Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 75

Chapter 75

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,320 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana kallon mai shigowar,sa'ida ce saidai ita batasanta ba,fuskarwa a washe ta qaraso falon tana takowa a hankali tana waigawa,da alama ba'asan tayo.nan ba,dab da shahida ta zauna tana kallonta "Anty,saike kadai?,nayi nayi da ummi tabarni nazo tace a'ah zamu takura miki kina hutawa ne,da qyar na samu na sallabo" murmushi shahida tadan saki tana duban sa'ida "Ina yini anty,ya gajiyar biki" "Lafiya lau,me sunanki" "Sa'ida,'yar anty usaina ce ni,kuma qawar uncle anwar" girarta shahida ta dage duka biyun tana dubanta alamun tambaya,dorawa tayi "Wallahi kun dace sosai anty keda uncle,uncle ya samu mata me kyau" tana murmushi sosai ta fada tana kuma sake kallon fuskar shahidan data ji tana burgeta,murmushi shahidan ta kuma saki "Ko?" Tace cikin sigar tambaya,kaita kada "Qwarai kuwa,amma anty,don Allah ki kularmin da uncle dina,wallahi inason uncle anwar,yana da kirki sosai,yana sonmu shima,yana kula damu sosai da sosai,don Allah anty" saita tsaya tana sake dubanta kafin ta kuma sakin murmushi,ta dora hannunta saman hannun sa'ida "Uncle din naki nima zai iya kula dani ne sa'ida?" Dariya ta saki "Tabdi,sosai kuwa anty,kinsan uncle anwar kuwa?,ai matarshi ta caba" saitayi qasa da murya "Na zaci fa zai iya aurena harna cewa ummi ina sonshi,ranar saida na daku sosai,ashe babana ne" dariya ta kubcewa shahida da sa'idan duka,da sauran dariya a fuskar shahidan tace "Babanki ne sa'ida,amma kita addu'a Allah ya baki wanda ya fishi nagartar halaye" "Akwai wanda yafi uncle dina kuwa?" Ta fada cikin tantama da tunani,kaita jinjina "Qwarai kuwa,duk wanda kika gani kome kika gani a duniya akwai wanda ya fishi akwai wanda baikaishi ba akwai dai dai dashi" "Tohm shikenan......" Bata qarasa maganar ba suka jiyo taku ana nufowa wajen,saita fiddo idanu "Na shiga uku anty,Allah yasa ba ummi bace" riqe hannunta tayi "Karki damu,zance nina kiraki ki tayani hira" shuru sukayi suna jiran ganin wanda zai shigo din. Sallamar mutum biyu ce,ummin sai muryar anwar daga bayanta,mummunar faduwar gaban data sanya shahida maida kanta cikin mayafi ta saukar mata,ummi anty usaina ce a gaba sai anwar din daga bayanta,idanunta akan sa'ida nashi idanun nakan shahida da kanta ke sunkuye lullube da mayafi,kama baki tayi "Na shigesu ni usaina,sa'ida...sa'ida ki shiga hankalinki da wannan rawar qafar taki,dama da akacemin ba'a ganki ba nan kikayo?,to tashi ki wuce ki bama mutane guri" da sauri ta zame hannunta cikin na shahidan sannan ta miqe,duk da haka da zata gifta anwar din saida tace "Uncle,kayi kyau sosai yau,amma wallahi in gaya maka gaskiya?,anty shahida ta fika kyau ashe" anty usaina batasan sanda dariya kubce mata ba,yayin da murmushi ya subuce masa shima ya bita da kallo harta fice daga dakin,ba ruwanta hakanan take,idan taga gaskiya saita fada,kusan halayenta suna kamanceceniya dana mahaifiyarsu,duk cikin yaran anty usaina tasu tafi zuwa daya,kusan sanda aka haifi sa'ida tare sukayi rainonta shida anty usainan tun lokacin mahaifansu suna raye,idanunsa ya sake saukewa akan shahidan a hankali duk da bai ganin fuskarta,yana tsaye a wajen har anty usaina ta zauna "Zauna daga can" ta fada tana masa nuni da inda takeso ya zauna din,kujerar da shahida ke kaine,duk da cewa mai yalwa ce amma saiya zauna a hannun kujera,cikin hikima da nutsuwa ta soma magana dasu "Alhamdulillahi rabbil Aalim,komai na rayuwa a tsare yake zuwa daga wajen ubangiji mai kowa da komai,basai na tsaya wani tambaye tambaye ba don nasan ba amsa zan samu daga gareku ba,abunda nakeson na fada shine,wannan auren naku ya isheku dama sauran mutane ishara,kun rabu da juna kun guji juna ba tare da dayanku ya sake tunani Allah zaiyi ikonsa ku sake haduwa a wannan bigire ba na aure,wannan kadai ya isa ya nunawa bawa yana tashi ne Allah yana tasa,ta Allah kuma itace dai dai,saboda haka ku sanyawa zukatanku salama,ku zauna da juna cikin aminci da bin umarnin mahalicci,kada ku yiwa Allah butulci wanda ya baku aron rai da lafiya ya kawoku wannan lokacin koda cikin zukatanku bason hakan kuke ba,dubunku na nan na fatan samun kamar takun,ya sake hadaku a sanda kowannenku rayuwarsa ta sauya ta samu ci gaba,ta yuwu hikimar rabuwar daku dama don kowanne ya cimma gacinsa ne,wanda wala'alla idan kuna tare da zaku cimma wannan abun ba,ku kauda hayaniya da tashin hankali ku ajeshi idanma kun daura azamar hakan,kuyita addu'ar Allah ya baku mafita ya sanyaya zukatanku" saita waiwaya ta dubi anwar "Kai kaine babba sannan kaine shugaba,kai keda hankali fiye da mace,sabida haka fiye da rabin nauyi da yanayin yadda zamanku zai kasance ya ta'allaqa a wuyanka ne,kasan komai basak na fada maka ba,iyayenmu kafin su rasu makarantace a gareka,ka dauki matarka ku tafi daga kai sai ita,ina muku fatan alkhairi,shahida...Allah ya bamu alkhairinsa kinji" kasa magana tayi kunya na kamata,ta fuskanci hakan sabida haka tayi murmushi taga bari kawai ta murje mata kunyar a wuce wajen "Ki daina kunyata,don kincemin bakison anwar wallahi banga laifinki ko daya ba,hasalima burgeni kikayi,donko nice kw abinda zanyi kenan,kawai saika rabu dani tsahon wasu shekaru ka zagaya ta bayan fage ka aureni haka akeyi?" Ta qarashe maganar tana duban anwar gamida harararsa "Kuma ka nemi yafiyarta kukan daka sa ta dinga yi da aurenka data yi bayan bata shirya ba bata amince ba" murmushi ya qwace masa mai dan sauti,itama antyn tana murmushin ta fice ta barsu. Shuru ya ratsa dakin na wasu mintina masu dan dama,idonsa akanta da yake lullube,zuciyarsa na masa bitar wasu shekaru can baya,yasha kwana idanunsa biyu yana wassafa yaya zai kasance duk randa shahida ta zama mallakinsa,yasha raba dare yana tsara ranar da irin abubuwan da zasu faru a lokacin,ga komai yazo ga lokacin yazo saidai cikin bahagon yanayi da dabaibayi,ajiyar zuciya ya saki a bayyane sannan ya furta cikin sanyin murya "Tashi mu tafi" yi tayi kaman batajishi ba,yayi tsai yana dubanta,ya tabbatar taji,har tsahon minti guda sannan yace "Kin sani sarai tun da can banason musu da taurin kai ko?,indai zaki dauki wannan dabi'ar zakisha wuya a wajena" daga haka ya miqe yayi gaba,tasan idan ta bari yafice batasan hanya ba,dole ta miqe itama ta bishi". Bangaren ajiye motocin gidan suka isa,yasa muqulli ya bude motar ya shiga,saita soma qoqarin bude gidan baya da zummar zata shiga,lock ya sakawa qofar ba tare daya waiwayo ya dubeta ba,hakanan ta gaji da tsaiwa ya yunqurin budewar ta matso gidan gaba ta bude,a hankali ta shiga ta zauna sosai sannan ta kame jikinta waje daya bayan ta sake jan mayafinta ta rufe fuskarta,karon farko bayan wasu shekaru masu tsayi ta sake hada mazauni dashi cikin mota,gaba dayansu jinsu suke banbarakwai,kowa yanaji kamar yana tare da baqonsa ne,ya dage dukka gilasan ya kunna ac dukda sanyin dake dan kadawa a garin,ya tashi motar suka fice daga gidan. Wani tuqi yake kaman bazasu gida ba ko kuma yana lallaba kwalta,duk da titin da sukabin fetal yake babu yawaitar jama'a sai haske fitilun titi tako ina,shuru ya ratsa motar babu me cewa komai har suka isa wani waje da sukeda saida kayan ciye ciye,kama daga ice cream,burger shawarma kaza da tsire da sauransu,saida yadanyi gaba kadan inda babu mutane sannan yayi parking,ya kashe motar ya fita. Bai jima ba ya dawo hannunsa dauke da leda ya sakata a sit din baya,sannan ya tashi motar sukayi gaba,hannunsa ya saka ya kunna rediyo freedom wanda minti biyar ya rage su fara shirin siyasa na kowanne

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});