Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 76

Chapter 76

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,291 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gauta,waqar jarumar matace ta soma plying,waqar tana taba zuciyarsa sosai,yana son ya kashe amma saiya samu kanshi da barinta tana ci gaba da tashi,sautin na karade motar yana shiga kunnuwansu cikin sauti madaidaici gami da haifarwa da kowa yanayi na daban. Ta gefan ido ya saci kallonta,tayi laqwas cikin sit din motar,idanunta a lumshe,zara zaran gashin idanunta sun fito sosai,juyawa yayi duka yana kallonta sosai,daidai sanda ta bude nata idanun,saiyayi hanzarin dauke kanshin ya maida ga titi yaci gaba da tuqa motar cikin nutsuwa da qwarewa. _zaku iya jina shuru gobe saboda wani uzuri daya tasomin,amma idan na samu dama zaku jini in sha Allah_ 😊 _kuci gaba dai dayi mana uzuri,kana taka ne Allah na tashi,ta Allah itace dai dai,har kullum burinmu mu sauke nauyinku dake kanmu,muna godiya_ 🙏🏽*Alqawarin Allah* 3️⃣7️⃣ _ziyarci tasharmu ta youtube SAUTIN HIKIMA,don sauraren littafanmu sabbi dama tsofaffi_ https://youtu.be/H7M7h6l6wNM A maidaidacin qawataccen wajen ajiyar motocin gidan ya ajeta kusa da 'yan uwanta biyu qasan wata rumfa,ya kashe motar can qasan ranshi yana furta "Alhamdulillah Ala kulli haal" sai a sannan shahida ta bude idanunta tana duban gabanta "Ki fito" ya furta yaba bude side dinshi ya fita,cikin kasala da fargaba ta bude ta fito ta soma bin bayanshi sanda yake takawa ta wata qawatacciyar doguwar hanya mara fadi sosai wadda kai tsaye ta sadasu da falon gidan. Ci gaba yayi da tafiya bayan shigarsu falon,saita tsaya cak cikin baqunta tana qarewa falon kallon,ba wani mugun qato bane,amma wadatacce ne sosai,wanda jeran ciki ya bala'in birgeta tare da fito da kyawunsa,komai na ciki yayi kyau ya dace dashi hakanan ya dace da gidan. Mintuna biyu ya dawo idanunsa a kanta ya mata nuni da wata hanya wadda zata sadaka da farfajiyar da dakunan baccin gidan suke "Dukka qasan nan mallakinki ne,ga hanyar dakinki nan,duk abinda baki fahimta ba kina iya tambaya,zaki iya tafiya ki kwanta" a hankali ta soma takawa zuwa direction din daya nuna mata ba tare data bashi amsa kotace wani abu ba. A nutsewa takebin yalwataccen dakin da kallo mai dauke da seat din gado dressing mirrow da wardrobe,sai wasu kujeru qwaya biyu masu dogon makari,daga dan qaramin carfet xuwa labule zuwa teburin mahadin kayan gadon duka dark purple ne da light ash,shima dakin ya qayatar da ita matuqa,komai ya tsaru yadda ya kamata,qamshi kawai yake fitarwa da sanyin raba,ta taka a hankali ta zauna kan daya daga cikin kujerun dake jere gefe daya zuciyarta nason soma rawa tana hana kanta,qofar dakin aka turo ta daga kai ta dubeshi sanda yake shigowa da leda a hannunsa,baice komai ba harya shigo ya aje ledar kan dan teburin wanda yake daura da ita ya fice daga dakin hadi da jaa mata qofar. Ta jima zaune a wajen tana saqa da warwara,ta dade tana tunanin wanne irin dama zasuyi?,ta dade tana wassafa yadda zata mu'amalanci anwar din ta ina zata soma kallonsa a matsayin miji?,yaya zamantakewarsu zata kasance?,sai da jikinta ya soma gaya mata irin gajiyar da yayi ya soma gazawa sannan ta bude toilet din dake cikin dakin,shi kansa abun kallo ne,ta dinga amfani da komai na ciki yadda ya dace ta sauya pad din jikinta ba tare data nemi ta sauya kayan jikinta ta dawo ta nemi waje ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Duk da gajiyar da yakeji saidaya kammala komai nashi daya saba kafin yin bacci,ya nade saman nashi gadon yana sauke nannauyan ajiyar zuciya idanunshi a lumshe kafin daga bisani ya budeshi,hakanan yakeson gidan,duk da bai kama qafar girman wanda yake ciki ba da haduwarshi gami da cin kudi ma baki daya,fili ne daya siyeshi a zamanin da yake hada kudi da qyar,a zamanin daya tara kudin tun daga qananu zuwa manya,gininsa ne kawai yayishi sanda yake cikin wadata,yanayin yadda aka tsara gidan yakan burgeshi shi kansa,ba yadda anty usaina batayi ya zauna a wancan ba tunda yafi girma amma yace a'a yafison wannan,yabi dakin da kallo a hankali idanunsa ya sauka kan ledojin daya shigo dasu,ci gaba yayi da kallonsu yana tuna wani lokaci can baya,lokacin da yake anwar din take shahidanshi,a lokacin yakan tsokaneta da cewa awara zai siyo mata duk randa aka kawota gidansa ranar farko tunda mayyar awara ce,dariya take ta sunne kanta a hijabi sannan tace "Ko haka ka shigomin ya anwar bazan damu ba,saboda kaidin da aka bani yafi komai da zaka shigomin dashi" ajiyar zucuiya ya sauke idonshi ya sauka kan safe dinshi daya daukoshi daga gidansa ya dawo nan dashi,zuciyarsa na gargadarsa amma sai daya sakko,ya saka lambobin sirrin ya budeshi,a hankali ya ciro envalope din da har yau yadda aka kawota haka take,ko takardar bayan ba'a canza ba bare saqon ciki,har rubutun jiki yana nan baro baro kaman yadda aka rubuta din. Zaman dirshan yayi qasan tiles din dakin,zuciyarsa na masa zafi tun bai fito da hotunan ciki ba,ya daga ya zazzagesu duka suka zubo,dai dai sanda wani abu ya tokare masa maqoshi,idanunsa suka soma sauya launi zuciyarsa na suya,haka ya dinga daga hotunan daya bayan daya yana kalla abinda ya jima baiyi ba donko sashen da suke ajiye bai fiya son kalla ba,kowanne hoto yayi a qalla minti biyar yana qare masa kallo kamar maison sanin dai dai lokacin da aka daukeshi,haka ya gama kalla baiga wani abu da zainuna akwai kuskure koba dai dai ba game da hoton,kowanne ya fito tas ya fita kar hakanan komai na jikin shahidan ya bayyana baro baro,gudun zuciyarsa yaji ya sake daduwa kansa ya soma daukan dumi,haka ya janyo envalope din ya soma maidasu ciki jin alamun hawan jininsa na neman tashi,yasan shiya jawa kansa daya kalla hotunan,amma hakanan kawai yaji kaman an tsunkulinsa kan ya jawosu ya duba,saiya miqe a daddafe ya shiga bandakinsa ya saje daura alwala ya fito ya tada sallah. Kamar yadda ya saba kafin ya idar sanyi da nutsuwa sun saukar masa,ya daga hannu yayi addu'a sosai sannan ya shafa,saman abun sallar yaci gaba da zama,kwanan da baiyi ba kenan kan gadonshi a darensa na farko cikin gidan aurenshi,sai akan abun sallar ya kwana,wanda bai sake farkawa ba saida ya rage mintuna kadan a tada sallar asuba sannan ya sake wata alwalar bayan yayi wanka,ya bare wata jallabiyyar ya saka bayan ya feshe jikinsa da turare masu sanyi da taushin qamshi. Har zai fice saiya tuna da ita,ya tabbatar haqqinsa ne ya kula da addininta,koma meye a yanzun tana wuyanshi,saboda haka ya sauya akalar tafiyar tashi zuwa sashen dakunanta. A sannan itama ta farka tana gefan gado tana shirin shiga bandaki ta sauya audigar jikinta taji knocking,tasan ba kowa bane saishi,tana ji amma tayi banza kaman bata ji ba,saida yayi a qalla wajen sau goma sannan tadan ja gyaran murya kadan,hakan yasa ya gane ta tashi sai kawai ya juya ya fice zuwa masallaci. Sanda ya dawo kashe wayoyinsa yayi baki daya ya haye saman gadon sosai bayan ya cire jallabiyar jikinsa daga shi sai gajeran wando,ya kwanta dai dai saman gadon yana sauke gajiyar da jiya bai samu saukewa ba. Duk da gajiyar datayi qarfe tara saura taji baccin ya fita a kanta,saboda haka ta miqe ta fada bandaki ta tara ruwa mai dumi sosai tayi wanka ta dawo cikin dakin ta shirya cikin atamfa riga da zani simple mara ado,bayan mai sai powder da kwalli kawai data

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});