Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,299 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

daya,haka soyayya take?,haka masoyi yakewa masoyinsa?,sai taji ya sake sireta,daya zama mai dogon nazari da dukka abubuwan da suka faru yanzu basu faru ba Ranta ya ninka bacin da yayi,hankalinta taji ya tashi,da qyar ta bude baki cikin muryar kuka tace "Mugu azzalumi,ba ruwanka da kowa sai kanka,ba ruwanka da damuwar wani sai taka,ka tanadi mugun nufi akaina kan abinda baka da cikakkiyar hujja a kai...." "Wacce huja nake nema baya ga wanda na samu....!" Ya juyo a fusace ya fada idanunshi da suka kada zuwa jaa suna kanta "Ba hujjar kake nema ba,kanayin komaine don ka wulaqantani dama,ka shirya komai ne donka tozartani,to Allah ya fika,ba zaka taba samun nasara a kaina ba,nuradden kuma idan Allah yaga dama kai baka isa ka rabani dashi ba"itama ta fada cikin tunzura fushi da bacin rai "kome zaki fada dai dai ne,duk yadda kika fassara lamarin a ranki ko a bakinki kisa a ranki haka ne,any ways ma ni nasan na taimaki rayuwarki ne,ko kina tunanin wancan wawan idan yaji wace ke a baya zaici gaba da haukan da yake a kanki?,kinga 'yammata....koki sawa ranki sauqi ko kar kisa duk uwar ubansu daya" kai take gyadawa bacin rai na cinta,idanunta fes cikin nashi,ji take kaman ta shaqe anwar din,a yanzu babu halittar data ji ta tsana sama dashi "Zan saka salamar duk da bakayimin fatanta ko burin samunta,amma ka sani....tsugune bata qare ba,don babu abinda zanyi da masoyi irinka nawar!,ka shirya tarbar duk wani abu da zai tunkaroka!" Tayi lafazin da alama wani abu ya motsa ranta qwarai,duk da murta na a raunane amma amma fuskarta da qwayar idanunta na bayyana jarumtarta,wani malalacin murmushi ya saki ya sake matsowa inda take,wannan karon har qamshin turarensan nan data sanshi dashi yana busowa zuwa hancinta,ya kafeta da idanunsa,muryarsa can qasa kamar mai shirin furta kalaman soyayya a gareta yace "A shirye nake,kece zan gayawa ki shirya zama dani idanma ba'a shirye kike ba,yaushe kikeso wasan ya fara?" Ya fadi cikin halin ko in kula,ganin kallon da yake mata bacin rai ya sanya ta fashewa da kuka sosai ta zube saman kujerar tana rufe fuskarta da tafin hannunta,saiya tabe baki yana isa inda hularsa take yasa hannu ya dauka yana cewa "Ashe raguwa ce ta gaske,tun yanzu?,wasan namu kuwa zaiyi iri qarkon da nakeso?" Ya dora hularshi saman kansa sanda ya qarashe maganar,saiya sanya hannunsa cikin aljihunsa ya ciro kudade sabbabi masu dan yawa ya aje hannun kujerar da take kai yana cewa "Ga kudin zance nan,kuma bance a sayi abunda za'a bugu da kudina na,idan aka siya Allah ya isa na" sosai maganar ta doketa,tana niyyar daga kai ta dubeshi ta fuskanci ya juya zai fita ne,har yakai bakin qofa sai yasake cewa "Ammmm..." Yana dawowa da baya,kanta yazo ya tsaya hannunsa daya a aljihun wandonsa dayan kuma yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa "Karki manta da sadakina akanki,shaidu kawai za'a tara a daura,ban lamince ki kula kowanne dan iska ba,ciki harda wannan looser din,idan kuma kikayi hakan shima Allah ya isa ban yafe ba" saiya sassauta murya ya sauko da kansa qasa qasa gab da ita "Ina fata har yanzu wasu daga halayen anwar basu bace miki ba daga kanki,mutum ne mai kishi,ina da kishi kan mace koba wadda ban biya sadakinta ba bare wadda na cire halalina sa nasha wahalar nema zafi da sanyi nabiya" a fusace ta bude fuskarta saboda yadda maganganunshi suka isheta,saita ganshi dab da fuskarta,cikin bacin rai da muryar kuka take cewa "Sadakinka din banza da wofi,idan kana son nunan kudinka wata tsiya ce kaje ka karbi sadakinka idan har ka isa cikakken namiji" tsaf ya karanci bacin ran dake kwance muraran saman fuskarta,saidai yadda yake jin quna yana tunanin bata jin haka,duk sanda zai kalli fuskarta yana tuna sanda aka sauketa ne a gabanshi,cikin maye,cikin jini,pant dinta a gabanshi aka cilloshi,wani ya riqe zuwa jikinsa gaban idanunsa,saiya runtse idanunsa kana ya bata baya ya soma takawa "Idan kin isa ke kije ki karbo kin kiga idan ban amsa ba,dama taimako nayi kuma na fuskanci ke bakiga hakan ba" daga haka ya qarasa ficewa daga dakin,sake rushewa da kuka tayi,ta tsani kalmar taimakon nan,wannan wanne irin cutace?,ita zai taimaka. Cikin gida ya qarasa,daada na rumfarta a zaune ita da hasina,saiya cire takalmansa ya zauna saman tabarmar dake shimfide qasan inuwar bishiyar dake tsakar gidan,daadan tayi tayi dashi ya shigo amma yace wucewa zaiyi,dole ta fito ta zauna daga gefan tabarmar itama "Zan wuce daada,ina tunanin rana ita yau za'a kawo lefe,to bansan inda za'a kai ba,can wajen umma,ko nan garin ko kuma gidan uncle hisham?" "Babu damuwa akai can hidan hashimun tunda acan za'a yi duka bikin,muma can zamu tattara ai mu tafi" "To daada,Allah ya saka da alkhairi ya qara girma" ya furta yana dan sadda kanshi qasa alamun girmamawa "Ina kuma ta shiga?" Daada ta tambaya,ya fuskanci shahida take magana,saiya saki murmushin daya qwata fuskarshi duk da baikai masa qasan ranshi ba "Tana daki tana kukan bata sona can na barota" kama baki daada tayi tana salati harta baiwa anwar dariya,harya miqe ya aje mata kudi ma sam bata kula ba tana ta jajjabi tare da sillewa shahidan hasina na dariya,sai daya sanya takalmansa sannan ya kalli hasina "Taimaka kije ki fito da ita daga dakin karta rube" dariya hasina ta saki sosai,abun saiya qayatar da ita,ya yiwa daada sallama suka fice zuwa soron gidan shida hasina. Bakin qofar dakin ya coge ya yaye labulen bayan hasina ta shiga dakin,ta isa inda take dunqule tana gursheqen kuka "Saikace yau akace za'a kaiki?,taso da Allah karki tara mana jama'a" hannun hasina ta buge tana jin takaici yana cikata,duk maganganunsu da daada tana jinsa,tamkar ma ya raina mata wayo ne,ko yana tunanin 'yar qaramar shahida daya sani a baya ce wannan? "Matsa hasina barta,bari na rage miki aikin na dauketa zuwa qofar soro saiki qarasa shiga da ita ciki,da sauri ta bude fuskarta,idanunta da sukayi jawur zuwa fuskarta ta kalleshi dasu "wallahi wallahi ka sake ka tabani sai kayi dana sani!" Ta fada a kausashe "Meye hakane shahida?" Hasina ta tambayeta tana dubanta cikin mamakin kausasa lafazin da tayi,dubanta yake sosai,yana son yace shine farau?,amma idanun hasina yasa ya maida amsarsa "Wallahi wallahi kinji nima na rantse matsawar baki tashi kin shige ba ko abinda yafi danasani zanyi saina dangana dake har rumfar daada" saiya maida dubansa ga hasina dake tsaye tana kallon dramer "Ina cikin mota a qofar gida,minti biyar na bata idan ta dara hakan bata tashi ba ki fito ki gayamin" kai ta gyada ya saki labulen ya taka a sannu ya fice daga soron. Bata buqatar duk wani abu da zai kawo wani kusanci tsakaninta dashi,so take ya tafi yabar gidan saboda haka ta miqe tana hada hanya,hasina ta dauki kudin dake aje inda ta tashi ta bita dasu a baya,ko kallon dada dake tsakar gida tana mita batayi ba ta shige rumfar daadan ta zube saman kujera,saita dora hannu aka ta fashe da ihun kuka ko zataji salamar radadin da take ji cikin ranta,hasina kallonta take idanu a waje cikin rudewa tace "Meyw haka ne shahida kike kamar wata 'yar shekara goma,ya zaki tara mana jama'a?" Takai qarshan maganar sanda daada ta runtumo cikin dakin tana tambayar ba'asi "Au ihu kike?"

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});