Chapter 26
Chapter 26
din hakan ya sanyashi cikin hanzari ya damqi kafadar shahidan da kayanta ya turata soron gidansu sannan ya jawo qofar soron. Koda suka dawo din suna tambayar ba'asi banza yayi dasu har suka qaraci tambayarsa sukaji haushi sukayi gaba. Tamkar shima d'an mayen haka ya dinga takawa yana hada hanya,tun daga gidansu shahidan har zuwa nashi gidan,yana shiga ya danna sakata,bai ma tuna da abokansa da zasu zo kallon ball yau a sabuwar qaramar plasmar daya sakawa falonsa ba cikin salary dinsa. Kan carfet din dake malale a falon ya zube,bai damu da ciwon hannunsa dake zubda jini ba,ciwon da yakeji cikin zuciyarsa ya ninka ciwon da yake hannunsa ninkin baninkin,wani irin suya qirjinsa da zuciyarsa suke masa,baisan me zai tuna ba,bansan me zaiyi tunani akai ba,baya gane komai,shahida kawai yake hangowa a yanayin daya ganta a gabanshi,sai kawai ya zame ya kwanta a wajen. Ranar haka ya kwana nan wajen,kafin gari ya waye ya zubda jini mai yawa,takwas na safe abokinsa kuma babban amininsa yazo ya dinga bugun gidan bai tashi ya bude ba,yana da tabbacin yana ciki tunda gashi ba kwado a qofar gidan,daga qarshe dai da hankalinsa ya kasa kwanciya saiya haura gidan kawai. A lokacin ya samu a daddafe yayi sallah yana zaune wajen xazzabi nason rufeshi "Wannan wanne irin abune haka anwar?,ya zaka kulle kanka cikin gida ayita nemanka?" Ya fada yana son karantar yanayin da anwar din ke ciki,baikai ga bashi amsa ba sukaji ana buga gidan,miqewa muhsin yayi don ya duba mai bugun gidan. Minti daya sai gashi ya shigo riqe da envalope ya ajiye gaban anwar yana cewa "Hala ma dai baka da lafiya ko?"muhsin yayi tambayar yana qare masa kallo "bani da lafiya muhsin" "Subhanallahi,kasha magani?" Kai kawai ya iya kad'a masa "Ya zaka zauna haka?,bari naje wajen sule mai shayi na samo maka ruwan zafi kasha sai ka samu magani kasha,ko na rakaka asibiti a dubaka" bazai iya magana ba saboda shi kadai yasan me yakeji,yana kallon muhsin har ya fice daga gidan. Sai a sannan idanunsa suka sauka kan envalope din dake gabanshi *SAQON GAGGAWA MAI MATUQAR AMFANI GA WANDA SAQON YA SHAFA* ya gani rubuce baro baro a bayan envalope din bayan ya juyata,hakanan yaji hankalinsa ya karkata gason sanin meye a cikin envalope din. Ta sama ya farketa saboda yadda ta mannu,ya zazzage duk abinda ke ciki,hotom farko ya kusa tafiya da numfashinsa,shahida ce rungume jikin wani qato,wanda hoton an daukeshi ne jiya da sukaje siyan syrup sanda ta kusa faduwa ya tareta,hoto na biyu sanda sukaje gidan qawar fiddausi ta daga syrup tana sha,sauran duka hotuna ne na tsiraici tare da wani saurayi haihuwar mahaifiyarsu,kaf numfashinsa ya dauke saboda wani abu daya tokare kafar numfashinsa,ya tafi daga zaune zai kifa luuu,abu na qarshe daya ji kiran sunanshi da muhsin yayi cikin qaraji da razana,daga haka komai ya tsaya mishi cak.https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/video *Alqawarin Allah* 1️⃣4️⃣ Ta bangaren shahida kuwa mahaifinta ne ya turo qofa ya tsinceta cikin wannan halin,wanda hakan ba qaramin kadashi yayi ba,bai gane a cikin maye take ba sai daya kamata zuwa cikin gida yaji tana surutai irin na wanda yasha wani abu ya bugu,saiya saketa suka zuba mata idanu shida ummanta suna kallonta,kasa tsaiwa tayi saita fadi luuu ta zube nata ci gaba da surutanta,wanda a nata tunanin anwar take kira ya tsaya tayi masa bayani,kuka umma ta fashe dashi yayin da abbanta cikin tashin hankali yace "Ina kika barmin 'yata taje mariya?" "Ina kuwa zan barta taje abba?,gaisuwar mutuwa suka je ita da qawarta" ta fada cikin tsananin tashin hankali da kuma kuka "Wallahi wallahi ki tabbatar da cewa indai wani mummunan abu ya samu 'yata toki kuka da kanki" ya fada cikin hargagi yana nunata da yatsa,a ranar dai umma babu bakin magana ta diyarta take,salati kawai take tana duba jikin shahida daya lalace da jini,bandaki ta kaita tayi mata wanka wanda shiya sanya bacci ya kwasheta bayan ta dawo da ita daki. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Da salati ta farka tana qarewa dakin kallo,ko ba'a fada ba tasan dakin ummanta ne,a hankali ta soma tuna me ya faru da ita,tun daga barinsu inda sukaje zuwa gidan qawar fiddausi,sauketa da saurayin yayi a qofar gidansu,daga nan zaren tunanin nata ya yanke,tayi tayi ta sake tuno abinda ya faru ta kasa,zuciyarta na gaya mata taga anwar,wata zuciyar tana ce mata bashi bane. Muryar umma ta jiyo tana kiranta cikin kakkausar murya wadda tasa hanjin cikinta kadawa "Shahida....ina kikaje jiya?" Saita kasa amsa mata,indai har a wannan yanayin ta shigo gidansu to tabbas bata da bakin kare kanta,kafin ta sake cewa wani abu umman ta zube dukka kwalaben da suka fado a jakarta wanda tuni ta gama karantawa ta kuma fahimci kayan shaye shaye ne a ciki,idanun umman jajur tace mata "Meye wannan shahida?" Kasa hada ido tayi da umman,hankalinta yayi qololuwar tashi,lafiyayyen mari umman ta sauke mata wanda ya gigitata,sannan yayi dai dai da shigowar abbanta dakin,wanda tunda ya fita sallar asuba daya daga cikin maqotansa ya masa jajen anga shahida an kawota qofar gida an yasar me ya sameta bai sake samun sukuni ba,yasan tabbas maganar akayita tattaunawa a jiya ana kuma sauya mata kamanni,yasan halin anguwar da 'yan unguwar kaf. "Ai kibar dukanta bari na gaya miki mariya,koma meye shahida ta zama laifinki ne,kin zaki baki kin kasa bawa diyata tarbiyya shine yanzu zaki zo kina wani hargagin banza da wofi?" Cikin bacin rai da shiga zafi biyu ta maida masa amsa "Indai shahida ta lalace ne kaima akwai laifinka,tunda kaima ubane ai ba'a dauke nauyin haqqin kula da ita daga kanka ba" "Au haka ma zaki ce?" "Eh na fada din,dame kakeso naji ne iye?" "To mariya nidai tsakanina dake saidai nace Allah ya isa ban yafe ba..." Cikin qaraji gana zubda hawaye tace "Nima Allah...." Qarar da shahida ta saki ita ta katse sauran magabar da umman tata taso furtawa,kuka take sosai hawaye wani yana bin wani "Ku dainawa juna Allah ya isa kune sila....dukanku ku kuka zama silar koma meye na koma a yau...ku ku kaini ga afkawa halin da nake ciki a yau,wannan abun da kukeyi shiya janyo komai,duk d'a na halak bazaiso yaga rana guda tak data zama ranar da mahaifansa sukai cecekuce ko jayayya ba a gabanshi,sai gashi ni nawa mahaifan a gabana suke xagin juna,a gabana suke aibata juna,a gabana suke debewa juna albarka,a gabana suke fada da junansu,duk yadda naso da ganin gyaruwar al'amarin hakan ya gaza,duk habyar da nabi ta ganin kun gyaru ba wadda ta bulle min,zafi da radadin haka yasa na nemowa kaina gurbatacciyar mafita,nake shan abinda ni a nawa tunanin bacci kawai zao sanyi ni,ban sani ba cewa ya shiga cikin abinda annabi ya haramta tunda zai gusar da hankali,zai saka maye,idan zanyi kuka bazanyi da d'aya saga cikinku ba,zanyi kuka ne sa dukkaninku,kun kasa fahimtata a sansa ya dace,kun kasa gane illar abinda kuke aikatawa a gabamu mu 'ya'yanku"daga haka ta miqe ta miqe jiri da kuma rashin qwarin jiki ya sanya ta dinga layi,amma bata dakata ba har sai data fice daga dakin zuwa nata dakin. Dukkaninsu sai jikinsu yayi sanyi,kowannensu ya shiga nazari da dogon tunani,bai sake cewa komai ba abban ya fice daga dakin,saiya zura takalmansa ma da niyyar ficewa daga gidan gaba daya. Yana sanya qafarsa a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96