likitan sannan ya miqe riqe da takardar maganin ya qaraso inda anwar din ke zaune,idanu ya zuba masa yana kallonsa wanda hakan ya sanya anwar kau da kai "Tsahon shekaru kana fama da wannan damuwar,kaqi gayawa kowa dalilinta,kaqi gayawa kowa dalilin faruwarta,duk dai amma bazai wuce akan shahida ba,anya kuwa anwar anya?,me yasa kake shirye shiryen halaka kanka ne babu gaira babu dalili?" Zumbur ya miqe ya soma takawa don barin gurin "Kar sake cewa dominta ne,na riga dana shafe babinta kamar yadda na shafe babin komai daya faru dani a baya" qara sauri yayi ya wuce zuwa bedroom dinsa yanason baiwa kansa qwarin gwiwa don baison ma anty husaina taji cewa baida lafiya,yanzu dukkan tsofaffin matsaloli zasu taso,magana wata nabin wata har sai yaji kaman kanshi zai tarwatse. Kwananta goma sha hudu tana qoqarin saisaita kanta da maida kanta cikin yanayin daya dace,yaqi tayi ba dan qarami ba a kwanakin da kanta,ta rame qwarai saboda jinya

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});