Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,288 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai yaji wani dunqulallen abu ya tare masa maqoshi "Ashe dama saboda wata qaddara ta fadawa rayuwata saika gujeni?" "Qarya kike!.....babu ruwab qaddara" ya fada cikin qaraji da daga murya,wanda har sai daya tashi daga kashingidar da yake yana fidda huci irin na wanda ransa yayi tsananin baci,daga gefan shahida tsoro ne ya kamata,tana daga zaune amma jikinta ya dauki rawa,cikin jarumta da dakiya tace "Amma yaya anwar....dare daya wannan abun har yayi girman da zai saka ka manta soyayyarmu?" "Soyayya?....soyayya kike fada shahida,daga yau ki sawa ranki nayi bikin bunne soyayyarmu,kisa a ranki baki taba soyayya da wani mai suna anwar ba" gabanta yayi mummunan faduwa,kalaman daya furta yanzu sunyi kama da wadanda ke rubuce cikin takardar dake qanqame yanzun a hannunta,da gaske anwar shi ya iya rubuta duk maganar dake kan takardar?,yana nufin ba bacin rai bane cikin hayyacinsa yake?,hakan yana nufin da gaske yana tare da wata?,ya sauyata da wata? "Sam baki dace dani ba bakiyi dai dai da rayuwata ba" kalaman suka sake saukar ba zata daga kunnuwanta zuwa zuciyarta,saqon ya isa kai tsaye zuwa qwaqwalwarta ya soma barazanar dakatar da aikinta "Nayi dana sanin saninki....nayi dana sanin kasancewa dake tsahon lokuttan dana diba a baya" ya furta cikin sanyi wanda hakan ya saba da ainihin abinda ke zuciyarsa na tururi da zafin da takeyi,idanunsa sun kada jazur dasu "Ya....yayya...kasanme...me kake fada kuwa?" Ta fada cikin harhada kalaman da suke niyyar qwacewa daga bakinta saboda tsananin dimuwa dataji ta afka lokaci guda "Shahida.....idan nace Allah ya yimin sakayya ba shakka banyi kure ba" qit ya katse kiran daga haka saboda numfashinsa da yaji ya soma yi masa tauri,kanshi ya kifa kan kujerar dake gabanshi yana fidda numfashi cikin wahala,ba shakka dashi ragon namiji ne kuka zai fashe dashi ko zai samu sassauci cikin zuciyarsa,domin a wannan yanayin da yake ciki kukan shine abunda yafi cancanta yayi. Daga fannin shahida kuwa miqewa tayi hannunta aka,sai kuma ta saukesu ta nufi qofa gadan gadan,komawa tayi da baya kuma saboda katsewa da tunaninta yayi,ta samu gefan katifarta ta zauna,lallai ba shakka koma meye zai faru a yau tana da buqatar ganin anwar ido da ido,zuciyata bata gamsu ba hakanan nata nutsu da cewa shi yake gaya mata wannan maganganun ba. Kusan wunin ranar gaba daya tsaho taga yayi mata,tayi sintiri sau babu adadi,takai ta kawo kaman wadda ta hadiyi tabarya,ko sha'awar zaman ma sam batayi har aka kirayi sallar magariba,magaribar tazo tadan gota sannan ta fito tsakar gidan sanye da hijabin sallarta. Ummantace kawai zaune saman abu sallar wanda suna hada idanu takau da kai,daga ita har abban nata ta fuskanci kamar suna kunyar hada idanu ne da ita ko yin wata doguwar magana tun maganar data gaya musu ta qarshe ta fito ta barsu a dakin,da alama yau abban nata ya samu ya lallaba ya fita masallaci sallah kenan,gefe ta samu ta tsugunna a takure "Zanje chemist din ado ya dubani"bata ce komai ba sai daga abun sallar gabanta da tayi ta ciro dari biyar ta miqa mata,sannan ta waiwaya ta kalli mubina dake zaune tana zane zanen 'yar tsana a paper "tashi ki rakata" tsam mubina ta aje takaddun,ta dauki hijabinta itama dake gefe wanda da alama tare da umman suka gama sallar ta saka tabi bayan shahida da tuni harta fara takawa zuwa waje,tuninta kawai ya zatayi da mubina. Dole ta fara zuwa shagon ado ta gaya masa qarya da gaskiya ya soma hada mata magani,sai tace masa tana zuwa,ta samu mubina zaune kan bencin dake aje a qofar shagon "Zauna mubina naje na amso wata allura da yace zaimin,karki sake ki tafi ki jirani na siyo na kawo yanzu zaiyimin"kai ta gyada abinta,tana ci gaba da kallo ta cikin qaramat tvn dake cikin chemist din. Sannu a hankali ta dinga tambayar gidan,karo na farko a rayuwarta data soma tunkarar gidanshi,bama gidan ba unguwar gaba daya. Sanda wani yaro ya nuna mata gidan saita tsaya cak zuciyarta na mugun bugawa kaman zata fito,addu'o'i ta soma karantawa tana neman agajin ubangiji,jin motsi daga cikin soron ya sanya tayi saurin matsawa ta rabe gefe tana kallon muhsin daya fito daga gidan ya miqe can layin nasu yana amsa waya. Sai data tabbatar ya qule sannan ta fito sosai,ta doshi gidan ta saka qafarta asoron da bismillah a bakinta. Dai dai lokacin yana zaune ne shuru,yayi nisa a duniyar tunani,gabanshi abinci ne aje,abincin da muhsin yaji haushin qin gaya masa damuwarsa da yayi ya tafi ya barshi yana mita. Bai ankara ba baisan ta shigo ba sai ganinta yayi tsaye bisa kanshi. Dubanta yake kaman yadda take dubanshi,kowanne da abinda qwaqwalwa da zuciyarsa take gaya masa,cikin hanzari ta isa gabanshi "Baka da lafiya ya anwar dama?,me yas....." "Dakata!" Ya fada a tsawace yana miqewa tsaye,ji yayi kamar ta dana mishi wuta a jikinsa,ganinta ita daya cikin wannan dare sannan kuma cikin gidanshi "Me ya kawoki me kikazo yi?" Idanunta fal hawaye take dubanshi,tunda suke dashi dai dai da second guda bai taba mata magana da irin wannan amon ba,har kullum shi mai tattalin kwanciyar hankalinta da farincikinta ne,yau daya anwar din gaba daya taga ya sauya mata?,tun daga lafazi zuwa kamanni "Na baki second biyar ki fita ki bani waje,idan ba haka ba saina baki mamaki wallahi" ya fadi idanunsa dake cike fal da kishi haushi takaici da baqinciki suka sake girma suka yo waje kaman zasu fado "Ya anwar....ka daina irin wannan abun kana bani tsoro wallahi....ya anwar wani ya baka labarin abinda na aikata ne yasa ka sauya haka?" Wani murmushin takaici ya saki,wanda shi kansa ba abinda ya qarawa fuskarsa face wani yanayi mai ban tsoro "Labari?,labari aka bani?labarin me?....shahida...ina cewa tun kafin kizo nan kinji me na gaya miki?" Kai take girgizawa kamar wata sabon tabi tana dubanshi,yayin da hawaye ya soma jiqa gaban hijabinta "Ka fada ne kawai amma ba kana nufin hakan har zuciyarka ba,ba zaka iya rabuwa dani ba,ba zaka iya gujemin ba" matsowa yayi dab da itar har suna musayar numfashi a junansu,idanunsa sun sake girma daja,ya sunkoya da fuskarsa saitin tata "So kike na maimaita miki abinda na fada a waya?,to ni anwar nayi dana sanin saninki da nayi,nayi dana sanin kasancewa da nayi dake a baya....shahida anwar bakya gabanshi a yanzu ki fita daga rayuwarshi,ya jima da yanke dukkan wata alaqa data taba hadaki dashi cikin tarihin rayuwarku keda shi" tunda ya soma maganar ta runtse idanunta tsam tana jin saukar hucin numfashinsa saman fuskarta,yayin da kaifi da dafin maganar ya dinga ratsa kowanne sashe na jikinta har ya isa ga zuciya ruhi da kuma qwaqwalwarta,duk da yadda idanunta ke a rufe hakan bai hana hawaye saukowa daga idanun nata ba kai kace lalataccen famfo aka bude,sanda ta ware idanunta itama akanshi sai yaja baya yana ci gaba da duban qwayar idanunta "Ya anwar....me yasa?,me yasa zaka yanke wannan kyakkyawar alaqar?,me yasa zaka yanke kyakkyawar dangantakar da aka ginata tun tana jaririya harta girma?" "Wannan kyakkyawar alaqar da kike magana akai ta dade da mutuwa,ta dade da juyewa zuwa mummunar dangantaka a wajena daga sanda na ganki kwance male male saman wa....." Sai ya kasa qarasawa saboda tuna mummunan ganin da yayiwa hotunan,wani abu mai tauri ya taho yaso ya toshe maqoshinsa,sabida haka cikin qaraji ya sake cewa "Ki

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});