Chapter 51
Chapter 51
din jikinsa sannan ya maida glass din motar sama ya bude murfin ya fito,sai daya rufe motar sosai sannan sulaiman yayi gaba anwar din na biye dashi a baya. A bakin qofar gidan anwar ya coge yana duban soron gidan yana tuna wani abu daya taba faruwa a wajen shekaru shida baya,a shekarun baya da suka wuce idan aka ce masa zai sake taka soron saiya qaryata,amma dattako mutunci da qaunar da dattijuwar ta nuna masa a baya ya dawo dashi yaci gaba da nuna mata nashi karamcin,sulaiman ya dubeshi "Ka shigo mana,bismillah" kai ya kada "Shiga tukunna ka gaya mata zan shigo" anwar din ya masa kwarjini da yawa don haka ya kasa musa masa,ya saka kai zuwa cikin gidan karo na biyu. "Tace ayi maka iso" sulaiman din ya fada yana duban anwar,a nutse ya sanya qafafunsa soron yaci gaba da takawa bisa jagorancin sulaiman. Qarqashin bishiyar dake gefe daya na tsakar gidan tabarma ke shimfide,nan sulaiman ya nuna ma anwar,ya sabule saucikin dake qafarsa ya ajesu sannan ya isa saman tabarmar ya zauna,dai dai lokacin da daada ke fitowa daga rumfarta hannunta dauke da kwanon sha wanda ke cike da ruwan randarta mai sanyi,idanunta akan anwar din harta qaraso,duk da ganinta dashi sau biyu ne tak a rayuwa,a lokacin da yafi haka qarancin shekaru da rashin cikar xati da kamala. Hannu yasa ya amshi kwanon sanda take shirin xama ya ajeshi gabanta,saida ta zauna sosai sannan ya soma gaidata "Mun sameku lafiya?" "Lafiya qalau alhmdlh....yaro kaike hidima damu haka tsahon shekaru uku amma baka taba tsayawa na ganka ba ko wani cikin 'ya'yana ya ganka ba bare yayi maka godiya" murmushi yayi har fararen haqoransa suka bayyana idanunsa a qasa,sai taga ya sake koma mata anwar din sak,anwar din da har kwanan gobe takeson tasan ina yake?,meya rabashi da jikartata,amma har yau idan zata tambayi shahidan sau dari bazata tada kai ta bata amsa ba,harsai ta gaji tayi shuru "Amma saurayi....sai naga kamar anwaru ko?,anwarun shahida" daga kai yayi yana duban dadan tare da jinjina ma qoqarinta data iya ganeshi "Shine daada" gaba daya fuskarta ta washe da fara'a sosai,wani irin farinciki ya mamayeta,tunda taga anwar din a wancan shekarun Allah yasa mata qaunarsa,ya shiga ranta sosai,dai daikun ranaku ne da zasu zo su shude bata tuna dashi ba "Ma sha Allah,Allah abin godiya,kana nan dama anwaru?,har kana iya zuwa guna ka aikomin da saqo amma ka kasa shigowa na ganka mu gaisa ko sau daya ne?,haba anwar,me muka yi maka haka?" Murmushin dai ya sakeyi "Kawai haka Allah ya tsara mana daada,shi ya raba ganawarmu sai yanzu daya qaddara haduwar tamu" "Wannan haka yake" ta fada tana jinjina kai cike da gamsuwa,har yanzu bakinta ya kasa rufuwa "Ashe daada baki manta dani ba?" Baki ta kama tana cewa "Ta yaya zan manta dakai anwar,bani bama hatta da qannen mahaifin shahida sun kasa mantawa dakai,kaiba irin mutumin da za'a manta dashi bane anwaru,gashi shekara kusan uku kanamin alkhairi ba tare daka bari nasan cewa kai bane....kai sule,zo nan zoka amsowa anwaru damammiyar fura da nono" tafada tana qoqarin kunce daurin habar zaninta dake daure da kudi,da sauri anwar ya dakatar da ita "A'ah daada,don Allah karki wahalar da kanki" dakatawa tayi da abinda take "Karka tsaidani anwaru,nasan yana daya daga cikin abinda kafison sha rahama ta gayamin tun lokacin ban manta ba,wannan shine kadai abinda nakejin zan iya maka" saiya qyaleta ta kunce kudin ta baiwa sulaiman ya amsa ya fice. "Wanne laifi muka yi maka haka anwaru daka gujemu haka?,ka bace mana bat,ina tsaka da murnar jikata ta samu nagartaccen miji,tunda har naji isma'ila Allah ya jiqan rai na yawaita maganarka na tabbatar da nagartarka,dana ganka kuma saina sake tabbatarwa lallai nagartaccen ne kai,ita kuma waccar almurar koxan kwana kwana tambayarta ba zata cemin kanzil ba" gyara zamanshi yayi sannan a nutse yace "Dukkan abinda ya faru a rayuwar bayi ba shakka muqaddari ne daga Allah,kisa a ranki hukuncin ubangiji ne bacewata daga rayuwarku..." "Gaskiya ne" ta amsashi tana gyada kai,sadda kanshi qasa yayi sosai "Zuwa nayi ki bani aurenta daada" kyakkyawan murmushi ya subuce kan fuskar dattijuwar,cikin ranta tana godewa Allah tare da hamdala,tayi tsammanin shahidanta ta rasa nagartaccen anwar din nan,sai gashi ya dawo a sanda basu zata ba "Wannan ai tsohon zance ne anwar,shahida ai taka ce" wani abu ya tsaya masa a wuya,zayafi kowa farincikin jin hakan da ace a baya ne sanda shahidan take shahidan anwar ba yanzu data zama ta kowa ba "Na sani daada,amma wannan karon nazo ne a bani auren shahida da gaske ba kamar a bayan ba" "Indai wannan kake da buqata kana iya komawa da aurenta,bamu da haufi kanka anwaru,koda mahaifin shahida na raye nasan haka zai fadi" hakanan yaji wani sasauci a ranshi da zuciyarsa,wanda ya danganta hakan da nasarar da zai samu ce ta nunawa shahida da saurayinta cewa shiba sa'ansu bane takowanne fanni "Amma duk da haka,ka jira zuwa gobe zan kira kawunnanta na tabbatar musu da aurenka da shahida" "Na gode qwarai da gaske daada da wannan karamci,amma inason kimin wata alfarma guda daya" "Ba zata gagara ba insha Allahu anwaru"sassauta muryarsa yayi "mun samu sabani da shahida wanda shi ya zama silar rabuwarmu na wadan nan shekaru,na dawowa shahida saidai yadda ta dauki zafi fiye dani ta tabbatarmin ba zata taba karbata a matsayin miji ba..." Yadan dakata a ranshi yana istigfari kan qaryarda yayi "Inason don Allah dada a boyewa shahida gaskiyar wanda ke neman aurenta,inason na gaya mata da kaina mu sasanta kuma kanmu ba tare da kowa ya shigo ciki ba" qanqan da ido daada tayi cikin masifa tace "Wato ja'ira tasan komai shi yasa ko zaka kwana tambayarta saita dinke bakinta ko?,yoni aida ka barni da ita don dakalin qofar gidansu mu gauraya da ita,ja'ira tana tafe kaman daben masallaci kai kace ba ita bace..." Duk yadda yake jin ransa saida fadan dadan ya bashi dariya,ya danne yana cewa "Ki haquri daada karki tasarmin ballina"qwafa taja "Don dai kace haka ne amma da goben zan gaya mata da kaina,idan yaso ta iskoni katsina ta hukunta ni" daada na tsaka da fadan dake baiwa anwar dariya yake kuma sakashi nishadi sabida nasarar daya samu sulaimanu ya dawo da damammiyar fura mai sanyi data sha suger,sosai anwar ya sake ya dinga sha suna hira da dadan tana bashi labarai wanda anan yaji labarin rasuwar abban shahidan,sosai jikinsa yayi sanyi qwarai,ya dinga jin babu dadi har cikin ransa,ya dinga tuno abubuwa da dama tsakaninsa dashi,yana qaunarshi sosai hakanan yana ganin girmansa,kaman dan cikinsa ya daukeshi ba suruki ba,yayiwa daada ta'aziyya sosai. Bata barshi ya tafi ba saida tayi masa irin danwaken da yakeso,wanda ta taba yi masa zuwansa ziyara wajenta na farko,baici da yawa can ba saboda tuna wani lokaci da yayi a baya,hakan yasa yaji cikinsa ya cushe,sai bayan la'asar sannan yayi mata sallama ya wuce. Daga nan gidan wani abokinsa ya wuce,bashi ya baro wajensa ba shima sai gab da magariba,koda ga koma unguwar kakannin nasa yana aje motarsa ya wuce sallah masallaci,acan suka gamu da kawu modu suka rankayo gida bayan an idar. Inna na zaune cikin rumfarta iskar fankar solar da anwar ya hada duka gidan na kaiwa da kawowa a falon,bata qure fankar can ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96