Chapter 87
Chapter 87
amma ta nuna kamar abin bai dameta ba,tunda tana tsammanin abinda ta aikata shine dai dai "Mommy,zuwa nayi na baki haquri" dubanta tayi sannan tace "Akanme?" Shuru tadanyi sannan daga bisani kanta a qasa tace "Nasan na bata muku kan qin auren anwar da nayi,amma a sannan idanuna ya rufe,don Allah momy kuyi haquri,ki tayani baiwa daddy haquri" tabe baki mommyn tayi tana miqewa "Aike za'a baiwa haquri,name zaki bamu haquri tunda kin aikata dai dai,rayuwarkice fa kuma kika zaba mata abinda kike ganin yafi davewa da ita" daga haka mummyn ta bude qofar dakin nata ta fice,da kallo ta bita kafin daga bisani ta janye idanunta tana sauke ajiyar zuciya,lallai aikine ba qaramiba a gananta kafin ta soma shan kan iyayenta,wanda sune tsaninta na nasararta Wajen anwar,saita miqe kawai tabi bayan mummyn,sai inda qarfinta ya qare kam. Lokacin sallar azahar taga ya sanya rigarshi ya fita,hakanan ta miqe itama ta shiga bandakinsa dake nan cikin office din ta shiga tayi alwala tazo ta tada sallah kan abun sallarsa dake cikin office din. Bai wani jima ba da yawa ya dawo dauke da takeaway,ya aje mata nata ya bude nashi ya wanke hannunsa ya soma ci,ta gefan ido take satar kallonsa,wato har yau halinshi nacin abinci da hannu dai yana nan. Ranar haka suka wuni har lokacin tashi,yana aikinsa tana zaune waje daya,saidai sam taqi zama saitin da zata ga fuskarshi koshi yaga tata,tayi danasanin karbar tayin aikinsa da biyoshi kamfanin datayi yafi sau shurin masaki,kome za'ayi kam ba zata taba iya aiki dashi ba,ta gwammace tayita zaman gidan akan zamansu qarqashin inuwa daya,suna musayar numfashi daya kusa da juna sosai har kamar haka,ta saurari muryarsa data wulaqantata wulaqancin da har yau yaqi gushewa yabar zuciyarta,duk sanda ta nutsa duniyar tunani saita tuna kalamansa da har yau bataji kalaman da suka yiwa kunnuwanta muni kamarsu ba. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe shida da minti ashirin da biyar na yammaci ya shigo gidan. ,yana zaune a falon yana sauke gajiyar daya tarawa kansa yau,ji yake kaman bazai iya hawa samanshi ba,da ido yake bin kowanne sashe na falon da kallo,ko ina fes yake ba alamun datti ko qura,hakanan yana fitar da sassanyan qamshi mai ratsa zuciya,amma saika rantse ba wani dan adam cikin gidan,sai qarar na'urori kawai dake fita kadan kadan,ya janye idanunshi kenan yana shirin miqewa yaganta tana fitowa,sanye take da doguwar rigar atamfa mai gajeran hannu,wadda tafitar da shape dinta sosai,kama dafa damammen cikinta,qirjinta da yake das cikakku,zuwa mazaunanta da suka dace da qirar jikinta,kanta babu kallabi sai gashinta dake daure waje daya,tayi kyau kamar wata 'yar tsana,fatarta ta sake fresh na zama waje daya,da alama ta fito daukan wani abune,suna hada idanu tayi turus kamar zata juya,sai kuma ta maze taci gaba da takowa,dab da zata giftashi tace "Sannu da zuwa" ciki ciki kamar wadda aka turawa tsumma a baki,wanda banda kunnuwansa dake dukka wajen ba bazai iya jin me tace ba,hakanan yaji yana da sha'awar ya takaleta,kwana biyu da bai ganta ba saiyaga kaman ya jima bai ganta din ba,saboda haka ya hade rai qyam sannan yace "Zonan" yadda ya kirata cikin gadara da bata haushi,amma saita tuna koma meye itace a qasanshi,saboda haka ta sassauta ranta ta tako inda yake zaune ta tsaya gefanshi,saiya daga kai yana kallonta "Me haka?,zaki samin ciwon kai rage tsahonki" dubansa tayi sosai kaman zata tanka saita shareshi,ta zauna hannun kujerar da take daura dashi,samun kanshi yayi da qare mata kallo,idanunsa suka tsaya kan qirjinta kamar wani mayen qarfe ke janshi,idanu ta zaro data fuskanci inda yake kalla,saita goye hannayenta a wajen abinda ya fargar dashi cewa kallonshi ya zarme da yawa,saiya maze yana sake hada rai "Haka kike zama dama idan bana nan?" Ya jeho mata tambayar,mamaki ya kamata,ta kasa gane me yake cewa? "Kamar yaya?,ban gane ba?" Ta tambayeshi itama tana kallonshi bayan ta kalli kanta "Wannan shigar gaskiya bata dace ba" mamaki ya sake kamata "Waini da waye cikin gidan?"ya gane sam maganarsa bata da makama saboda haka yace "tunda haka kika zaba shikenan,bani ruwa nasha tunda baki iyaba har sai mutum ya roqa" ta gane sarai neman abun fada yake,saboda haka ta miqe kawai ba tare datace masa komai ba ta wuce kitchen din,saiya waiwaya ya bita da kallo,karon farko da yaji wani abu yana ratsashi tun daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafafunsa,ya lumshe ido yana ambaton sunan Allah,baqon feelings yakeji sosai wanda har yaso danne gajiyar da yakeji. Idanunsa ya bude sanda take aje masa ruwan,idanunsa kuwa sukayi kyakkyawan gani,saiyaji kaman yakai hannunsa kamar ana janshi ne,ya samu da qyar yayi controlling kansa sanda qamshin turarenta ya soma rarraba mishi hankali,yana kallon tasoma takawa don barin wajen ya kasa magana sai binta da idanu,da qyar yasamu cewa "Nace ki tafi ne?" Waiwayowa tayi tana kallonshi fuska a turbune "Zo nan" ya sake fada,ba yadda ta iya don batason ta saba da dabi'ar musu da gardama data soma masa ya zame mata jiki "Zubamin" ya fada yana nuna mata ruwan,haka ta sake duqawa tana zuba masa,ta gama ya amsa yana nuna mata wata leda daya shigo da ita "Kaimin dakina" ya dora qafarsa daya kan daya ya soma shan ruwan,baki take turowa ciki ciki,ya soma kaita bango,ta dauki jakar ta soma hawa saman,nan ma da kallo ya bita yadda mazaunanta ke juyawa kai kace tana sane takeyin hakan,ajiyar zuciya ya sauke bayan ta bacewa ganinsa,ya dire cup din da hanzari ya miqe ya rufa mata baya. *Alqawarin Allah* 41 _ku ziyarci tasharmu ta youtube don sauraren tsofaffi dama sabbabin littafanmu,da sababbin ma da bakusan dasu ba wadanda zasu fara zuwa muku ta tashar nan gaba kadan da ixinin ubangiji_ https://youtu.be/-tPtW9YtNpU Tana shirin fita yana shirin shigowa sukayi kacibus,tadanja da baya tana neman hanyar wucewa "Waye ya miki karatun yadda ake zama da mijine?" Yayi tambayar yana dubanta,dagowa tayi cikin mamaki ta kalleshi,saiya dage mata gira guda daya "Eh,gaskiya bata iya komai ba kaman yadda na lura,saboda bangani a qasa ba" ya fada yana takowa zuwa inda take tsaye,yanajin bazai iya barinta yadda ta rikitashi taci bulus ba ba tare da shima yau yadan taba koda fatarta ba yaji yadda akeji,baya ta soma ja tana kallonshi,bata fahimci me yake shirin aikatawa ba saida ya kusa qureta jikin madubin dakin,idanunta cike fal da tsoron da takeson boyewa tace "Meye haka kakeyi?" "Abinda kika gani" ya bata amsa bai fasa nufota ba,cikin dan tsoro tace "Karka tabani" cak ya tsaya yana kallonta "Tunda kwartone ni?" Ya amsa mata ta sigar tambaya,bai kuma bi ta kanta ba yaci gaba da nufarta,don baijin zai iya haqura din shima bai d'aana ba,ko ina ta kalla ya riga daya kangeta,a haka ya hade gap din dake tsakaninsu,ya zagaya hannunsa ta qugunta ya janyota sosai cikin jikinsa,fuskarsa ya sauko da ita dokin wuyanta yana kai hancinsa,ta soma juye juye tana son ta qwace daga hannunshi "Banaso,meye haka,ka sakeni" "Ni kuma inaso" ya fada yana fidda numfashi saboda yadda abun ya soma masa dadi,wayarsa dake saman mudubin ta dauki haske da qara,wanda hakan yaja hankalinsu gaba dayansu,a tare idanunsu ya sauka a tare kan screen din wayar,sunan NAFISA ya bayyana saman screen din,dauke idanunshi yayi yaci gaba da abinda yake,hakanan taji wani abu yadan sosa mata rai kadan,amma saita dauka yadda ya tarfata ne yake yadda yaso da ita,sosai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96