Chapter 57
Chapter 57
zaka yiwa fuskarta kaga yadda ta fada,ta dashe hakanan tayi fayau,duk yadda anty zubaida taso ga kwantar mata da hankali kan lamarin hakanan taji hankalinta ya kasa kwanciya,tana ji ba auren dole za'a mata ba,a'ah nata ya xarce wannan ya koma auren qarfa qarfa. Tunda ya hangota ya fito ya tsaya yana jiran qarasowarta,ji yake kamar ya isketa ya tarbeta,tana isowa suka hada idanu sai taji zuciyarta ta karye gaba daya,tausayin nuradden din ya kamata fiye da ita kanta,don dama ita tuni ta sallamawa soyayya bare tayi mata kamun da zata jigata aduk sanda ta tashi gwada izzarta,saidai ko babu komai sabo mugun abu ne hakanan turken wawa ne,da hanzari ya zaga ya bude mata daya seat din ya kalleta "Shiga ki zauna,kar tsaiwar tayi miki yawa" karon farko ba musu cikin kasala ta zagaya ta shiga din,saidai duka qafafunta na waje,shima saiya zagaya ya shiga mazaunin direba yabar qofar a bude. Idanu ya zuba nata gaba daya yana hasaso ta ina zai soma daukar rashinta,sam yana jin bazai iya ba,a hankali ta bude baki zatayi magana ya daga mata hannu ya tsaidata "Karkice komai shahida,maganar gaskiya bazan iya rabuwa dake ba,bazan iya rabuwa dake ba shahida matuqar ba aure aka daura miki ba,zanci gaba kuma da yaqi tuquru don ganin na sameki,koda hakan na nufin zanje wajen daada da kaina na roqeta tabarmu tare ne" da hanzari ta bude baki "Ina nan ina gwada sa'ata,kuma ina saka ran samun nasara,idan hakan ya cimma tura zan sadaka da ita daadan taci daga bakinka" ajiyar zuciya ya sauke yana kallon shahidan,wani qaunarta yake sakeji,baya fata ko sau daya ya sakejin kalmar rabuwa a tsakaninsu. Tsahon mintina ashirin suna tare suna baiwa juna baki kafin yayi mata sallama yace zai wuce amma ta dakaceshi a waya,hakanan suka rabu kowa jiki babu qwari musamman nuradden din. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 Cikin satittikan da suka biyo baya suka fara zama watanni shahida tayi dukkan iya yinta don ganin daada ta janye qudirinta,an maidawa koma waye kudinsa da suka amsa amma abun yaci tura,bata taba ganin daadar ta dage kan abun haka ba irin wannan,sannu a hankali taji ta soma tsanar kona waye wannan,da wanne irin abu haka yazo da tashin farko za'a dauketa sukutum da guda a bashi ita?,sannan ta kowanne fanni kowa ya cije yace sai anyi?,hatta da anty zubaida ma yanzu ta soma bin layi,balle ummanta data ga kamar ma tafi kowa murna da farincikinda abun,don ko rannan data je gida bacin rai da baqinciki ya hanata wuni,wai umman har tarin biki take mata,hakanan su mubina har sun fidda anko,ita bata ma sani ba,sai 'yan uwanta 'yammatan dake sa'anninta daketa kiranta kan zasu sayi anko akwai a gida wajen umma?,ko sau daya ta kasa amsa musu saidai taja tsaki ta kashe wayar. Batun ya tsaya mata qwarai a rai,harta lura ta soma ramewa,bacin ranta da har zuwa lokacin wanda ake budurin a kansa bai gabatar da kanshi a gareta ba barema tasan waye,hakan ke nuna ma bata da wani daraja ko muhimmanci a wajensa kenan?. A haka aka shiga azumin ramadana,Allah ya taimaketa batayi sake da kwanakin ba,ta tsawaita ta kuma nace da addu'ar neman mafita wajen ubangiji babu dare ba rana,duk ta zama wata sukuku da ita,sauqinta daya wurin aiki sun bata hutu data tura cewa bata da lafiya,ba zata koma ba har sai bayan sallah,ko daya taqi samun nutsuwa cikin ranta,bacin rai fargaba da qunci da batasan na meye ba gaba daya sun cikata. Da sallah kuwa tana ganin su mubina dasu faruqu suka shirya tafiya katsina tace saisun dawo bata zuwa,ita lallai sai daada ta fuskanci fushi take da ita,daadan dako a jikinta wai an mintsini kakkausa,hakan na sake qona ran shahida,an shiga wata na biyu har ya cimma qarewa a yadda ma taji suna fada biki saura sati biyar amma bata yaba sashi a qwayar idanunta ba?,itakam taga yadda za'ayi wannan abu haka take yawaita fada cikin ranta,saitakejin ma abun kamar wasa,kamar bamai yiwuwa bane,hakan ya sanya ta sake baiwa nuradden qwarin gwiwa da kyautatan zaton lamarin bazai dore ba. 🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍🎍 *_SO DANGIN MUTUWA_* Satu guda cif cif da sallah ranar litinin daada ta buqaci shahidan tazo ranar juma'a mai zuwa,qememe tace bata zuwa ba inda zata,mubina ce 'yar isar da saqon data ji abinda tace bata ce komai ba harta gama wuninta tayi tafiyarta gida. Qarfe tara da rabi na dare suna gama waya da nuradden ta maida wayar chargy ta dawo tana cire hijabin jikinta don taji dadin kwanciya tana son saurarar littafin JARRABI na huguma (littafin da nan gaba kadan zaizo muku a SAUTIN HIKIMA TV dake youtube,idan baki subscribe ba ki hanzarta zuwa kiyi don kar a fara babu ke) ta gyara daurin dankwalinta don tafijin dadin kwanciya,sosai salon labarin ya qayatar da ita shi yasa da an dora sabon shiri a sautin hikima bata missing. Anty zubaida ce ta turo qofar dakin ta shigo itama da hijab har qasa a jikinta,da alama kayan baccine a jikinta "Baki kwanta ba?" "Shirin kwanciyar nake dai,jarrabi nakeson in saurara kafin na kwanta din" murmushi kadan anty zubaida tayi "Kin ganni nima kundin qaddarata nake saurara,ya zamemin jiki kullum saina saurari sabon episode idan sukayi updating" "Na koya miki ko anty?" Shahida ta fada tana dariya "A'ah,ai littafanne idan kika fara saurara baki da zaman lafiya saikinji qarshen kowanne labari" "Gaskiya kam", zama anty zubaida tayi kan kujerar mudubin shahidan " dazu mubina tazo tace miki daada tace kije daga ran talata zuwa juma'a shine kika ce ba zakije ba?"yanayin fuskar shahida yadan sauya,sam ita yanzu ko zancan katsjna ma bataso ayi mata "Anty to me zanje nayi mata kuma?,bayan ta gama tsara duk yadda ranta yakeso?" "Amma bai kyautu ta kiraki kiqi zuwa bako?,tunda kinsan cewa koma meye daada ba maqiyiyarki bace masoyiyarki ce,kome zata yi zatayishi ne sabida tana sinki ba don ki cutu ba" shuru sukayi gaba daya,anty zubaidan na karantar shahida,yayin da shahidan ta shiga tunanin me zata je ta yiwa daada?,amma tana ganin kuma wannan kamar wata dama ce da zata kaimata nuradden ya gwada sa'arshi ko Allah zaisa haqarsa ya cimma ruwa,kai ta kada "Shikenan,zanje ran alhamis" "Yauwa,dadai yafi" ta fadi tana miqewa "Anty don Allah idan kin fita ki cewa faruqu yayimin transfer din data,data din nan satinta daya da ita nakejin littafin,donma ba cirar data din ake ba ai da tuni ta qare" "Yana falon uncle,zan masa magana" ta amsa mata tana fita a dakin. _kuyi manage da wannan_ https://youtu.be/_XVqJSBXVPI *Alqawarin Allah* 2️⃣9️⃣ Da hanzari ta koma jikin wayarta ta cirota,ta koma gefan gado ta rubuta saqo ta tura masa,saita kashe wayar don ta tabbatar ta barta akunne nuradden bazai barta tayi barci ba,tunda damar da yake nema kenan gashi ya samu. Washegari tana kunna wayartata kuwa kiransa ne abu na farko daya soma shigowa,yadda taji muryarshi ya kasa zaune ya kasa tsaye kaman ance masa an bashi ita dinne,tun a ranar suka shirya yadda tafiyar zata kaya,ya nemi su tafi tare tace sam,ya sameta kawai a can ran alhamis din,murmushi ya saka mai sauti "Bakison hawa motata kwata kwata shahida,don know why....koda yake babu komai saura qiris in sha Allahu,Allah yakai damo ga harawa dai" murmushi kawai ta saki tana yanke kiran,bazai gane bane,baisan irin illa tabo da masifar da shiga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96