Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 47

Chapter 47

Alkawarin Allah Book 1 Complete Hausa Novel 1,290 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

futo da system dinta wadda a office din ta kwana bata je da ita gida ba jiya "Kai masha Allah,duka kamfanin nan ba office din dake burgeni nakejin dadin shigoshi irin wannan,komai neat masha Allah" ya qarashe maganar yana sauke idonshi a kanta,dan qaramin murmushi ta saki sannan ta soma dai daita cumputer din gabanta,ba tare data sake bashi wata qofar sako wani zancan ba ta soma gabatar masa da abinda ya zaunar dasu. Tun tara da rabi suke abu daya har qarfe daya da rabi na rana kafin su kammala,ta gaji matuqa tayi tubus,ga 'yar banzan yunwa dake damunta,kujerarta taja baya bayan ta rufe system din tana hamma idanunta lumshewa wanda sam bata kula da yadda mudassir ya zuba mata ido yana kallonta ba cikin burgewa,tunda suka zauna qamshinta ke burgeshi "Yadai madam?" Ya tambayeta har yanxu idanunshi na kanta,sai a sannan ta juyo ta dubeshi,fuskarta adan hade kaman yadda ta saba idan ta fuskanci kana da shiga sharo ba shanu "Da akayi me?,ai mun gama ko?,sauran aikin ya rage naka da nawa,kowa yaje ya tsara abinsa cikin system dinsa,duk randa zamu gabatarwa da boss kowa yasan me zai fada" kai ya rausayar "Ba haka nake nufi ba,naga kaman bakijin dadi ne" miqewa tayi tsaye tana gyara yafen mayafinta,bandaki takeson shiga sabida fitsari ya matseta gashi yaqi fita ya bata waje "No,ba komai gajiya ce kawai.." Ta tura kujera baya sosai yadda zata samu damar fita daga tsakanin kujerar da teburin. Gab da zata shige bandakin aka nemi izinin shigowa office din ta bayar,masinjarta ce cikin girmamawa tace "Kinyi baqo ne anty(haka take kiranta saboda yadda take ganin qimar shahidan" cikin mamaki tace "Baqo kuma?,custumer ne?", ta tambaya duk da tasan bashi bane,don yawanci ba'a ganinta ita idan ba wata matsala bace akan pyment da custumer zaiyi,koda kuma zai ganta ma za'a rakoshi ta qarqashin wani office dake kula da shige da fice da kuma siyayyar kaya a kamfanin " a'ah,yace yana son ganinki ne personal"tayi tsammanin cikin mutanen dake takura mata ne,abun saiya qona mata rai,batason abinda zai shafi mutuncinta a wajen aikinta,sabida haka taja tsaki "Jeki ce masa lokacin aiki ne yanzu,ya nemeni ta waya ko waye idan na tashi daga nan" "Toh" ta fadi tana juya ta fice daga office din,tsaki taja ta dawo don daukar ruwa ta soma sha tukunna "Sai haqurifa,kinsan kowanne mutum da yadda Allah yake masa baiwar jama'a" waiwayowa tayi ta kalleshi,shaf ta mance dashi cikin office din,saita dauke kai tana sake hade girarta ba tare datace masa komai ba,batason a dinga zama mata cikin office tafison kuna gama aiki ka kama gabanka,wayarta dakw cikin jakar hannunta wadda ke saman teburinta tayi qara,a nutse ta qarasa ta zugeta ta cirota,sai taga number nuradden,fuska tadan yamutsa saboda yadda taji gabanta yadan fadi,ta daga ta kara a kunnenta "Allah ya baki haquri gimbiya nine fa,ko nima ba za'a samu damar ganina ba bayan alqawari aka yimin?" Mamaki ya cikata,ta yaya akayi yasan kamfanin da take aikin,banda abinki wannan wajen kina tunanin zai xama boyayye ne?,shahararren waje irin wannan? Wata zuciyar tace da ita,murmushi ta qaqaro "Ayyah bansan kai bane,minti daya ina xuwa" kiran nashi ta katse ta soma neman wata number cikin ranta fana dana sani da Allah wadai da kunna wayarta data yi,data sani tun daxun ta barta a kashe kawai,wani sashe ta kira na kamfanin ta bada umarnin a rakoshi,daga haka ta kashe wayar,duka sai jikinta yayi sanyi taju qafafunta kamar an bubbuge mata su,sai ta zauna saman kujerun cushion dake gefe daya na office din. Sanda ya turo qofar lokacin saddam ya miqe yana fadin "Bari na samo miki wani abun,na fuskanci kaman yunwa kike ji" bata iya amsa mishi ba yayin da sukayu clashing da nuradden sanda yake shigowa,suka kalli juna saddam ya sanya kai ya fice nuradden ya bishi da kallo,sai daya bace masa sannan ya dauke idanunshi ya qaraso yana rufe office din idanunshi a kanta "Waye wannan din?" Ya tambayeta kai tsaye,tasan akan wa yake tambaya saita saki murmushi "Abokin aiki,aiki muka gama dashi yanxu" dan shuru yayi kishi na cinsa,ji yayi kaman ya maqure saddam din sabida ya karanci irin kallon da yakewa saddam din shima irinsa yake masa,kansa kawai ya jinjina yana qarasowa "Kin kashe wayarki kin tsammaci bazan iya laluboki ba duk inda kika shiga ko?" Boye dariyarta tayi,batasan ya dagota ba "A'ah,kasan idan ina aiki banason yawan amsa waya,dalili kenan daya sanyani na kashe" inda ta tashi ya koma ya zauna yana kallon office din nata,kaman yadda ya saba burge jama'a shima ya burgeshi sosai "Sannunka da zuwa" saiya kalleta "Allah yasa har zuci" qaramar dariya ta saki "Da ba har zuci ba da tunu na koreka ai" maimakon ya amsa saiya jefo mata wata tambayar "Wanne babban baqo haka kukayi a companynku yau?" Dan tunani tayi kadan sannan tace "Gaskiya ban sani ba,saboda ba bangarena bane" kishi yakeji sosai da fargabar kar shahidan ta subuce masa saiya sanya idanunsa cikin nata sanda take za a wata kujerar da take kallon tashi "Haka manyan mutane ke zuwa wajenku?" Kafada ta dage "Wajensu dai,abune mawuyaci ni nasan zuwansu ko fitarsu,tubda ba sashe na bane saidai idan wata matsala da buqatar zuwa wajena ya zama dole" "Ina kishinki shahida" cak ta tsaya tana kallonsa,kalamansu sunyi shigen kama dana juna,ya tuna mata dashi dole saboda yanayin yadda yayi furucin,hakan ya sanya ta miqe kawai ba tare data samu abun fada ba "Kinsan sonki yake?" Ya jefa mata tambayar sanda take bakin dan qaramin fridge dinta tana ciro masa ruwa da lemo,saita waiwayo tana dubanshi,murmushi ya qwace mata "Wani abu makamancin haka bai taba shiga tsakanina dashi ba,kar ka saka komai a ranka,kai kanka shaida ne na wace shahida,abu mai sauqi ne samun hanya zuwa zuciyata kai tsaye har haka?" Maganar tata ta bashi qwarin gwiwa,sai yayi shuru yana nazarinta,harta dawo ta aje masa lemon da ruwan a gabanshi,yayin dashi kuma ya dire mata ledar daya shigo da ita "Ga abinci nan,inajin kamar kina da buqatarsa shi yasa dana tsaya naci nayo miki naki takeway din,don nasan ko xuwa nayi nace kizo muje muci taren ba zuwa zaki ba" ya fada cikin jefanta da magana,tasan yana jin haushin hakan,ita kuma ra'ayine sam bata dashi,sabida haka tayi murmushi kawai,ko yanzun ma ba zata iya cin abinci yana kallonta ba shina ya sani,amma duk da haka saiya soma bude mata ledar yana cewa "Kiyi haquri yau dai daya kici a gabana,saimu tattauna abinda ya kawonin,kada lokacin break dinki ya qare na shiga haqqin company",bai gama budewa aka sake bude qofar aka shigo,dukansu suka maida hankali ga qofar,saddam ne hannunshi dauke da ledar gidan abincin dake daura dasu,wanda shahida tafi order abinci acan,fuskarsa cike da murmushi ya nufosu kai tsaye ba tare daya dubi nuradden ba ya iso gabanta,dora abincin yayi saman na nuradden daya bude mata yace "ga favourite dinki nan", wani abu ne ya takorewa nuradden wuya,ya daga kai ya kalli saddam cikin fushi "Wanne irin rashin hankaline malam?" Dubansa saddam yayi "Da akayi me?" "Ta yaya zaka shigo kai tsaye ba tare daka nemi izni ba,sannan ka samemu zaune zata ci abinci ka dora wata ledar a sama?" A dage saddam yace "Matarka ce?" "Koba matata bace ina zaton tare ka ganmu" cikin halin ko in kula

Table of Contents

Chapters

96 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});