Chapter 58
Chapter 58
motar wani ta sabbabawa rayuwarta bane,tabon da har yanzu bata daina jin dacinsa ba yana zaga jiki da rayuwarta gaba daya. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Qarfe sha biyu da minti arba'in da biyar tayi sallama falon daada,hasina 'yar gidan qanin abbanta ce zaune ta daga kai cikin mamaki da farinciki ta amsa sallamar "Mutan kano,yau a gari?,ni har nayi fushi fa,wai shahida kizo har garin nan kwanaki amma ki kasa leqani,gaba daya kin watsar dani kaman wadda ta miki wani mugun laifi?" Murmushi shahida tayi tana zama kan daya daga cikin kujerun gami da cire mayafinta ta aje gefe,iskar fankar da aka qurewa gudu cikin falon tana kadata gami da shigarta tako ina sakamakon zafin da ake zabgawa da kuma uwar rana "Kiyi haquri hasina,ba'a son raina ba wallahi,wannan tsohuwr ce ta min laifin daya shafeku,amma kiyi haquri zanzo in sha Allahu" cikin murmushi hasina ta tabe baki "Kedai bansan me ya dameki ba,koda yake an auna arziqi da aka samu ma kika ci gaba da zuwa katsinar da kika yiwa yajin aiki wajen shekaru hudu" murmushin da baikai har zuci ba shahida tayi tana cire agogon hannunta "Yanzun ma mawuyacine idan ban koma muku yajin aikin ba ai" ta qarshe fada wani abu na takore mata wuya idan ta tuna kasassabar dasu daada suka aikata mata,saidai takanji sassauci idan ta tuna tana da hope a yau,qasa qasa da murya hasina tayi "Hala ta kusa kwatanta miki abinda taso yimin kenan?" Kallonta shahida take ba tare da tace komai ba tana son jin qarin bayani "Wai in gaya miki matarnan daga zuwa mata hutu shikenan tasa aka mata kiran saurayina qafa da qafa wai ya kamata ya fito hakanan,wannan shekarar ta shirya aurar da jikokinta,wai basai ya dorawa kanshi wata dawainiya ba yayi abinda addini kawai yace masa ya wadatar Allah ya sawa auren albarka" tagumi da haba shahida tayi kawai tana jin wannan bayanin,ita kenan ta mata dakyau ma data amshi kudin aure,amma gwara hasina da ita sau dubu "Hasina kukan dadi kike,kinsan me daada tayimin?" Kai ta girgixa tana duban shahida "Kudin aurena da sadakina suka amsa gaba daya ba tare da na sani ba,kuma ba tare da nasan waye zan aura din ba,kawai don bincikensu ya basu managarcine suke ganin ya dace dani" idanu waje hasina ta fito dasu tana duban shahida,kafin tace wani abu suka jiyo maganar daada daga tsakar gida wadda ta fito da wanka ne tana fadin "Da kika shigo kika bar akwatin naki rana na duka waye zai dauke miki" dole kowanne yaja bakinsa yayi shuru harta iso falon,saita kalli idanunsu na 'yan sakanni kana ta tabe baki "Magulmatan banza da wofi" daga haka tayi wucewarta daki donta saka kaya,yayin da shahida cikin dacin rai da baqincikin daya taso mata ta fito tsakar gida ta shiga bandaki tayi fitsari sannan ta daura alwala nan bakin famfo ta shigo da akwatin nata. Qarfe daya da minti ashirin na rana tana tashi daga saman abun sallarta wayarta ta dauki tsuwwa,hasina ta miqo mata ta duba,nuradden ke kira ko bai fada ba tasan ya iso ne,gabanta taji yayi mummunar faduwa ta daga idanunta ta kalli daada data qarawa fura da nono ruwa take sha,saita kalli hasina,suka hada idanu ta mata signa sannan ta fita tsakar gida,ba jimawa ta biyo bayanta,janta tayi bakin kitchen ta gaya mata abinda ke faruwa "Tabdi,kina tunanin akwai abinda zai sauya dada?,amma arashin tayi akan bar arha,bari na gaya mata baqo zai shigo" ta juya tana komawa,kafin takai ga shiga falon yaro ya tamfatsa sallama yana rangada fadin wai ana sallama da shahida,daada dake zaune a rumfarta tayi katsu tana jiran taji wanda zaiyi magana cikinsu,shuru sukayi ba wadda ta amsa,sai daadan ta kira yaron ya qaraso bakin rumfar "Waye yake sallama da ita?" "Wani ne,wai nuradden daga kano" "Kano?" Ta sake tambayar yaron,saiya kada kai alamun eh,shuru na sakanni sannan tace "Jeka ce masa ya shigo" juyawa yaron yayi ya fice ita kuma ta kira shahida da hasina gaba daya "Xauna nan" ta nunawa shahida gefanta,ba musu ta zauna jiki a sanyaye,ta dubi hasina "Bude firinjin can ki ciro ruwa da lemo" ba musu hasinar tayi yadda tace,dada ta nuna mata shimfidar daddumar data gama salla akai bata kai ga daukewa ba tace ta dora saman nan. Cikin minti biyu kacal nuradden ya bayyana cikin falon,yaci manyan kaya yanata qamshi,bashi kadai bane shida wani abokinsa ko kuma ince amininsa ne,duk da dan uwanshi ne,cikin girmamawa suka zauna saman shimfidar suna gaida daada,ta amsa musu kadaran kadaham,yayin da idanun nuradden ke kan shahida. Tayin ruwa da lemon tayi musu,Sayyid abokinsa ya bude ya zuzzuba musu a kofi,kusan shi kadai yasha,yana sha suna dan taba jira jifa jifa da daada tana tambayarshi kano,kasancewar ta dauki shekaru masu dama rabonta da ita,tun kafin rasuwar babansu shahida. Sai da suka kammala tasa hasina ta zuba musu abinci,saidai sunce a qoshe suke,tilas ta rufe ta maida kitchen din,shuru ne ya ratsa na dan wani lokaci sannan sayyid yace "Am...daada,abinda yake tafe damu dama magana ce game da shahida da kuma abokina nura,duk da nasan bata sanar miki da zuwanmu ba" "Haka yake" a nutse sayyid ya fayyacewa daada komai,tayi gyaran murya tana dubansu "Nasan cewa kuna da labarin an bada shahidan harma an karbi sadakinta,idan ma ta boye maka bata gaya maka ba ni ya zama wajibi na gaya maka gaskiyar abinda ake ciki" "Ta fadama bata boye ba daada" "Yauwa...an riga da an karbi sadakin yaron,kuma a shekarun da Allah ya bamu bai kamata kuma ace muna magana biyu ba,uwa uba sanin kanka ne cewa haramunne neman aure akan nema,koda ciniki akan ciniki ne haramun ne bare nema kan nema,matar mutum kabarinsa,Allah ya qaddari haka tun farko shi yasa ya hukunta jinkirin zuwanka garemu,saboda haka ina mai yaba maka bisa soyayyar daka nunawa jininmu,ina kuma mai maka fatan samun dacewa da wata matar data fita,sannan ina mai dorawa da baka haquri,kayi haquri,Allah ya sawa zuciyarka dangana" sayyid ne kawai ke amsawa da amin,yayin da gaba daya jikin nuradden ya mutu murus,zufa ta dinga yanko masa tako ina "Mun gode sosai da karamcin da akayi mana" sayyid ya fada sanda suke miqewa bayan sun ajewa daada kudi "A'ah yaro...nifa bazan karba ba,zoka dauka ku wuce Allah yayi maka zabi mafi alkhairi" qememe suka qi dauka haka suka fice,daada ta juya ta kalli shahida dake zaune gefanta tana sharbar qwalla "Saikije ki sallamesu" daga haka ta miqe ta tayi wucewarta daki,sanda ta cimma qofar gidan tuni su nuradden sun wuce,sai tex daya turo mata na anjima zai kirata don yanzu baida nutsuwar tsaiwa,sulalewa tayi ta zauna gefan gadon,tana qoqarin hadiye kukanta. Shigowar daada dakin ya sanyata daga kai tana kallonta,tana daga tsaye ta soma magana "Kin kyauta sosai da kika sanyashi yazo kika toxarta mu,daa can kinsan yana sonki baki bashi dama ba har saida muka yanke hukunci a kanki?,ko kina tsammanin mu warware maganar da mukayi kaman qananun mutane?,to idan ma zaki kwantar da hankalinki ki nutsu waje guda shiya fiye miki alkhairi,ki shirya kuma ki dakaci zuwan gobe,mijinki da yardar Allah zaizo kuga juna,idan kinga dama kuma idan yazo din ki watsa mana qasa a idanu" daga haka daadan ta juya tayi ficewarta,sai kawai shahidan ta bita da kallo ranta na quntata,koma meye shi ya janyo mata,kuma shima
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96