Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 67

Chapter 67

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,300 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kulle gam tanason tilasta kanta tayi bacci. Haka aka dinga mata knocking tana ji ta share,donko hasina yau saidai ta kwana wani dakin amma ba nata ba,kadaitaka kawai yau take da buqata. Sai sha daya da wani abu na dare sannan bacci ya soma fisgarta,qarar wayarta yasa ta bude idanunta ahankali kan wayar dake aje saman cikinta,ta daga wayar tana dubawa,lambace babu suna,kaman ba zata daga ba sai kuma ta daga kana ta kara a kunneta gamida yin sallama,can qasa taji an amsa sallamar har bata tantance muryar waye,shuru ya ratsa da wasu sakanni "Nuradden" ta canki sunan "Shahida,na rasa ta ina zan fara koyawa kaina haquri dake" idanunta ta lumshe tana jin bacin rai na ratsata "Kayi haquri noradden,duk ni na jawo mana komai,da ace banyi jinkirin hanaka zuwa gidanmu ba da guni hakan duka bata faru ba" "Ki tayani addu'a kawai,Allah ya yayemin,don ba lallai bane na daina sonki" daga haka wayar ta katse,a sanyaye ta ajiye wayar ta mirgina daya barin nata,harga Allah bata tausayin kanta kamar yadda take tausayin nuradden din,ya riga ya fada da yawa,ta kuma son ciwo da radadin soyayya,musamman a sanda ka rasa abinda kake tsananin so ka kuma saka ranka dashi,a hankali kalamanshi suka fado mata,baya neman yaradarta,bata cancani ta rayu cikin farinciki ba ta zabi wanda takeso,zai aureta ne don ya nuna mata ya isa,lebanta na qasa ta cije tana rarrabe maganar da abinda yake nufi,auren manufa zaiyi da ita kenan?,zaiyi ne don cimma wani boyayyen nufi nashi?,lallai zata nuna masa yayi ganganci,akwai banbanci tsakanin da da yanzu,ta jima ahaka tana saqa abubuwa da yawa tare da tunawa da al'amura masu yawa kafin bacci yayi nasarar saceta. Washegarima kusan fitar wuri tayi,tana tsaye a kitchen tana shan ruwan dumi anty zubaida ta taras da ita "Ba zakiga kayan ba kenan zaki fita" agogonta ta kalla sannan ta sauke hannu "Sauri nake anty" "Hakan yasanya jiya nace a tasoki ki gani ai" baki ta tabe a fakaice tana tuna haushin da hasina taso tura mata ajiyan da yadda ta matsanta mata,kayan da bataga abinda anwar zai zuba a ciki da zasu burgeta ba "Idan na dawo na gani,saina dawo anty" ta fada cikin hanzari bayan ta dauki jakarta data aje ta rataya tana ficewa da hanzari,kasa cewa komai anty zubaida tayi sai binta da kallo kawai da tayi harta fice sannan ta girgiza kanta tana tadi ita da zuciyarta,ko ba'a fada ba tasan ganin kayanne bata sonyi. Kwana uku tana cewa anty zubaidan zata gani amma bata yarda taje inda sukebama bare ta gani,dole ta gaji ta zuba mata idanu,a haka har akaci kwana goma sha biyu,ga tsammanin anty zubaida shahidan zata dauki hutu wajen aiki,saidai taga ko ajikinta bata fasa fita aikin na,sake qara mata kwana biyu tayi taga ko zata dakata da fitar,saidai ranar daya rage biki saura kwana bakwai cif da safe anty zubaida ta sameta a falo tana karyawa ta gama shiryawa tsaf,kallonta sosai take taga da gaske take fita aiki zatayi?,kallon harya sanya shahidan itama yin sak tana kallon anty zubaidan,saidata soma dan tsuke fuska sannan tace "Ina zaki haka da safe?" Tambayar tadan baiwa shahida mamaki,ko maqota sunsan inda taje zuwa daga safiya zuwa yammaci bare anty zubaidan,don ita bata kawo tambayar tata nada alaqa da aurenta ba "Office mana anty" ta fada cikin son gamsar da ita,kai anty zubaida ta girgiza "Bakisan aurenki saura kwanaki bakwai ba ko lissafi ne ya qwace miki?,ko kuma duka kina sane saboda kinha na zuba miki ido ne?"wani abu ya taba zuciyar shahidan,ba zancan data tsana a yanzu irin zancan aurenta,tana sane saura kwanaki bakwai su qullashi to amma ita meye nata a ciki?,me zata zauna gida tayi " to anty,ni menene nawa a ciki?,me zan zauna nayi a gida?" "Eh babu komai naki a ciki tunda zubaida ce zatayi aure,so kike duniya ta zagemu ko?,tunda kike kin taba ganin amarya budurwar da aka aurar salin alin?,to banason sakarci,babu ruwana da wani abu daya taba gittawa tsakaninki da anwar ni aikina zanyi kawai,rawata zan taka,saboda haka ki koma ciki daga yau zansa abban huda ya dauka miki excuse,su baki hutun sati uku" kaman ta zunduma ihu haka taji sanda anty zubaida ke maganar,abinda ta dauka wasa ne gashi yana neman tabbata,ba damar musu da ita saboda yadda ta tsare gida sosai,haka shahidan ta soma takawa don komawa dakinta "Eheennn...jimana" anty zubaida ta sake fada,saita tsaya gami da waiwayowa tana dubanta,sai data kallo agogo sannan tace da ita "Qarfe sha daya na rana zamu fita dake,ki zauna cikin shirin" kai ta gyada kamar kazar da qwai ya fashewa cikin cikinta,haka ta dinga tafiya harta isa daki,ta watsar da duka kayanta kanta na daukar zafi,me yasa anwar yake son ya soma da nasara da sa'a a kanta?,me yasa anwar ya dawo cikin rayuwarta bayan bata da buqatarsa?,haka ta dinga yiwa kanta tambaya ranta na zafi. Sha dayan da 'yan mintina suka fita ita da anty zubaidan kawai,bata tambayeta ina zasuje ba har saida suka isa gidan sannan ta fahimci wajen gyaran jiki ta kawota,tamkar wata doluwa haka ta dinga bin anty zubaida da kallo har suka gama gaisawa da matar da gabatar da shahida wajen matar a matsayin amaryar da za'a yiwa bikin "Kai tubarkalla masha Allah,wannan badon hausawa suna cewa idan kana da kyau ka qara da wanka ba ai bata buqatar komai,saida nasan gyaran ba qaramin hawanta zaiba zubaida" tana jinsu harta gama surutunta ta soma hada kayayyakin gyaran jikin ta buqaci shahida ta sauya wani zani na daban data dauko.mata,fuska ta bata tana duban anty zubaida ranta na baci ta wani gefan,yanzu saboda anwar ne aka kawota nan wajen "Anty,don Allah abar abunnan,batamin kaya kawai zaiyi" dago idonta tayi daga wayarta da take dannawa ta watsawa shahidan harara,hakanan tana ji tana gani ta sauya zanin aka shiga mata gyaran,bakinta gum tana bin matar da kallo kaman ta mangareta saboda yadda takebin fatarta da kayyakin tana shafeta dasu. Tana ganin kawai bata lokaci da bata kudi ne. A qalla sun kusa kashe awa biyu cur ana abu daya,bin jikin nata take da kallo yadda ya soma wani santsi sulbi da sheqi na musamman,tabe bakinta tayi data tuna saboda me akayi mata,sai taji gyaran sam bai burgeta ba,tana maida kayanta wani qamshi na tashi daga jikinta duk sanda ta motsa,turarukan qarshe da aka murje mata jikinta dasu. Basu jima ba suka isa gida,a falonta zauna cikinsu huda wadanda ke kallo,faruq ya kalleta "Anty harkin fara canzawa,kaman bakeba akan dazun da kuka fita'binsa tayi da ido kawai ba tare datace komai ba,kafin ta gama tunanin da take ta jiyo muryar huda "anty...zamuyi kewarki,tafiya zakiyi yanzu ki barmu?"ta qarasa fada a shagwabe kaman zata saki kuka,nan take ran shahida yaso ya sake baci da tuna hakan da tayu,anty zubaida ce ta katse komai tana tambatar faruq me suka dafa musu,yace white rice ne bazai iya miya ba,hararsa tayi "Daga kai har haidar din a rasa wanda zaiyi miya?" Huda na gefa na musu dariya,kai ya langabar "Allah ummi shi yasa nace ki samo mai aiki fa" tsaki taja sai shahida ta miqe "Bari na hada" tafurta tana yin gaba zuwa kitchen. Kayan miya ta diba ta soma gyarawa sannan tayi blending,dukka rabin hankalinta da nutsuwarta nakan tunani,data hada miyar saita zauna cikin

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});