Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,318 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kadai na rage ina rayuwa a gidanmu,maganar gaskiya shahida zan gaya miki ba boye boye a tarayyarmu,saboda ina fata Allah ya shiga lamarinmu,niba mai kudi bane,bani da komai sai abinda Allah ya tsagamin,karki tsammacin samun rayuwa mai tsada,kyauta mai tsada ko nauyi daga wajena irin wanda samari sukewa 'yammatansu,indai kina ganin tafiyarmu akwai matsala,duk da tsananin soyayyar da raina ke miki zan iya haqura na barki da muradinki" kai take girgizawa,sam a batajin zata iya rabuwa da anwar,qaunarsu dashi daga Allah take,wata qauna ce mai qarfi data kama dukkaninsu cikin qasa da kwana bakwai,tasan cewa ba qaramin lamari bane a tsakaninsu "Ni dinma ba wata bace,kaman yadda kake gani rufin asirin Allah ne da dukka bawa yake qarqashinsa,ina addu'ar yadda muka hadu Allah ya tabbatar damu a haka" sai data fada kuma taji kunya ta kamata,sun d'an jima kadan suna hira ita dashi,yana bata labarin abinda yake karanta yanayin makarantar da dai sauransu. Qarar wayarsa ce ta sa ya dakata da abinda yake gaya mata,ya ciro wayar daga aljihunsa yana duba mai kiran,gabansa yadan fadi,don sam zuwansa wajen shahidan ya mantar dashi abinda ya tunkarosa,neman mudin rigestration,hausawa suka ce mai kurmin ido da wuri yake fara kuka,haka yake duk sanda suka soma exams tun a lokacin yake fara fafutukar neman kudin,wanda tunda ya soma karatu haka yake,Allah gatan bawa ne,sai yake bashi kafin lokacin da za'a rufe,saidai wannan karon yana fargaba,saboda ganin yadda rayuwa ta sake cudewa,fadi tashi ya yiwa mutane yawa,babu ta sake samun gindin zama a rayuwar al'umma. Saida aka sake kira ya sami ya daga da sauri,don babu ko ficika a layin nashi "Ina zuwa in sha Allahu" kawai yace ya latse wayar ya maida aljihu,miqewa yayi tsaye hannayensa cikin aljihun yana duban shahida qasa qasa,ta masa kyau qwarai,bai taba ganin macen data masa kyau kaman shahida ba,komai nata mai kyaune,tun daga yatsun qafarta har kanta,dauke kai yayi da sauri yana kwabar kansa daga kallon qurillar da yake mata sanda ta dago kai tana dubanshi sanda taga ya miqe "Allah ya taimakeki zan tafi" ya fada yana qawataccen murmushin daya sake fitar da sigar kyansa, "Allah ya tsare hanya...na gode"murmushi ya saki "nine da godiya,yau an shayar dani irin abinda nake ji abokaina na fada....zumar soyayya.....dama haka take?,haka akeji?" Dora tafin hannayenta tayi saman fuskarta ta rufe tana murmushin jin kunya,yayin da ya zuba mata idanu yana kallon zara zaran yatsun hannunta da suka dauki hankalinsa,ya sauke sassanyar ajiyar zuciya cikin ranshi yana roqon Allah daya sanya yana kammala karatunsa ya shiga cikin sahun daliban da suke samun aiki da wuri,don a yanzu jikinsa har ya soma sanyi da irin kyan daya lura shahida nashi,irin matan da masu kudi ke rububin samu su aure,Allah kada ya sanya shahidan ta subuce masa,ubangiji yasa rabonsa ce,da ya gama dacewa nan gidan duniya,tunanin daya dinga yi kenan har sukayi sallama ya wuce. Koda yaje inda ake kiran nasa ma ba wani biyan buqata ya samu ba,kudin da yake nema bai samu ba,amma sai sam baiji wata damuwa can ba wadda ya saba ji a baya duk sanda yaje neman kudin registration dinsa bai samu ba,wannan karon darensa cika yayi fal da tunaninta da begenta,ya dinga juyi saman katifarsa,ya danna wayarsa yana zargin kansa me yasa bai karbi number wayarta ba?,sai kuma ya saki murmushi daya tuna koya karba dinma ina yaga credit din kira?,da gaka ya lallashi kansa yana addu'ar Allah ya kaimu gobe lafiya. Tun daga wannan lokacin wata iriyar soyayya mai qarfi ta shiga tsakanin anwar da shahida,dukkan tunaninsa nata ne,duk wani motsinsa shahida na ciki,tuni labari ya kai kunnen anty usaina,kallon anwar din kawao tayi tana mamaki,tunda suke dashi bai taba kawo mata zancan wata yarinya ba,hasalima koda da tsokana tayi masa zancan budurwa tabe baki yake sannan yace "Uhmmmm,anty kenan,anata kai wa yake ta kaya?,yanzu kojin labari kikayi ina kula wata ba zaki tsawatarmin ba?,a wannan yanayin da muke ciki anty mu tsira da rayuwarmu ma,indai ina da abun kula budurwa na kasa baki ba shakka bani da wani amfani a rayuwa" tunda har taga yadda anwar ke muradin shahida sai batace komai ba,tunda haka ta faru tasan cewa soyayya ce tayi masa mugun kamun da bai zata ba "Su anwar manya,ashe an fada tarko" dariya yayi yana shafa kansa "Anty,shahida ta dabance,na soma sonta a sanda babu tsarin soyayya a rayuwata gaba daya,tana da hankali da kamun kai yarinyar,anty koke na kawowa shahida kika ganta zaki sota,fatana kawai Allah ya dubeni dana kammala karatun nan na samu aiki,na kula dake anty na kuma samu damar auren shahida" damuwar qaninta tata ce,su biyu suka ragewa juna a duniya,anwar irin mutanen nan ne jajurtattu,duk da bashi dashi,duk da shima neman dafawar wani yake amma indai ya samu ko yaya samun yake saiya tuna da ita,akwai sabo sosai a tsakaninsu,ba wanda ke iya boyewa wani wani abun,sun zama iyayen juna abokan shawarar juna "Kullum fatana kenan anwar,ina maka addu'ar wahalar da kakesha a rayuwarka ta zame maka alkhairi dajin dadin da har iyayenmu dake kwance a kabari xasu ji dadinsa" "Allah ya amsa anty" "Yanzu ya ake ciki da kudin resgistratin dinka?" Ta fada bayan ta aje masa shinkafa kwano guda da wake rabin kwano,wanda aduk sanda ta samu budi take bashi ya samu ya sauya kalar cimar da yake ci,duk da itama ahalin ni 'yasun take,amma haka suke raba wuya da dadi tare,kamar yadda idan shi dinne ma hakanne,duk da yana qoqarin boye mata wasu abubuwa da dama amma takan fuskanci wani abun koda bai gaya mata ba da bakinsa "Muci gaba da addu'a,in sha Allahu kafin sannan Allah zai kawo" "Allah ya dafa mana don isar annabi" "S A W" ya qarasa mata,daga haka ya miqe,saita kwance bakin zaninta,yasan me take da nufin yi saboda haka ya dakatar da ita "Ina da hamsin dina da zan hau mota,bar kudinki" kai ta daga tana kallonshi,tanason karanto gaskiyarsa ko akasin haka,don ya saba gaya mata haka,qarshe kuma dabawa yake a qafa har gida duk da tazarar dake tsakaninsu saboda bashi dako sisi,ganin haka saiya juya da sauri yana mata sallama,bai tsaya saurarenta ba ya fice. Yana tafe a hanya tunani fal ranshi,shi daya idanunsa sun kada sunyi ja,fatansa da addu'arsa Allah ya bashi abinda zai sakawa anty usaina dashi,tunanin shahida daya fado masa a rai shiya dauke duk wani radadi dake ransa,har ya murmusa shi kadai ba tare daya san ma yayi hakan ba,ya dinga tuna wuninsu na yau,yana zaune daga shagon balarabe kamar yadda ya saba yana more kallonta,lokaci lokaci sukan hada ido su sakarwa juna murmushi,wani kallo da yayi mata ya sanya man abincin dake hannunta ya kware duka cikin botikin shinkafar,kunya ta kamata yayin dashi kuma ya dinga mata dariya,har a hanyar komawarsu gida ya dinga tsokanarta kan ashe raguwa ce ita bai sani ba?,anya idan anyi aure zata iya dauke soyayyarsa kuwa?,kunya ta sakata guduwa ta barshi da botikin,sai mubina ce ta shigo dashi,wannan tunanin na shahida shi ya hanashi jin nisan tafiyar,har ya iso gida,sai yaji kamar baiyi tafiyar komai ba,bai zauna ba ya kunna risho dinsa ya dora shinkafar,sannan ya tube kayanshi ya shiga wanka saboda idan ya fito yaji dadin duba karatun jarrabawarsa. Cikin wasu 'yan qididdigaggun kwanaki qalilan wata iriyar alaqar soyayya mai qarfi ta qullu tsakanin shahida da anwar,wata

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});