Chapter 44
Chapter 44
dan uzuri ya riqeni" "Toh uncle" daga haka dukkansu suka kashe kiran,tunani ya shiga sosai,sai salon tuqin nasa ya koma slow kaman bazashi gida ba,tunaninta ne ya dawo masa sosai tun farko alaqarsu irin wanda bai taba tsintar kansa a ciki ba. Sai daya kashe wasu mintoci kafin ya isa gida,a gajiye ya isa falonshi ya fada saman kujera yana lumshe idanunshi kafin ya budesu,yanason manta komai amma abubuwan nata zarya bisa qwaqwalwarsa,sai kawai ya miqe zuwa bedroom dinshi,ya cire kayanshi ya daura towel ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi sosai. Ya jima zaune gefan gadonshi yana neman bacci ya sureshi amma abun yaci tura,saiya miqe zuwa wani safe na musamman dake dakin,ya saka lambobin sirri ya budeshi,envalope din daya tsani gani yau da kanshi ya daukota,ya bude abubuwan dake ciki gaba daya,hotunan ciki suka bayyana,take kanshi ya soma daukan zafi,idanunsa suka kada jazur dasu,saiya kasa ci gaba da kalla ya soma tattaresu yana tuhumar shahida cikin ranshi "Me yasa shahida me yasa?,me yasa za k iyi haka,me yasa kika tarwatsani,me yasa kika tarwatsa duk wani buri da fata na?" Ya qarashe maganar yana cilla envalope din cikin abun ya maida ya rufe,saiya fada saman gadonshi yana maida numfashi gami da ambatar "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" *WASHEGARI* Qarfe goma da minti arba'in ya isa gidan cikin dinkin shadda wadda tayi masifar masa kyau da fito da kyawunshi. Dukkansu suna falo suna karyawa "Uncle sannu da zuwa,ina kwana" suka dinga fada daya bayan daya,fuska a sake yake amsa musu yana tambayar lafiyar kowa suna amsa mishi "Ina ummin taku?" "Tana sama tana wanka" sa'ida ta bashi amsa bakinta fal da zance,turarenta ya ciro ya miqa mata tasa hannu biyu ta amsa cikin Murna "Uncle na gode,na gode" "Yauwa" ya amsa yana duban tashar da suke kallo,hijra tv waqoqi suke sanyowa na mawaqa daban,sa'ida ce ta tashi daga cin abincin da take ta dawo kan kujerar da anwar yake kai "Uncle" ta fada qasa qasa,waiwayo yayi yana kallonta "Uhmmm" "Maganarmu ta jiya...." Shuru tayi ta ganin saukowar anty usaina,suna hada ido tahau rarraba idanu,miqewa tayi tsaye kafin ta iso,ta jefa mata harara "Ku kwashe farantan nan kukai kitchen,munaya ki hadasu ki wanke,ke kuma uwar zance ki bita ki daura abincin rana,kafin ki gama laqaqin naki kin gama" duka suka miqe falon ya zama daga ita saishi,ta zauna tana dubanshi "Jiya sai kuma na jika shuru,sa'ida tace ba zaka samu shigowa ba" yana shafa kanshi yace "Wallahi,jiyan na taho wani uzuri ya tsaidani" "To Allah ya rufa asiri" a mutunce ya gaisheta ta amsa masa cikin kulawa sannan daga bisani tace "Ko a hado maka abincin kari?" "Eh to...amma bada wani yawa ba" dauke idanunta tayi daga kanshi ta mayar qofar kitchen din ta kira sa'ida tace ta hado mishi. Yana karyawan suna taba hiran,a hankali shurunsa yafi maganarsa yawa,hankalinsa ya karkata kan hijra tv da suka sako waqar jarumar mata,saita dinga taba ranshi kadan kadan,tana tuna mishi wani lokaci can baya,a nutse ya dauki remote din dake aje kusa dashi ya sauya tasha,dai dai sanda anty usaina tace "Anwar....ya kamata fa ace ka soma shiri,biki saura sati hudu amma banga alamun hakan tattare dakai ba"sai daya hadiye abincin bakinsa sannan yace "to me zanyi anty bayan wanda nayi" "Kamar ya me zakayi?,haka zaka aurar musu diya babu maganar lefe babu komai?" Aje cokalin hannunsa yayu sannan yace "Nifa anty,da zaki yadda da maganata ayi haquri a qara min wasu watanni" "Saboda baka da gidan sakata ko baka da kudin yi mata lefan?,ko sadaki ne baka dashi?" Murmushi ne ya subuce masa ba tare daya shirya ba "Au dariya ma nake baka ko anwar?"kai ya girgixa dariyar na kubce masa "ni na isa antyna,kawai dai....naga kina yin nafisa ne da yawa" zamanta ta gyara sosai,alamun maganar da zata masa nada muhimmanci "Ba haka bane anwar,ka fahimceni,mutanen nan suna da kawaici da dauke kai,basu da son zuciya ko tilasta mutum,da wasu ne su yadda suke ganin sun isa dakai dinnan kawai zasu baka umarnin ka auri diyarsu ne,su saka kuma ranar biki da komai baka data cewa,uwa uba ina gudun halayyarku ta maza kafa kazo ka murje ido kace ka fasa ka barmu da kunya" murmushi yayi yana kallon qasa,shikam dama bayajin zai dauki irin wadan nan abubuwan,dalili kenan da tun farko ya zabi yaci gashin kansa,bai qasan wani bare ya tilastashi koya tauyeshi,rama halacci dai wannan yasan abune mai kyau,kuma shine hujja daya,dalili daya da zai sakashi ya haqura ya auri nafisa "Anty kiyimin kyakkyawan zato,ba abinda zai faru da yardar Allah indai daga bangarena ne,abinda kawai yasa na buqaci qarin shine,akwai wata 'yar tafiya da zanyi ta wata uku,kinga zaifi kyau naje na dawo,hankalina ya hadu waje guda,duk abinda za'ayin ma sai ayin,zan baki kudin da zai isa a hada lefan kafin wucewata da sauran abubuwan da aka sabayi na al'ada" ajiyar zuciya ta saki "Shikenan,yanzu ya za'ayi ka shaida musu?" "Wannan duk ba damuwa bace,zan samu alhj da kaina,baida matsala,yasan da tafiyar tawa dama" "Shikenan,Allah yayi mana jagora ya bada sa'a" "Amin anty" daga haka suka shiga hirar data shafesu,sai wajejen shabiyu na rana ya baro gidan shima ganin haduwar hadarine,baya n ya tambayesu ya tabbatar basu da wata damuwa. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Cikin harabar gidan yake zaune cikin motarsa,murfin motar side din da yake a bude yake,hakanan ya ziro qafarsa daya waje,iska mai dadi dake kadawa tana shigowa har inda yake,iskar na masa dadi qwarai,,dalilin kenan daya sanya idanunsa lumshewa yana shaqarta har tsakiyar kanshi,knocking glass din motar yaji anyi,ya ware idanunsa a hankali suka sauka kan fuskar nafisa dake tsaye cikin kwalliya tana dubanshi daga sama har qasa,duk da fuskarta qawace take da kwalliya amma annurin cikinta kadan ne,shigarsa take kallo,yayi kyau cikin qananun kaya baqaqe qafarshi saye cikin wani booth mai bala'in kyau,quruciyarshi da kyanshi muraran suka bayyana,sai taji sonshi na sake shigarta,baqinciki da bacin ran daga bikinsu ya sake mamayeta har hakan ya bayyana kan fuskarta "Whats wrong with you" ya tambayeta idanunsa qyar a kanta,saitayi narai narai da idanu,qwayar idonta cike da qwalla,,da alama gab take da sakin kuka,shuru tayi ba tare data amsa ba,fitowa yayi gaba daya daga motar ya rufe sannan ya jingina da ita hannayensa shima harde a qirji "Me ya sameki kuma?" "Au..baka ma sani ba zaka cemin?" Hannayensa ya watsa yana harde qafafunsa sannan ya soka hannayensa a aljihun wandonsa "Eh to,xai iya yiwuwa ni abinda nake tunanin shi zai saki kuka ke a wajenki bashi bane" "Me yasa anwar me yasa har qarin watanni uku bayan wata gudan dake gabanmu" girarshi biyun ya dage yana murmushi "Au,kice ke kukan aure kike,to saurin na meye?,wata hudu kawai saiya zama damuwa?" Langabe kai tayi tana dubanshi "Ni sai ya zama damuwa mana a wajena idan har wajenka bai zama damuwa ba,dama ni na damu dakai ai na sani" murmushi ya kuma saki,yadan tafa hannunshi kadan "Abinda ya faru ya riga ya faru,sai a jira zuwan lokaci" "Ai shikenan,yana iya"agogo ya kalla sannan yace "Zan wuce" idanu ta zaro "Duka duka yaushe kazo?,haba ya anwar mana don Allah,hajiyama fa tace ka shigo kaci abinci" "Sauri nake nafisa,amma idan na samu chance anjima zan dawo,idan ban dawo ba kuma sai gobe" ya qarashe maganar yana bude motar,sai daya shiga sannan ta mayar masa da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96