Chapter 10
Chapter 10
fada sam,shi kuma bai fahimta ba bare yaja bakinsa yayi shuru ya barshi. Haka ta dinga raba abincin kamar yadda ta saba,saidai tanata dube duben kadan kadan da batasan meye dalili ba,harta kammala tsaf ta hada kwanukanta waje daya,haka kawai saitaji ranta ya baci lokacin data gama shirin komawa gida,duqawa tayi don daukar botikan taga an sako hannu an dauka,da hanzari ta dago don ganin waye?,ta tsammaci ma su ahmadi ne ma basu gargadin da aka musu jiya ba yau suka dawo,saidai ga mamakinta saurayin jiya ne,gaba yayi abinsa sai tabi bayansa sukaci gaba da tafiya ba tare da kowa yace da d'an uwansa wani sbu ba. Basuyi wani nisa ba ya janye ta koma ita ce a gaba shi yana baya,bata kawo komai a ranta ba ta tsammaci bazai gane gidan nasu ba shi yasa yayi hakan,kamar tafiyar jiya har suka je inda ya dakata a jiya ya aje mata botikin,saidai yau din ta daga ido ta kalleshi,akaci sa'a shima ya kalleta a sannan,wani irin zallar kyau da kwarjini idanunta suka gani,sai taji wani abu tun daga qwaqwalwarta har tafin qafarta,mazewa tayi gami da d'auke kai tana jin izzarta ta diya mace na motsawa,a nashi bangaren ma wani abu mai qarfi yaji yana janshi game da ita tamkar maganadisu da mayen qarfe,sai bakinsa yayi nauyi,bai furta mata komai ba ya juya ya soma takawa don barin wajen,daga manyan idanunta tayi tana bin bayanshi da kallo har sai daya bacewa ganinta,batasan me yasa ba bakuma tasan sanda ta saki murmushi ba ta daukin botikin nata ta fada gida. Tsahon kwana uku irin hakan na faruwa tsakaninsu,ba wata magana data taba shiga tsakaninsu,duk sanda tayi yunqurin yin wata magana saita kasa sabida kwarjinin da yake mata,tana son tace ya daina rakota saboda ganin yadda idon sa'idinawan unguwa ya soma dawowa kansu saidai ta kasa furta masa hakan,cikin ranta takejin nishadi a duk sanda suke wannan tafiyar ta kurame tun daga masallaci zuwa qofar gidansu,ko sunanshi bata sani ba,sai taga meye nata na tambayar sunansa ma,aishi ya kamata ya soma tambayarta sunanta,wani sashe na zuciyarta ya qalubalanceta da a'ah ba haka ake ba,ke yakewa alkhairi,ko godiya baki taba yi masa ba kan rakokin da yake,ta jinjina kai tana tabbatarwa da kanta rashin kyautawarta,ta kuma quduri aniyar a gobe zata masa godiya ta kuma tambayi sunanshi,kai ta girgiza kuma tana sake sakin murmushi,batasan dalilin daya sanya take yawan tunashi ba,batasan me yasa takejin wani baqon yanayi game dashi ba tun ranar data soma dora idanunta a kanshi,bata da amsa,tilas ta aje tunaninta a gefe sanda ta jiyo muryar babanta sun soma rabon halin nasu shi da ummanta,saita miqe a hankali ta isa bakin windon dakinta,ta yaye dan labulen net din dake maqale jikin window din tana kallon yadda suke dagawa juna murya kamar zasu yagi juna,batasan lokacin da wani hawayen baqinciki ya sauko mata ba,baqinciki da b'acin rai ya bata dukkan wani farinciki data tsinci kanta a ciki,wannan wacce irin rayuwa ce?,ina zata je ta daina ganin wannan baqincikin da bacin ran?,tabbas da akwai inda zata ta qauracewa wannan masifar da tuni ta jima da tafiya,tana son mamarta,hakanan tana son bananta,duk cikinsu babu wanda take goyon baya a cikinsu,batasan me yasa suka zabi wannan rayuwar ba bayan ga zuria suna tarawa,hakanan kowa yayi musu shaidar kyakkyawar mu'amala a waje amma me yasa gidan aurensu ya gurbace haka kamar sansanin yaqi?,haka ta zauna cikin dakin ita d'aya tana rusar kuka harta gaji da jin sautukansu ta dannan kanta qarqashin filo tana ci gaba da zubda ruwan hawaye. Kamar kowanne lokaci yauma ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani,sai hijabi mai hannu da yasha guga,kasancewar ummanta mai tsafta ce,hakan ya sanya dukka yaranta tun daga kan shahida zuwa faruqu zaka samesu fes dasu,hakanan ma gidanta da duk abinda ya shafi gidan,sosai higabi mai madauri purpule colour yayi mata kyau sosai,yau shigar ta musamman ce ita kanta tana jin hakan a jikinta,yau mai d'aukar matan bai qaraso ba tilas tadan zauna jiran zuwansa,tun tana jin ba komai harta soma qaguwa,haka kawai taji ra zaqu taje wajen,ta leqo agogo yafi sau nawa amma shuru yaron bai iso ba,saita kasa zama taci gaba da duba agogo har ummanta ta fuskanci haka,iya saninta shahida na zuwa kai sadakar abincin nan ne don kawai tana tsananin jin nauyin uncle isma'il,kusan kullum fuska a hade take tafiya a haka kuma take dawowa "Ya akayi ne shahida?,ko tsoron makara islamiyya kike?" Cikin rashin jin dadin ranta ta kada kanta "Toko yau zaki zauna kawai idan yazo saiya kai shi?" "A'ah umma....zan kai bari dai yaxo din" ta fada da hanzari,don bata jin zata iya jurewa rashin zuwanta wajen "To ai shikenan" umman tata ta fada tana kwashe shanyar kayan sawarsu da shahidan ta gama wankewa daxu,ciki harda ba mahaifinta don sam bata da quya ko gandar aiki. Yana isowa ko zama bata barshi yayi ba ta sakashi ya dauka suka wuce,sai taga kaman bata sauri,kamar tabar wani yana jiranta,haka dinga ji har suka isa wajen. Daga nashi bangare shima har ya soma tunanin me ya hanata zuwa har yanzu?,yana daga zaune cikin shagon bala yana duba agogon wayarshi,sama sama yake amsawa bala hirarsa,ya daga kai don sake kallon muhallin da take zama din sai yaga isowarta,wata ajiyar zuciya ya sauke ya zuba mata ido daga inda yake,kaman ance mata ta waiwayo sai suka hada ido,ta danso ta dirirce amma saita maze,ta samu waje ta zauna yayin da kowa ya soma fitowa da kwanonshi yana amsa. Duk motsin da take sai taji kama idanunsa ne a kanta,eh ba kama bane kallon nata yake,a yau ya hana kansa kallonta,duk da ta kamashi yana kallon nata yafi sau shurin masaki amma ya gaza dainawa,haka suka dinga hada ido lokaci zuwa lokaci har abincin ya qare,hakanan yau take jin wani faduwar gaba,ta dinga hada kwanukanta da sauri tana son yau ta bace masa,saidai burinta bai cika ba,tana gama hadawar ya iso wajen,ya dauki botikin ya soma takawa,bata da abinyi illa binsa. Suna isa inda suka saba ta zaci zaiyi yadda ya saba,amma ga sabanin tunaninta wannan karon sai yaja ya tsaya tsam yana riqe da botikin "Baki da kirki" taji ya ambata,ba shiri ta dago suka hada ido,qwayar idonta cikin nasa,yayi.mata wani kallo fuskarsa dauke da murmushin da yasa gudun zuciyarta qaruwa,cikin hanzari ta sadda kanta jin yadda yake shirin karya lagonta cikin qaramin lokaci "Nima na san haka ko baka fada ba....kayi haquri.....na gode da karamcin daka yimin harna tsahon kwana hudu,Allah ya saka maka da alkhairi" "Amin...amma bawai kyauta nayimiki ba,nayi miki ne donki biyani" ya fada cikin salon tsokana,a nata bangaren ta zata da gaske yake,take mummunan tunani ya darsu a ranta game dashi,baya ta danja kadan sannan tace "Ni bani da kudin biyanka,tun farko ma bansan biyanka kakeso nayiba da nace ka barshi" kai yake girgixawa dariya nason subuce masa,dariyar data qara masa kyau har tasa adam apple dinsa ya dinga motsawa "Ba kudi nakeso ba 'yammata....zuciyarki kawai nakeso ki mallaka min" ya tsinci kansa da fada,don ya shagalta da kallonta har baisan maganar da yake qasan zuciyarshi ya bayyana ba,a bazata taji maganar,don bata taba tsayawa ga da ga wani namiji ya gaya mata hakan ba ita dashi baki da baki sai wannan karon,ganin ta riga dataji me yake fada
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96